INA TARE DA ITA BANSAN ITA BACE 1-10

Asalin labarin
****** ****** ******
Mlm mamman cikakken dan adamawane bafulatani ne gaba d baya, yana zaune d matarsa d’aya da y’aya 3 musa abdullahi,Ibrahim bashida wata Sana’a sai kiwon shanu ,bayan Musa yatasa yasakashi makaranta lokacin d yagama primary skul yatafi secondary skul asannan asaka saka sauren k’an nansa suma askul d’in.. Cikin ikon ALLAH Musa yagama yaciba d karatu shida yan uwansa har yagama yasamu aiki agarin Kaduna ,yakoma can da zama sai week end yake zuwa daga baya yahadu da binta (Ummi)suka fara soyayya har zuwa aure ,suna zaune cikin so d kauna harta haifi danta Suleiman Wanda Ibrahim yad’auki son duniya ya azamasa komai yace my son ko Hutu suka samu yazo Kd yace gun yaronsa yazo yaganshi ….ana cikin hakan mlm mamman yarasu ,Wanda hankulansu yyi matukar tashi sosai ,saidai me ?” Bayan rasuwar sa ,inna wato majaifiyarsu Musa tatai ciwo itama saidai rasuwar tayi sunyi kukan rashin mahaifiyarsu dg baya ,suka sanar da danginsu zasu koma Kd da zama dama alokacin su Ibrahim sun kammala karatunsu ,nan suka koma Kd bbu jimawa Ibrahim yasami aikin banki, yayinda abdullahi shiru sbd takardunsa basuyi kyau ba..
Hakan yasa Musa bude masa shago yana siyarda kayan provision “akuma lokacin ,Ummi ta haifi Yusuf .cikin ikon ALLAH Ibrahim yanasamun cigaba sosai ana cikin hakan yahadu d zainab(mommy) shikuma abdullahi zulai(mama zulai)nan suka sanar d yayansu ,bbu bata lokaci yasayi fili babba yace anan kowa zai Gina part nasa su zauna bayason rabuwa dasu ,sunkuma ji dad’in hakan sosai.
” haka kuwa akayi kowa yagina nasa saidai na abdullahi ne koma baya sbd bawani haline dashiba sosai kamar su,hakan tasa suka ida masa ,bbu bats lokaci aka d’aura aure aka kawo amare ,zainab wacce ta kasance yar masu Hali sosai dan Mayan dakinta zaka gani ka gane hakan,wannan dalili yasaka zulai jin zafinta da hassadarta g zainab harda ma binta sannan ta lura duka acikin mazajan ,mijintane koma bayansu,yyinda Suleiman any time yana gun zainab dan ana kawota jininsu yahadu sabanin zulai dabaya zuwa part dinta , dan bbu fuska alokacin da aka kawo su zainab yah Suleiman yana dan 6years .
Basu jimaba d auren musu d Ibrahim suka tafi hajji sukabar abdullahi hakan kuwa bakaramin bakin ciki zulai tajiba nan taita zuga mijin ai cutarsa sukeyi miye miye tun baa yarda harta zugasa ya yarda koda suka dawo sai yarima bays bays dasu tun suna tambayarsa har suka share ..
Zulai taso su hada kai d mommy su ware Ummi sai mommy ta k’i yarda d hakan,aiko saita shiga mugun nuna musu kiyayya ,sukuwa suka zauna cikin girmama juna dan Ummi ita tasakasu yah Suleiman su rika cewa zainab mommy zulai kuma mama ,dama ita Ummi suke ce mata ,shikuma Ibrahim daddy sa abdullahi Abba ..
Shekarsu daya ,zulai tahaifi yaseer ,bayan shekara2sannan mommy ta haifi Usman ,befi 5month ba aka haifi zubaida ,dg nan sai Mommy ta haifi Muhammad, itama zulai tahaifi Habib ,alokacin kuwa ita Ummi yaranta 5dan bacin Yusuf ta hafi yara 3 Habiba sadeeq da Auta Fatima..dg nan sai zulai ta haifi mace wato Rukayya alokacin kuma mommy Nada cikin iftihal…
Wanda da d’an gidanta akayi rain on cikin sbd yana bata wahala Wanda alokacin yah Suleiman yana dan 15 yaers aka haifi iftihal kada kuso kuga murna gun yah Suleiman abinda baitabayi ba aduk yaran da aka Haifa bayansa ,bbu kunya yyi Kane Kane dashi acikin mata ana zaman barka dashi yana mugun jidake babyn ,da kansa yace shi iftihal yakeso asakamata,bbu musu daddy ya yasaka mata ..
Tundaga nan yah Suleiman yashiga rainon iftihal indai kaga basa tare to yana skul. tun bata shaidashi harta ganesa ,sunansane farkon iyawa abakinta wato yah ile ita ce ke kiransa da hakan.
Bayan anyayeta gun yah Suleiman ta koma ,shine wankanta wankinta tsarkin kashinta komaima hartayi 3yaers sannan ta koma gun mommy akuma lokacin yah Suleiman ya kammala secondary skul din sa zai tafi karatun soja sbd hakane burunsa yataimaki kasarsa .
Alokacin dazai tafi ansha daga sbd yadda iftihal ta nuna Sam ita ah ah duk ta rikice d koke koke ,hakan yasa yace yafasa ,saida daddy yyi d gaske tukum sannan yatafi ,sai yasamu Hutu yake dawowa gd ,Wanda daddy duk bayan2 weeks sai yatura masa k50 ,kuma shima abbu natura masa dandai na daddy sunfi yawa sbd daddy yanxun yafisu karfi..
Gefe guda kuma mama zulai najin zafin hakan kan fifikon da akeyi agidan aganinta anfi ji d iftihal d yah Suleiman,sabanin su yaseer dan 15years da zubaida yar 10 users yaran da basuda tarbiya ko kadan uwarsu ta batasu dan ma yah Suleiman yasaka ido akansu sosai dan ko gabanta hukuntasu yake dan naga daukar raini ,Dan iyakarsa d mama zulai gaisuwa dan yagama karantar halayenta..
Saidai fa kuma zulai tayi wani mummunan k’udiri aranta saura kiris hakanta yacimma ruwa..
Yah Suleiman kyakkyawa ne ajin farko dan samunsa acikin maza sai antona dan guy din yahadu b karya ,farine dogo ba canba ,yana siffan ingarmun mazaje dan yanda faffadan kirki jikinsa amurde yake ga bakin gashinsa na Fulani usuli da sajensa da yyi lub afuskarsa yakara masa kyau ,dariya namasa wuya indai yyita to tarene da angel dinsa ,ga wushiryarsa dke tsakkiyar hakoransa inyyi murmushi ta fito abin Burgewa ne ga katuwar sallayarsa dke atsakkiyar goshinsa baki kirin tasake haskasa kai fadin haduwar yah Suleiman bata time ne gashi kwata kwata mata basa gabansa dan da wuya yashiga gun dkeda mata wata batace tanasonsa ba yanada tauhidi sosai d sosai …hakan yasa inyasha gun dake da mata sai ya daure fuska dama gashi d kwarjini kamar betaba dariyaba da hakan yake samun sauki abinda.miskiline na karshe ko acikin friends dinsa, shiyasa suke masa lakabi d (big man)inkagansa yana fira d fara’a to da iftihal ne ,wacce duk abinda takeso yana mata ko abun yyi yagani na mata sai yasiya mata gata da shegen cin naman tsiya indai yana gd duk dare saiya siya mata ,kannensa na mugun shakkarsa dn bbu wasa .
Iftihal kyakkyawar yarinya ja ce tanada pink lips da idanuwa Manya masu sheki ga girarta sbd cika takusa hadewa ga
ga hanci har baka intana turo dan karamin bakinta tafi kyau ga gashi hargadon baya ,mama zulai najin zafin wannan kyawu na iftihal…
Cigaban labarin…
Share ..
????????mmn fareesa ce✍????✍????
mmn fareesa ce✍????✍????[3/19, 6:08 AM] Itz B Y ebrerheem:AWESOME WRITER’S ASSO..????
(palace of excitation and pleasant writer’s)
INA TARE DA ITA !
????????????????????????????????
(bansan ita bace)
????????????????????????????????
Story &written by mmn fareesa
????5&6
Cigaban labarin…
Suna isa bed room d’in sa ya ajiyeta kan bed hade da janyo k’atuwar trolley d’insa ya aje gab da gadon yabud’e ,k’uri d ido iftihal tayi tana kallon abinda ke sama koba a fad’aba tasan tsarabartace ,su sweet ne d chacoolat sai biscuit da kayan Kitso ihun murna tayi hade d fad’awa jikinsa cikin jin dadi tace yeeeeeee!yaya ni d’aya… Murmushi yyi yaja hancinta yace oh my angel duk murnance haka ?”tace eh mana tana fara’a…hade d tashi tsaye “ahankali yace tafiya ma zakiyi kibarni ko firar baza’amunba?” yafada yana wani daure fuska irin na yara!”dariya tayi tace lah um um yaya zanje na boye abuna sai mommy ta mun wanka sainazo muyi firako ?”tashi yyi yace eh to amma muje narakaki kayan sun miki yawa ko bbu musu ta dauki ledar sweet 2yad’aukar mata sauran yabita har parlourn mommy, suka sami su Osman d Muhammad na kallo nan sukayita masa sannu ya amsa ,saida yarakata har bed room d’in mommy dan yasan mommyn bata ciki sbd alokacin tana sashen daddy ,sannan yafito yabarta ciki..