INA TARE DA ITA BANSAN ITA BACE 41-50

Ban aikata abinda kake zargimmu dashiba ko abida?”
“cikin tsoro tace eh”
Tsaki yyi yace to tunda bakinku daya da ita bbu damuwa zanje yanxun insanardasu dan nasan angama sallah….muryar abida yaji tana cewa nidai Dan ALLAH zan fadi gaskiya kada kafad’a….yatsinafuska yyi had’e da watso mata mugun kallo yace aikin banxa ke har wata gsky ce dake.,,,
Yaseer jikinsa sai rawa yake dan beson abata masa suna kuma baidamu asirin mm zulai yatonuba ,dan haka yace pls yaya kasauraremu zamu fadi gaskiya….
Yusuf azuciyar sa yace anxo gurin.”
Kallonsu yyi yace kubiyoni..bbu musu suka bisa .
A part din Ummi suka nufa ,byn Yusuf yashiga suka bi bayansa, Ummi na zaune kan carpet tana lazimi..yyinda abbu ke kan 2seeter yana karatun alkur’ani mai girma.,,,,
Da tambayoyi fal afuskar abbu ya amsa sallamar su bayan yakai aya..
Yusuf ne yafara cewa abbu ina kwana?”
Abbu yace lfy lau lfy dai ko?”naganku haka tun gari be ida haskeba?”
Yusuf yakalli abida had’e da cewa ke kimana bayani… Yyinda Ummi tayi musu kuri tana sauraron ta ji mesuke tafe dashi.dan tunda tagansu gabanta ke fad’uwa..
Bbu boye boye abida ta zayyane musu komai akan abinda mm zulai ta sakata tayi dan tasan kobata fad’aba korarta z’a ayi ga suna mata kallon y’ar iska.
Salati kawai abbu keyi yana mamakin mugun Hali irin na zulai ,sainan yana jin tausayin Usman dabecimata komai ba tabisa da sharri haka .
Cikin bacin rai abbu yace wa yusuk jeka kiramun abdullahi da matarsa…nan yah Yusuf yafita dan kiransu…
Abbu yajiyo yakalli abida yace lallai dan Adam kenan dg yau zakibar gdn nan kin gama zamansa.,,
Ummi kuwa tazo mak’ura dan jitake yau bbu abinda zai hana tadaki mm zulai ko ita, ko ita..
Yah Yusuf kuwa yana sanardasu sak’on yafito.
“Mm zulai kuwa ta tsorata da jin kiransu ake da jijjifin nan” jiki bbu kwari tabi Abba dan jin kiran me ake musu..
Suna shiga taga yaseer da abida kai duke dg nan cikinta yafara juyawa had’e da jin gabanta na dukan Tara Tara.. Lolx
Ko gaisawa basuyiba abbu yakalli abida yace ke mamaita abinda kika fada”bbu inda inda ta sanar da su komai….tun kafin ta ida mm zulai ta fara borin kunya wai sharri ne zaa mata..
Sbd bacin rai da bak’in ciki Abba bece komai ba yafita…mm zulai na kokarin binsa Ummi ta cafkota had’e da makata ga bango tahau nusarta…
Gaba daya abbu yasha mamakin Ummi ganin yadda take dukan mm zulai sai ihu take ,ya yarda da akace mai hkri bai iya fushiba…
afusace yacewa su yaseer sufita itakuma abida ta tafi gd sun sallameta…
Abbu naganin sun fita yazauna kan kujera yana kallon su be rababa dukda dai anfi jibgar mm zulai duk da itama tanad’an kai duka…
Saidai Ummi ta jigata mm zulai sannan tabarta ,yyinda abbu yadauke kansa dg kallon su har mm zulai ta fita..
Zama Ummi ta yi tana nishi ,abbu yagirgiza kai yace banso kika daketaba ,amma bazancemata komai ba saidai duk radda ta sake makamancin hkn zanbasu mamaki wlh..
Ummi tace gsky alh mubar musu gdn ,nagaji da mugun halin matar nan da ya’yanta ,sannan gsky kajanye auren Habiba da yaseer gsky,yanxun in su mommy sun dawo suna sami irin Sharrin da aka soma usman zasuji dadi?dame zasuji ?”batan y’ar su ko kazafin da akama Usman?
Murmushiin takaici abbu yyi yace ah ah gsky bazan janyeba kisaka ido munata addua ,sannan maganar brain gd bata tasoba dan bata isa ba sbd ita muraba zumunci wlh dan insha ALLAH Ibrahim yakusa dawowa befi 5weeks ba sbd karatun su Muhammad Aida sunkai 1month da dawowa ma,sannan kuma bazan bari suji maganarba dan bbu dadi..
Kuma wlh koda sunci galabar yimasa sharrin nibazan yardaba sbd Usman yaron kirkine…Ummi ta katsesa da cewa hkne wlh ALLAH yashiryeta inxata shiryu ,sukuma ALLAH yamaidosu lfy ,,
“Yace ameen”
“Ahankali abbu yace dama inada niyar yimiki mgn inna gama karatu ,sai wadandan suka shigo”
Ummi tace to inajinka ALLAH yasa alkhairi ne,,,
Murmushi yyi yace shine insha ALLAH ”
Dama maganar auren Dana ce zanyi wa Suleiman ne da wannan yarinyar”shine yau amasjeed nike ma liman maganar had’e da Neman shawararsa …shine yamun tuni akan gsky akwai kuskure idan na aurarda yarinyar bbu San in iyayanta ,dadai da sanunsune to bbu damuwa, shine na tambayi Suleiman yanxun dazamu shigo gd a ina yatsinceta?”
Shine yacemun dg garin da yatsinceta zuwa nan awa4,gashi bata hayya cinta bara muje aduba iyayanta.
Amma nace masa yabari konan da zuwa sati 2ko 3sannan ta warware sosai koba da itaba sai muje garin da hotanta abinciki iyayanta..
Ummi tace wannan gsky ne alh nima nayi tunanin hakan “to amma yanxun anfasa auren ko?”
Abbu yace eh amma kuma tunda narigada nayi niyar ya aureta ,bayan anga iyayenta indai sunbasa bbu damuwa zai aureta dan hakanan naji kaunar yarinyar tamkar y’a ta…
Ummi tace wlh ko ni to ALLAH dai yabata lfy “yace ameen….kafin Ummi ta yi mgn yah Suleiman yashigo parlourn yaduka har kasa yagaidasu..
Bayan sun amsa ,nan abbu kesanar dashi anfasa auren ……murmushi yyi har fararen hakoransa suka fito.
” Wanda Rabon dayi irinsa tun kafin iftinsa ta bata”ahankali yace hkne abbu ai dama tun sadda kayanke hukuncin nafara maka mgn kace kagama yanke hukunci wlh dama abinda zantunatar dakai kenan saikaki saurarata..
Abbu yace hkne yanxun dai naga kana murmushi akan ance anfasa auren ko?”
To ba’a fasaba”insha ALLAH ,inharmun samu iyayanta zan nema maka auranta…
“Ahankali yace to abbu had’e da tashi dan Baron parlourn adaidai nan kuma, Fatima ta fito rik’e da hannun iftihal.”
Dukawa tayi tagaidasu abbu da yah Suleiman ,yyinda iftihal ke tsaye tana raba ido.
Yah Suleiman yasaci kallonta …suka hada ido lumshe idonsa yyi dan saiyaga tamasa bala’in kama da angel dinsa..
Gurinsa ta matsa …. da sauri yanufi k’ofar dan fita tuni tabi bayansa shikuwa besan tabiyosaba..
Ummi kuwa girgiza kai kawai take yi ta kalli Fatima had’e da cewa muje kitchen ahada break fast! Amma yarinyar nan tayi brush?”
Fatima ta ce eh wlh tayi da kanta bansan Wanda ya koyar da ita ba…abbu dke shirin barin parlourn yace eh gsky yarinyar Nada saurin ruk’e abu..
************
Abba kuwa koda yafita sashensa ya wuce rai bbu dadi dan mm zulai ta kasa Bango…yana nan zaune ta shigo kamar an jehota da bakinta afashe tana matsar ido..
Tsaki Abba yyi yace wlh naso tamiki Wanda kika kasa tashi ,bakida tausayi baikda mutunci ,ace wai yan uwana su kikebi da sharri ….cikin jin haushin kalamansa tace wato bazaka dauki matakiba ko?”akan dukan datamun”
Hararar ta yyi had’e da Jan doguwar tsuka yace wlh daba dan yaranmu ba wlh da tuni zamana dke yakare amma wlh ko baran badad’e saina kara aure ..
Sbd zama dake ke daya matsalace…zaro ido tayi had’e da cewa mekace?”
“Yace abinda kunnanki yaji” bejira amsartaba yabar dakin da nufin yaje yabawa abbu hkri.
Ita kuwa yabarta da baki fashe tanata masifarta ,had’e da jiran yaseer yashigo tazagesa Ta’s tunda yana gani abida ta tona mata asiri yakyale..
Haka kuwa akayi yaje yabawa abbu hkri da sanardashi zai kara aure indai yasamu wacce tamasa,abbu kuwa yagoya masa baya sosai ,sannan suka kira yaseer suka masa Ta’s sannan aka kira Yusuf sukace yyi shiru kada yabari Usman d’in yaji maganar yace to ….
Yah Suleiman kuwa tafiya yake besan tana bi…..