NOVELSUncategorized

INA TARE DA ITA BANSAN ITA BACE 51-60

Azaune tasamesa ,nan suka sake gaisawa yashiga yima ta nasiha da tuni akan rayuwa had’e da hakurin zama da mutane.

Ahankali tace wai Abba d gske nan zakabarni?”

“yace eh gsky” sbd banaso kisake komawa kauyen nan gsky kuma dan ALLAH kuyimun biyayya dukda ke yarinyace dudu shekarunki  15 ne amma musulunci ya yarda namiki aure..

Hawaye takayi ,mlm yace kiyi hkri kinji?”insha ALLAH auren nan alkhairi ne gareki..

Mutanan nan sun mana komai arayuwa basu nuns komai garemu ba ko San in suwanene mu sukace inba dansu aurenki ,aiko sunyi ,kuma nafahimci sunada kirki da daraja dan Adam tun dg kanki,shiyasa nabasuke ,duk da haka nima zanyi istihara nanemi zabin ALLAH nakumasa ayuba dke d’an gari yyimun bincike dukda na yarda dasu ..

Ahankali tace to Abba !amma naso inkoma gd wlh yace bbu damuwa zanxo miki dasu su ganki insha ALLAH..

Firar su suke ta yi gwanin shawa’a ,batabar dakinba  saidai aka kira azhar tukum sukayi sallama ta nufo sashen Ummi..

Samun Ummi tayi tana share parlour ,ga dining table  nan anshirya abinci samansa..

Da sauri ta karbi sharar ,Ummi na cewa ki bari kinji ,amma ta Karba ta share Ta’s tayi mopping ,sai sannu Ummi ke mata azuciyarta tana yana tarbiyyarta.

Tambayarsu Fatima tayi Ummi tace suna dakinsu suna bacci..

Murmushi tayi tace bara natadasu muyi sallah,Ummi tace eh dakin kyauta dan lokaci yyi,nan ta nufi dakin yaran yyinda Ummi ta wuce dan yin tata sallar.

Tana sjiga ta tarasu ,duk sukayi arwallah suka yi sallar ,suna gamawa ,nah nah tafara karatun alkur’ani mai girma cikin sweet voice dinta mai zaki tana fidda hartufa cikin hafshar Wanda ke waiting parlour yanaji..

Su Fatima sukayi mata kuri da ido ganin duk karatun nan datake dakane bbu littafi ,azuciyarsu sun yaba da iliminta..

Yah Suleiman da shigowarsa kenan ,kunnensa yajiyomasa zazzak’ar muryarta tana rera karatun alkur ani mai girma..

Ummi ya kalla had’e da cewa Ummi wake kara tun nan cikin yaran nan ?”

Ummi tace hmmm baby ce fan”

Yatsina fuska yyi .had’e da cewa ina daki akaimun abincina acan”.

Ummi tace to ,nan yafice yana mamakin baby azuciyarsa ..

Baby nah nah bata ida karatunba saidai takai aya ganin yadda su Fatima ke santin muryarta.”,,,

Fitowa sukayi parlour ,Ummi ta mikowa baby basket had’e da cewa ungo kikaiwa yayanku yana dakinsa…

Jikinta na rawa ta Karb’a dan  batasan yin musu da Ummi ,”ahankali tace inane dakin.?”

Fatima tace muje narakaki.

Jikinta sai rawa yake ga fad’uwar gaba yanaji ,suna fita tace amma dan ALLAH ki kaimasa sai najiraki ko?”

Fatima tace um um bbu ruwana wollah ,kadai kijamun yatattakani ,tunda ke aka aika kije wlh zaifi sauki .

Adede nan suka iso d’akunan samarin gidan ,ta nuna mata dakin farko tace nan ne nasa..

Gabanta na dukan Tara Tara tanufi k’ofar had’e da murdawa.

Tashiga tayi sallama..

Share

????????mmn fareesa ce ✍????✍????

AWESOME WRITER’S ASSO..????

(palace of excitation and pleasant writer’s)

   INA TARE DA ITA!
????????????????????????????????
    (bansan ita bace)
????????????????????????????????

Story &written by mmn fareesa

Wannan page din nakine beauty baby kiyi yadda kike so da shi inaji dake irin totally dinnan????????

????59&60

NOT EDITED

Tashiga tayi sallama amma tanajin tsoro azuciyarta!

Karewa parlourn kallo tayi ta hango sa kan 3 seeter ya kishingid’a yana karanta jarida,sanye yake da farar jallabiyya ,azuciyarta tace oh mutumin nan akwai jinkai kodan yaga yanada kyau !oho..

Sake maimaita sallamar tayi..can ciki ciki ya amsa yana wani had’e rai.

Ajiye masa basket d’in tayi gabansa”ahankali tace gashi inji Ummi!
Beyi mgn ba ita kuma ta juya dan tafiya…keeeeeeeee!baby xonan”yafada tamkar bashi yyi maganarba.

Tunani take azuciyarta wacece baby ?”ko watace me suna hakan adakin ,tafiyarta tacigaba da yi hartakusa kaiwa k’ofar fita atsawace yace kikasake kika fita bada izinina ba zaki gane kuranki…

Turo baki tayi cikin shagwaba tace Toni ai basunana baby ba ,nah nah nisunana .

Tsaki yyi yace da hakan kowa ke kiranki agidan nan ,dakuma hakan zaacigaba da kiranki ,kuma kik’i amsawa kiga yadda zanyi dke yar kauye kawai da ita kazama me kashin kwance….

Ai tuni baby ta fashe da kuka da dire dire ita wlh batasonson tunda yake cemata mai kashin kwance.

Dariyar data taso masa yadanne yace eh ance me kashin kwance kije ki tambaya kiji aikinayi kullum sai na wanke miki kashi da asubar fari shine dankin samu lfy kike wani iyayi ko?”

Harararsa tayi had’e da murguda masa baki tace eh d’in aidai konayi ba ahaiyacina ne ba ko?”kuma ni bansanka yah Abbas nikeso yafika s….tsawar dayyimata ne yasata yin tsit.

Cikin kakkausar murya yace keeee!dakata inkika sake maganar wannan dan kauyen me yellow d’in hakoran nan xanbaki mamaki sokuwa dke nima ai basonki nikeba dazaki birgeni ,shine kicewa mlm bakyason auren dazanyi farin ciki da hakan,Dan inba my angel d’ina ba bbu wata macen dazanso har abada koda zanso wata toko Rabin son danikewa iftina bazata samu ba.

Batayi mgn ba amma tatsintsi kanta daji n haushinsa ,juyawa tayi dan tafiya ta murda k’ofar… Wani Jan kwata kwaren kadangare yyi saurin shigowa kafin ta fita…

Kara tasaki had’e da juyowa da gudu ta fada jikin yah Suleiman tana cewa wayyo zanmutu dan ALLAH yaya kada kabari yayimun wani abu….da sauri yace ke ki nutsu ki dagani Nina fitar dashi sai sani ihu kike mana!

Cikin shagwaba ta ce to kaini ciki ko gurinsu Fatima dan ALLAH kaji?”

Lumshe ido yyi dan saita tuna masa da iftinsa itama tsoron kadangare take yi sosai.

Hannunsa data girgiza yadawo da shi tunaninsa ,cikin kuka tace kayi wani abu yanafa cikin dakin nan!

Cikin mutuwar jiki yace ke baby ki cikani ko!cikashi tayi tana hawaye sai kuma yaji tausayinta..

Cikin rarrashi yace bazaimiki komaiba !make kafada tayi tace um um nikafitar dashi yanxun pls.

Nuna mata wata k’ofar yyi yace kishiga na koresa inba hakaba kekika sani..

Bb musu ta Shiga ciki,Ashe bed room d’in sa ne ,azuciyarta ta yaba da tsabbartasa ,zama tayi ko ina sai kamshi yake ita kanta jikinta kamshin turaren sa yake.

tafi minti 15zaune kan bed din sa…yashigo da sallama yace oya matsoraciyya kifitomun adaki kin wani zaunamun a saman bed .

Bata ce komaiba ta fito gun basket d’in ta nufa tayi serving nashi..yanata mamakin ta tana yar kauye harta iya serving d’in mutum inzaici abinci..

Zama yyi kan carpet ta ajiye masa gabansa had’e da zama kusa da shi sai sukayi tamkar mata da miji…

“Ahankali yace ke kinci abincin?”

Bata kallesaba tace ah ah”

Yace to muci tare kinjiko?”

Ba musu ta jawo spoon suka fara cin abincin ,sai tsakura take ,yyinda yaketa cin abincin sa hankali kwance .

Can tace yayaaaaaa!

Kallonta yyi ,”ahankali tace nakoshi!had’e rai yyi yace ah ah tare zamucinyesa dama bakison cin abinci ko?

Cikin shagwaba tace dan ALLAH kayi hkuri wlh na koshi kuma zantafi gun su Fatima …

Beyi mgn ba yaci gaba da cin abincin sa.

Har yagama sai turo baki take ,tashi yyi yace ki gyara gurin yanxun kigyaramun dakin…

“Ahankali tace to amma inna gama zantafi ” had’e rai yyi yace oh baby kin rainaniko?”

Cikin kukan shagwaba ta ce ah ah yaya kadafa anemeni,juyawa yyi yana tafiya yace Toni na rikeki ne?”

Batayi mgn ba yyi ficewarsa ,tashi tayi ta gyara parlourn da bed room d’in, byn tagama ta kwaso kayan abincin ta nufo part din Ummi ta zauna anata fira da ita…

Previous page 1 2 3 4 5Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button