NOVELSUncategorized

INA TARE DA ITA BANSAN ITA BACE 21-30

Share hawayen sa yyi yashiga lissafin shekarun iftihal yaga harta haura 14years tuni yashiga yin gumi sbd yadda gabansa yafadi fatansa ALLAH yasa ifteenshi bata mantashiba.

“ga wani mugun kishinta daya taso masa ” dan yasan yanxun ta isa wani yace yana sonta oh ALLAH dai yatsare masa ita…

Addua yyita yi dg nan bacci yyi gaba dashi.””””

Zubaida kuwa tunda yah Yusuf yace taje jikinta keta kirma ,tasan muddin inbata jeba kashinta yabushe.

,,,atsorace ta nufi part d’in su ,dakinsa ta nufa ta murd’a k’ofar had’e da yin sallama har sau3 ana3 ne ya amsa…jiki na rawa ta shige ,zaune tasamesa kan bed g lop top agabansa yana latsa….doguwar tsuka yyi had’e da cewa ke wawiyar inace ?”zakimun tsaye bisa kai”hmmm koda yake k’ila dan kinji abbu yace yabanike sadaka shiyasa ko?”to wlh yarinya zaki gane bakida wayo indai nine .”

Oya kije inner wear’s dina da jallabiyoyina na jike atoilet ki wankemunsu Ta’s,zaki wuce ko kuwa?”

Yafada cikin tsawa ,jikinta na bari sum sum ta wuce ,tafara aikinta ,azuciyarta tana zaginsa da ganin muguntarshi ,amma dole ta janyewa auren yah Yusuf inba hakaba kuwa tana tare da wahala..

Yana nan kan bed ta fito “ahankali tace yaya!tsaki yyi yace inajinki ,nagama ne dama ,yace ok kije kiwanke toilet din. dan murguda baki tayi ganin baya kallonta tace to pls zanje gun kamun friend dita..wani mugun kallo yamata had’e da cewa ke xonan!

Hakuri tafara bashi,tsakiyyi yaisa gunta yad’auketa d mari gigitacce …tasaki k’ara had’e da dafe kuncinta…cikin jin haushin ta yace kamun gidankui!bazakiba sakara kawai duk ranar da naganki gdn nan bbu hijab hmmm wlh kinsan saura ,maza kixo kimun kamun kunne .

Kuka tasaka tana bashi hkuri, kallonta kawai yyi beyi mgn ba jikinta na rawa tazo ta yi ,bece tabariba said a yaga takusa suma tukum yace tatafi.

Aranar d ciwon kai zubaida ta kwana mm zulai kuwa ta tsinewa yah Yusuf yafi akirga ,kuma tasha alwashin bazata bari ayi aurenba kota halin k’aka..

Bayan kwana,2
  *****  *****  *****
Ayaune mlm d inna kuluwa suka bar kauye sbd zuwa asibiti anemata lafiyarta.

Nah nah ce da Jidda zaune suna cin abinci, bb atine na gefensu ” ahankali tace dan ALLAH nah nah inkun k’are cin abincin kije kidebomana ruwa asola”nah nah tace to baba ai mungama bari na wanke hannu.

Nan ta tashi taje ta wanke hannunta ta d’au tulunta ta nufi gun solar.

Tana a hanya taga Dije k’awarta itama can zasu,maganar jamaa d tafiya sukaji abayansu ,Dije ta waiga yatsine fuska tayi tace hmmm wlh mai garine d jama’arsa mu basu hanya su wuce kafin su ida isowa d alama ta nan gun zasubi dan nasan gd zashi…itadai nahnah batace komai ba ,suka tsaya gefen wata bishiya yyinda mai gari mamuda d jamarsa suka tafo dan wucewa…saidai me kamar ance nah nah tad’ago kawai sukayi ido 4d mai gari yyata kuri d ido yanata kallo kamar zai cinyeta..

Tuni Dije ta lura ,suna wucewa Dije tace oh kinga wannan tsohon najadun yana ta kallonki to ALLAH dai yasa kada yace sonki yake dan xai iya wlh tunda haka yake bbu abinda ya iya sai auren yara jikokinsa bbu jimawa inyaga wata yasaki wata ya aura..

Zaro ido nah nah tayi tace oh to nidai wlh kwalelensa ALLAH yakiyaye tsoho dashi ina yarinya na auresa…adedenan suka iso gun dibar ruwan,nan kowace ta diba ta nufi gd…

Mai gari kuwa suna wucewa yasaka sallau babban yaronsa ya binciko masa wacece wannan yarinyar..

Haka kuwa akayi yazo yasanar dashi ai y’ar mlm.Haruna ce kuma baya gari ,amma ai habu yayansa na nan,mai gari yace akira masa baffa babu.

Aiko sallau yaje har gdn baffa habu yace yazo Mai gari na kiransa,cikin fad’uwar gaba yace ALLAH yasa banyi laifiba?”

Sallau yace ah ah alkhairi ne muje dai.

Bayan sunje mai gari sai nan nan yake d baffa habu ,nan suka gaisa.

kai duke mai gari yace dama dalilin kiranka…..

Share..

????????mmn fareesa ce✍????✍????[3/19, 6:08 AM] Itz B Y ebrerheem:AWESOME WRITER’S ASSO..????

(palace of excitation and pleasant writer’s)

  INA TARE DA ITA !
????????????????????????????????
    (bansan ita bace)
????????????????????????????????

Story & written by mmn fareesa

Banida bakin godiya ga masoya wannan novel naga comments bbu adadi agrps daban daban d PC kuyi hkuri darashin reply mutane sunmin yawa ngd sosae mmn fareesa natare daku duk wuya..????

wannan page din nakine kawata ta kaina my safeenah kiyi yadda kikeso dashi kinfi kowa son INA TARE DA ITA!????????

????27&28

NOT EDITED

Kai duk’e mai gari yace dama dalilin ki
ranka shine naga y’ar k’aninka tamun to ance baya gari kuma ba yanxun dawowarsaba.”
   Ajiyar zuciya baffa habu yyi yace hakane ranka shi Dade….mai gari yace nikuma gsky inason na aureta asatin nan yaya za ai?”baffa yace eh to ko kabari ubanta yadawo tukum”
Mai gari yace gsky nafiso ayi yanxun kuma duk abinda kakeso nabiya yanxun zanbiyya shi …..d sauri baffa yace to to to aibbu komai kabada komai aina isa da ita ko ubantama balle ita ”
fuska awashe mai gari yace to madallah,nan yafito da damin kudi yabashi yace nasada kine da Neman aure..
      Sannan yafito da wasu yace gashi wannan nakane bbu damuwa zanma kara maka wasu burina ta amince d aurena…..cikin zakuwa had’e da had’ama baffa yace bbu komai dolenta ma ta amince tunda batada wani uba ayanxun bacin ni ,yafada had’e da saka kudin cikin aljihu yace rana eta yau zaa d’aura muku aure d ita,cikin jin dad’i mai gari yace to shikenan jibi zanxo tadi gunta sai natambayeta me take so?”sai inbata kud’i ko?”azuciyar baffa yace nikuma na karbe dan bazan bar banzaba wlh dan wad’an nan kudin cima raina zanyi kuma nima nakara auren dasu..afili yace to shikenan sai jibin amma gdna zaka sameta kuma kazo d marece ”
Mai gari yace to bbu damuwa ,nan sukayi sallama yayinda baffa yakudurta gobe zaije yasanar da atine kota yarda ko karta yarda,kuma yatafo d nah nah takoma gdnsa da zama  har ayi auren..””

      ********

Ummi ce zaune da su Fatima Auta da Habiba suna break a dining area, Fatima ta ce nidai gsky Ummi in yah Usman baya sonafa? “Murmushi Ummi tayi tace hmmm yaro kenan ai duk cikinku bbu Wanda naji dad’in hadnsu kamar keda Usman dkuma iftihal da yayanku, ALLAH dai yabayyanata…
Ameen sukace baki d’aya, amma wlh banso hada Habiba d yaseer ba sbd halinsa ,amma kuyita addua nima zantayaku dan had’a zuria d zulai bawani abun jindadi bne..amma har gobe ina godiya ga daddynku d mommy sun nunawa zuria ta so d k’auna shiyasa naji dadi da zaku auri jininsa…Habiba takatse mata mgn da cewa nidai gsky Ummi banason yah yaseer acanjamun d…sallamar yah Suleiman ce ta katse mata mgn ,shigowa yyi fuska bbu walwala da kakinsa ajikinsa na sojoji yyi masifar yin kyau,dukawa yyi yagaishe d mahaifiyarsa yayinda kannensa suke gaidashi ya amsa atakaice”.
Ummi yakalla yace dama yanxun zantafi can wani k’auye gaba da kauyen KALGO anturamune dg office sbd bbu tsaro agurin, yan fashi natare fatake…zanyi kwana2 insha ALLAH ,bayan gurin yyi yadda akeso zan komo gd…murmushi Ummi tayi tace to babana ALLAH yatsare yabada sa’ar abinda akaje yi,yace ameen fuska asake alamar yaji dad’in addu ar ta..
      Nan kannansa sukayi ta masa fatan isa lfy nan yafice dg parlourn yanufi parking space yashige motarsa yabar gdn..

Previous page 1 2 3 4 5Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button