GURBIN IDOINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 21-30

Saida mutane suka rake sosai aka fara Ankara da abinda yafaru ganin rudewa da tashin hankali da Abdulsamad yake ciki da yawa wainda suka dauka sune basuji sunan daidaiba suka fahimci cewan daidai sukaji Ashe auren ne dai bada Dr Abdulsamad aka dauraba.

Take kurar hayaniya tafara kaurewa daga gurin
Ganin Abdulsamad na Neman zarewa yasa Abbi daya Gama sallamar baqinsa ya Kama hannunsa sukai cikin babban gidan na Alhaji babbah.

Qanin CM Professor Ibrahim shine ya tsaya yaqarasa sallamar sauran jama’ar aka watse wasu nata sake sawa auren albarka wasu Kuma na shiga mamaki da son Jin yanda wannan mugun Al’amarin yafaru hakama wasu take suka ringa maimaitawa wainda basujiba cewan sunan fa AA MAJEED ne aka daura dashi.
Mamaki da firgici wasu suka Kuma shiga Jin sunan Wanda aka daura dashi din aikuwa take tun anan suka fara shigar da gulmar Internet.

An watse tsaf ba kowa Dan hakan Alhaji babbah ya kalli su Alhaji buhari dake cikin mummunan yanayi na bacin Rai da fushi.

Cikin sanyi da taushin murya ga Wanda baa kyautawaba yace”

Alhaji buhari kuyi hakuri nasan baa kyauta mukuba tako Ina Musamman da baa sanar daku komaiba ko fahimtar daku komaiba Saida kukazo cikin baynar jama’a hakan tafaru.

Dr Abdulsamad dake tsiyayar wasu ruwan zufan tashin hankali da fita hayyaci ya kalla duk saiyaji jikinsa yayi sanyi da tausayin Abdulsamad din sbd duk Wanda ya kallesa yasan yana tsananin son Inayah so Mai tsanani,

Tayaya Za’a kallesa ace Masa uwarsu daya,
Uban ne kawai Basu saniba ko dayane tunda A MAJEED cewa yayi uwar kawai yasani itama a bisaga qaddara.

Shi kansa Dr Abdul idanuwansa duka da hankalinsa suna kan Alhaji babbah sbd ya fahimci agurinsa zasuji abinda suke buqatan ji Wanda zuciyarsa ayau harbawar datake yasan ta wuce kowane irin tsari da akeson zuciyar Dan Adam ta buga.

Babu wani yaren dazai gane ayanzu idanba na maganar aurensa da Inayah bane.

Dan jinjina maganar dake bakinsa Alhaji babbah yiyi tareda dauke idanuwansa daga Abdul ya maida kan su Alhaji buhari dasuke manya zasu fahimtarsa a natse yace”

Ita wannan yarinya Inayah wadda mahaifiyar Abdulsamad ke Kira da Ayshatouh ‘yar mahaifiyar Abdulsamad ce wadda ta jima da Bata tun jarinta Wanda A jiyan bayan haduwar mahaifin Inayah Wanda yanzu zance mijinta da ita mahaifiyar tasa suka tabbatarda Dr Abdulsamad da Inayah uwa dayace ta haifesu,

Dr Abdulsamad da Inayah uwarsu daya Kuma kaman yanda duk muka sani Babu aure tsakaninsu,

Sauyin Wanda aka daura dashi Kuma wannan nine Nan na tayasa yanke wannan hukuncin sbd kaman barazana da ita mahaifiyar yarinyar takeson tayiwa MAJEED Dan hakan muka yanke hukuncin ya aureta.

Dan haka a taqaice ABDULMAJEED shine ya aura AYSHATOUH INAYAH,
Shine mijinta ayanzu,
Sauran bayanin Inda ita mahaifiyar Dr ta samo yarinyar har suka Zama uwa daya da Dr wannan saidai aji daga gareta.

Wani mummunan shock da matsiyacin zufane ya fesowa Alhaji kabiru zuciyarsa na harbawa da mamaki ya juya ya kalli malam Umar Dan uwansa Wanda harya fisa jiqewa jagab da zufa.

Alhaji buhari daya Gama samun qullewar Kai da mamaki da Yar rudewa yace’

Inayah kuma Yar Hadiza?
Tayaya?
Garin Yaya?
Yaushe?

Shaqewa muryar Alhaji kabiru tayi a Rikice murya na yankewa yace”

Inayah itace AYSHATOUH????
‘yar da Hadiza ta Haifa ranarda mahaifiyarmu ta rasu??

Da tashin hankali malam Umar ya karba da cewa”

Innalillahi wainnan ilaihrrjiun
Tabbas Hadiza ta haifi ‘ya takuma saka Mata Ayshatouh.,
Idan har ya tabbatarda Hadiza ce dimun wadda tabar Masa ‘ya to tabbas kuwa wannan ‘yar ta Hadiza ce halak malak sbd ranarda ta haifeta ranar tabar gida.

Sai alokacin zufa ta karyowa Alhaji buhari Jin dai ta tabbata Hadiza haihuwa tayi ba aure bayan rasuwar salisu.

Da sauri malam Umar daya fahimci tunanin dake zuciyar Alhaji buharin yace”

‘yar Hadiza ‘yar halak ce
‘yar sunna Dan kuwa cikinda salisu yabarta dashine muma sai daga baya muka Ankara da hakan Dan haka ‘ya ‘yar halak ce
Uwarsu daya ubansu daya da Abdulsamad gashinan zaun…..” Ya qarasa fada Yana waiwayawa Inda Abdulsamad ke zaune sai kawai sukagansa zube baya numfashi da alama ya jima da sumewa Basu saniba sbd tashin hankalin da kowa yake ciki.

Arikice Alhaji buhari yayi kansa shida malam Umar suna Kiran sunansa Amma da alama ba sumar kadai yayiba kaman harda attack yasamu.

Innalillahi wainnan ilaihrrjiun””Alhaji buhari yake fada Yana kamo Abdulsamad din da qarfinsa
Ba arziki Dole zaman bayanin yaqare sukai asibiti dashi hankali tashe.

Bayan fitarsu kallon Abbi Alhaji babbah yayi yana nazarin halin tsananin damuwar dayake ciki da rashin ta Ina zai Kama wannan rakitaccen Al’amarin.

Tausayinsa ne Dana Abdulsamad ma dayafi kowa tausayi yanzu Dan yasan Al’amarin zai daki yaron sosai sudai dama saukinsu da hamdalar dasuke shine da baa daura aurenba da komai yafi lalacewa uwa daya uba daya.

Bayason qarawa MAJEED damuwa da wasu zantukan Dan haka ya taqaita da cemasa,

“MAJEED kaje gida kasamu ka nutsa kanka ya sake kafin shima Abdulsamad asamu lafiyarsa saiku zauna duka kuyi taron fahimtar juna,

Itama yarinyar kada kace zaka kasa karban wannan qaddarar sbd ko ahakan Allah ikonsa ne ya nuna,
Haisawa sukace matar mutum kabarinsa
Allah yayi itace matarka shiyasa Bai baka ikon aureba tun kuruciya har gashi manyanci nason zuwa hakama rabon zamtowarta matarka ya hadaka da mahaifiyarta harta dawo hannunka dan ka tarbiyantar da matarka da kanka Dan haka shi Allah Babu ruwansa idan ya jarabta mutum to akwai tanadin dayayiwa wannan bawan idan har yayi tawakkali yacinye wannan jarabawar.

Allah yasa mudace,
Allah Kuma yabaku zaman lafiya yasawa wannan auren albarka.

“Amin” CM ya amsa adduar ta Alhaji babbah Yana cewa”

Allah yaqara girma.

A natse MAJEED shima yayiwa Alhaji babban godia kafin suka fito.

Dayake da lafiyayyar Lexus din CM sukazo Dole shine ya maidasa gida.

Suna Isa gidan Yana ajiyesa harabar gidan yakira matansa yace kowaccensu ta fito su koma gida sbd yasan ba qaramar rigima zaayiba idan zancen auren ya Isa cikin gidan tunda duk matane bare ita kanta Inayah din
Gwara idan zatai Rigimar ya Zama ba kowa a gidan.

MAMUH

LOVE/MARRIAGE/ROMANCE

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button