NOVELSUncategorized

INA TARE DA ITA BANSAN ITA BACE 31-40

Kaci amanar zumunci kuma insha ALLAH zakaga sakamako”

Ace y’ar kaninka Ku sanwaltar masa da ita bacin bagunka yabartaba”aguna yabarta sbd son zuciya ka kwaceta dg guna to bara kaji…

Afusace baffa habu yakatseta da cewa keeeeeee ! Atineki kiyayeni wlh”

Bansan inda ta tafi ba ,can kutashafa kokuma nace ketasha fa,inaso yanxun kibarmun gd tunda bakida mutunci…. Cikin kuka atine tace bbu damuwa zantafi ,saidai inaso kasani d’an hakkin da ka raina shike tsone maka ido…

Inaji ajikina sai nah nah tadawo insha ALLAH tazama abar kwatance kuma ina zargin dasaka hannunka ta bata..

“Yanxun in mlm yadawo kace masa me?”

“Afusace yace nace masa uwarki?”

Murmushin takaici tayi kafin tayi mgn Maimuna (kishiyar delu tayi sallama dan sadda abun yafaru tana k’auye gun suna)

Delu kuwa yatsina fuska tayi dan tana kishin Maimuna”acikin su atinece kawai ta amsa sallamar..

Maimuna tace lfy atine kike kuka?”

Tsaki baffa d delu sukayi atare..yyinda atine cikin kuka take sanar da ita abinda yafaru…

Salati kawai take yi tana mamakin halin mijin nata…afusace delu ta kalli baffa tace dan ALLAH mlm ni kakoresu ko sumin shiru…bata rufe bakiba atine tace hmmmm basai yakoremuba nizan fita ita kuma gdn mijintane…

Amma inaso kisani namiji duk yadda kike da shi baida tabbas kibi sannu wannan hura hancin banaki bne,kaikuma kaje kaida ALLAH inajiye maka tsoron haduwarka da Mlm wlh…bata jira amsarsuba dg shi har delun ta fice dg gidan tana hawaye…

Maimuna bata sake cemusu uffanba tabude dakinta ta shige tanajiyosu suna zaginta itada atine,amma bata kulasuba.,,,,

Haka atine ta koma cikin k’unci da damuwa agd tana adduar ALLAH yasa nahnah bagurbatacciyar hanya ta biba..

Burinta mlm da kuluwa sudawo gd”

        ********

Tanayin sallama tasami yah Yusuf kishingid’e kan 3seeter yana waya sai murmushi yake Wanda yafito masa da kyawunsa .

Sarai yaji sallamar ta sai yyi mata banxa”

Ita kuma tana tsaye bakin k’ofar tak’i karasowa ,tunda bai amsaba.

Sauraronsa take dan tagane da mace yake wayar…sai wani kwantar da murya yake qasa qasa yana mgn.

Wani haushi taji Wanda batasan daliliba ,kwalla taji a idonta tana tausayin kanta ,wani gefen na xuciyarta nasanar da ita ko ya aureki keda banxa duk daya kuke agunsa tunda da wacce yake so ..

Tunawa tayi da mukhtar saurayinta dake mugun sonta”lumshe ido tayi tana mugun jin haushin yah Yusuf kuma tasha alwashin tambayar mama wanne sharrune zatamai ?

Kodan kada ta auresa ta yarda zatayi hakan….muryarsa taji yana cewa baby bye zankiraki latter..

Yatsina fuska tayi ta bankomasa harara,cikin rashin SAA suka hada ido da ita. ”

“Wayyo jitayi hangar cikinta ta kad’a”

Ta shi yyi tsaye yace ZUBAIDAAAAAAA!

Nikike harara?”

Atsorace tace ah ah dan ALLAH kayi hkuri kada kai nakeba…doguwar tsuka yaja yace hmmm wlh inna kamaki zakiji jiki ,oya ni dallah kibiyoni kina fama da wasu shanyayyun idanuwa naki mitts…yyi tsaki.

Bed room suka nufa yabude ward rope yafito da tulin kayan wankinsa sunfi kala 12harda su suit da jeans yace ta wanke nanda awa daya intagama ta wanke toilet d’in da tayis d’in bango..

Kamar tasaki ihu sbd bakin ciki da bacin rai ayau ta tabbatar yah Yusuf mugune na karshe kuma baya k’aunarta ko kad’an.

Jiki bbu kwari ta kwashi kayan ta nufi toilet.

Shikuwa yayi kwanciyarsa kan bed ya lumshe ido..

A cikin toilet kuwa tana wanki tana tsinemasa yafi dubu bbu adadi tana mugun jin tsanarsa da haushinsa,said hawayen bakin ciki take ga wahalar wanki .

Da k’yar ta idar da abinda yasata dan takai2 hours aciki sadda ta fito anata kiran magrib..

Fuska bbu walwala ta iso gefensa yana shirin tashi yayo alwallah tace yaya nagama!

Harara yagalla mata yace ainasani basai kin fadaba ,kije kiyi sallah kidawo kisake karban hukunci sbd nakamaki kina hararata..

Ihu da kuka tasaka Wanda bata tab’ayi agabansaba da shure shure….lumshe ido yyi yana kallonta ganin yadda take abu tamkar wata yarinyar karama”

Ahankali yace ko kimun shiru ko na dakeki da belt kina jina?”

Cikin kuka tace dan  ALLAH yaya kayi hkuri nagaji ne wlh bazan sakeba…juyawa yyi yace kisake mana ,kibaccemun da gani…da gudu ta fice ta na nishi.

Shikuwa girgiza kai yyi yawuce toilet abinsa..

***** ****** *****

Yah Suleiman kuwa suna fita dg parlourn yacika ta yanajin haushinta yanufi parlourn Ummi yyinda iftihal kebiye dashi…

Zama yyi ransa adagule agefensa yajita kawai ta aza kanta akafad’arsa had’e da rike mata hannu guda tana wasa dashi Lamar yarinya….

Wani yarrrrrrrr!yaji da kasala ajikinsa amma bbu yadda zaiyi tunda baa hayyacinta takeba .

Murya qasa qasa yace oh baby kiyi mgn pls kinji ko anfasa wannan auren kinji?”

Itadai kallonsa take amma batayi mgn ba ,hannunsa dake cikin nata yakwace had’e da Janata hanci yace hmmm insha ALLAH kinkusa warkewa kona huta da aurnki da akeson azamun..

Amamakinsa sai yaga tasa hannunta taja masa hanci harda sajen fuskarsa ,besan sadda yyi murmushi ba dan Sak yadda angel d’in sa kemasa in suna wasa tayi masa..

By surprise yaga tayi murmushin itama yadda taga yyi ..wani fad’uwar gaba yaji ganin hakoranta da wushiryarta irin na iftinsa ne.

Wata zuciyar tace hmmm kabi ahankali ,gixone kawai dan itace aranka ,amma basa wani kama….hannunsa data rike had’e da azasa saman goshinta yadawo da shi hayyacinsa.

Kalonta yyi ,”ahankali yace sannu kin kusa warkewa ai Dr zaizo yamiki dressing gun,dan yafahimci gurin raunin kemata zafi…

Murdo k’ofar akayi ,Ummi ce tashigo had’e da samun guri ta zauna .

Shikuwa yah Suleiman saikok’arin zameta yake daga jikinsa amma taki yarda saima kokarin hawaye takeyi…

“Ahankali Ummi ta ce kayi hkuri banana kaji?kayiwa abbunka biyayya bazaka taba tab’ewaba duniya da lahira insha ALLAH.

Auren nan kadaukesa amatsayin kaddara dakuma jahadi ,ko yanxun kaga yadda take makale dakai bacin kuba maharraman juna bane auren shine maslaha agareku har ALLAH yasa tasamu lfy.

Sannan inaso kabawa makiyanka kunya gun yima abbunka biyayya tunda anamaka wani zato mummuna akanta kuma raina yabaci matuk’a..

Yah Suleiman yyi yakatseta da cewa insha ALLAH Ummi zanyi biyayya ga abbu sannan zankarbi rayuwa aduk yadda tazomun.

Sannan wannan matar kibarta Ummi kada kibiyemata dan batada hankali,amma duk ranar data kaini bango wlh zatayi nadamar dabata  tabayiba arayuwarta.

Ummi tace bbu komai ALLAH yyimaka albarka yakaremun kai aduk inda kake ,kuma insha ALLAH iftihal zata bayyana mudai cigaba da addua.

” cikin jin dad’in addu ar ta yace to Ummi bara natafi masjeed ”

Mike wa yyi tsaye …tuni y’ar tawa itama ta mik’e… Lolx,ahankali yace dan ALLAH Ummi ki riketa natafi masjid, gsky kada narasa jam’i!

“Tasowa Ummi ta yi Yakama hannunta,tuni tafara turjewa tana hawaye,shikuwa gogan sai aikomata da harara take yi,hanyar fita yyi yana cewa dan ALLAH Ummi kuyi mata wanka awanke mata gashinta sbd tsami take wlh..

Girgiza kai Ummi ta yi tace hmmm banana kenan itada akama dinki aka aiba ,a wankesaba ,adai mata wankan da dubara.

Bece komai ba yafita.

Ita kuwa sai da Ummi takira Fatima da Habiba suka tayata rarrashinta ,sannan tadena botsarewa.

Yah sulaiman be shigo gdn ba sai da akayi isha’i….

Part din sa yanufa …

Share..

Previous page 1 2 3 4 5

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button