INA TARE DA ITA BANSAN ITA BACE 11-20

Bayan sallar la’asar mlm Haruna ne d matarsa kuluwa suke tafe zasushiga cikin k’auyen dg ganinsu kasan dg tafiya suke mai Nisan gske sbd kayan dasuke tafiya dsu ahannunsu…mlm Haruna yakalli matarsa yace oh kinga garin nan namu duk yacanxa mun anyi gyara sosai harda titi…kuluwa tace hmmm mlm kenan ai shekara 6ba wasa bace !kaduba fa shekararmu 6 rabonmu da garin nan sai yau Muka dawo mudan zauna mukoma dan gsky binni d dadi zamansa…kafin mlm Haruna yyi mgn iftihal dke yashe cikin ciyayi ta kwallah kara!had’e d cewa yah ileeeeeeeeeeee!dan ALLAH kazo,inane nan gurin?”da sauri mlm Haruna yakarasa gun, ciyayin yana adduar Neman tsari sbd shi malamine kuma masani kuluwa dke biye dashi yace um um mlm kabi fa a hankali wannan rayuwa,yace bbu komai d izinin ALLAH had’e da cewa tadakata nan ,shikuma yamatsa gurin…kyakkyawar yarinya yagani tana waige waige da alamar tsoro atare d ita kuma yanayin jikinta yanuna masa dg birni take kuma gdn wadata..
“Ahankali yace yarinya dg ina kike?”
Atsorace iftihal ta juyo ,jikinta na rawa ganin ta wani guri b gidansu…sake tambayarta yyi saita saka kuka tace ina yah ile yake ka kaini gurinsa dan ALLAH tafada had’e da cigaba da kukanta….
Atake mlm Haruna yagane akwai wata akasa duk yadda akayi wannan yarinya tanada makiyya,cikin dubarunsu na masana ,yace eh yana gdna muje can inkaiki gunsa amma kiyi shiru kinji ko?”
Ta shi tsaye iftihal ta yi tace to d gske kake?”
Yace eh xo muje ,bbu musu ta nufi gunsa, yyi bismillah had’e da sabarta akafadarsa suka fito hanya gunda kuluwa ke tsaye…
Baki bude kuluwa tace oh mlm wannan yarunyarfa ?”yace eh banason tambaya nima yadda kika ganta haka naganta ,muje gd nasamu tayi shiru kada kisake sakawa tayi kuka…kuluwa tace oh masha ALLAH kyakkyawa d ita ,inama ace yarmu ce muma ALLAH yabamu..
“Mlm yace ameen.”
Mikawa kuluwa ita yyi yace goyata ,kinsan ansan bamutaba haihuwa d anganta zaatamana tambaya”,karbanta tayi had’e da bude wani akwati ta Ciro zani ta goyata,yyinda iftihal tayi shiru sai binsu d ido take itadai burinta suje gdn taga yah ile dinta kawai…
Bayan ta goyata ,mlm Haruna yadauki sauran kayan su suka ida shigowa garin ,gab dazasu’isa gidan dasuke suka hadu da baffa habu(yayan mlm Haruna ne) yatsina fuska baffa habu yyi yace oh aina zata bazaku dawo gd asalinkaba sai dai ka mutu gun yawon tsangaya,shekara d shekaru kuntafi in ita kuluwa ba yar garin nan bace ai kai dan nan ne ko?”kodayake tunda baku tab’a haihuwa ba ai dole kuki garin nan ….cikin kosawa d gazawa d maganar baffa habu mlm Haruna yace hmm yaya kenan kullum sai kamun gorin haihuwa to yau ga yata nan sbd ita nadawo garin nan kuka jini nah …yafada had’e da daga hijab din kuluwa ,atake kyakkyawar fuskar iftihal ta bayyana ,cikin mamaki baffa yace dgske wannan y’ar kace?”mlm yace eh ,kasan cewar kulawa jajir take kuma kyakkyawa ko ancemaka yartace dole kayarda d hakan,su baffa sai akayi shiru yawuce had’e da yimusu sallama…
Kuluwa na kokarin mgn mlm yadaga mata hannu ,nan suka ida isa bakin k’ofar gdn mlm yabude suka shigo d addua hade d sallama..
gd ne matsakaici ,Wanda duk kauyen in akacire gdn mai gari to bbu kamar gdn,ginin simintine ko ina harda bayi ,daki 3ukku ne daya azaure inda yaran mlm ke kwana masu karatu gunsa, mlm Haruna dakinsa 1sai kuluwa 1 d’ayan na bakine sannan basa yin kiwo irin na mutanen kauyen kuma kuluwa nada tsabta sosai..
Suna shiga ta sauke iftihal ,wacce ko zama batayiba taketa tambayarsu ina yah ile yake? “Mlm yace ta nutsu sai anjima zai xo yaje yadawo ,nan tasaka kukan shagwaba ,mlm dkeda son yara yasabeta yana rarrashinta yafice d ita waje..
Nan kuluwa ta tashare gidan da dakuna, nan gidan ta wanke bayi da yyi kura sbd sunada rijiya agidan tuni gidan yadakko haske ,tana goge ledar kasa mlm yashigo sabe d iftihal ,a hannunta d daurin nama gashashshe da yoghurt, sai wani a hannun mlm ,zama yyi ya ajiyeta yakwance mata naman yata sa mata gaba yamikawa kuluwa nata tayi godiya had’e da cewa bara nayi sallah sai anmata wanka ko?”
Mlm cikin jin dad’i yace to ,dan tunda yaga iftihal yakejinta tamkar y’ar sa ta cikinsa sai nan nan yake d ita, to Itama kuluwa haka ta ji son iftihal..
Iftihal kuwa kasancewar ta da son nama gashikuma tanajin yunwa aisaita cin abunta tanashan yoghurt harta cinye Ta’s ,mlm yyi murmushi yace to yata yasunanki ?”
Kallonsa tayi tace angel !maimaita Kalmar yyi yasan basu suna ne na ,Kalmar turancice ,amma saiyakalli kuluwa yace gsky yarinyarnan akwai abubuwan Dana fahimta tare da ita ,amma insha ALLAH zanyi istihara d dare akanta duk Wanda yace miki meye sunanta ,kice nah nah tace to amma ai basu bne yace kice suna gyatumarkine d ita ,inmun gano iyayanta mu basu ita inbamu ganeba to muriketa amana ALLAH yabamu…
Kuluwa tace gsky ne mlm ,amma yanxun kaje kayi sallar ,sai kafita kasuwar gwanjo kasiyo mata masu kyau na yara mu aje kayan jikinta mu Adana dan gaba kuma muyimata photo….mlm yace gskyarki kuluwa ngd sosae da yadda kikebin umarnina ,cikin son mijinta tace bbu komai mai gidana na kaina ,murmushi yyi yatashi ,zai fita iftihal dke ta kallonsu tasaka ihu ita tana zuwa yakaita gun yah ile d’in ta.
rarrashinta kuluwa tahauyi ta goyeta ,sannan tayi shiru ,bayan mlm yafita kuluwa ta lallabata ,taje tayi salla sannan itama taci naman ,taje tacirewa iftihal kaya ta links ta adanasu ,Tamara wanka Ta’s tabarta dg ita sai pant..
Sannan tazo ta share kicin ta aza sanwar tuwon masara ,tadawo ta shimfida musu tabarma ,suka zauna sai Jan iftihal take d fira ,ita kuma tayi shiru tana turo baki…ana cikin hakan mlm Haruna yashigo d gudu iftihal ta fada jikinsa tana kukan yakaita gun yah ile …dagota yyi had’e da fito d wasu sweet d Loli pop yasakamata a hannu ,tuni tayi shiru yace oh yar baba haka kike d rigima?”
Kallon kuluwa yyi yana amsa sannun da zuwanta yamika mata ledar yace ga kayan kiwanke mata sai aruka saka mata kafin daivmusan iyayenta ,amsa tayi tace to yanxun kazo kayi wanka ,kaje ka huta na gyara maka d’akin ka…murmushi yyi yace to ngd…nan taje taja ruwa takaimasa bayi .
Wanene mlm?
Mlm Haruna haifaffen dan garin galgone ,su ukku ne agun iyayensu dasuka jima d rasuwa,baffa habu sa mlm sannan kanwarsu ,atine.
Mlm Haruna Mlm ne masani sosai dan duk k’auyen bbu mlm kamarsa ,yahadu d kuluwa agarin kano sunje wani waazi ,nan suka fara soyayya dashi ,kuma ita asannan duk jsce tayi shikuma beyi beko ba haka ta yadda ta auresa dukda yana dan k’auyen ,saidaifa kyakkyawa ne ,bayan anyi mgn aka musu aure aka kaita kauyensu.
Haka sukaita zama bbu haihuwa ,tuni suka maida lamarinsu gun ubangiji ,yyinda baffa habu keda mata da yara6 Wanda said surutu yakewa mlm yakara aure shikuma Yakiya,hakan yasa yyita masa gori..
Mlm Haruna yana yawon karatu gari gari kuma kafarsa ,kafar kuluwa,bashida wata sana’a ,malintakarnan ita yakeyi ,kuma yanasamu sosai bbu abinda baya siyawa matarsa naci ko sha ko sutura ,hakan yasa baffa habu kejin zafinsa…kuma mlm yasan d hakan to saima suka bar garin suka tafi zariya gun karatu shine suka dad’e haka har suka waiwayo gd tukum..
*******
bayan ,sallar isha’i mlm ne zaune kan tabarma ,iftihal na gabansa suna cin tuwo tare sai rarrashinta yake dan har yanzun catake anemomata yah ile dinta ,shikuwa mlm yafahimci tashak’u d ile d’in, kuma komai yatambaye bata bashi amsa sai tayi shiru..