GURBIN IDOINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 21-30

Tana son faruk kusan ma fiyeda yanda taso Zaid Kuma cire sonsa aranta zaiyi Mata wuya sosai amma Kuma Dole Zata dauki dangana kodan kada acigaba da cin mutuncin Abbinta da maganar yanda ya haifeta,

Itadai koma Yaya mahaifinta ya haifeta tunda Bai yar da itaba kokuma ya gudu yabarta kokuma yamayi denying zamansa mahaifinta to tanason abunta ahakan,

Idanma bada aure ya haifetaba Bata buqatan sani tunda barna ce to Riga ta afku ba gyara acikinta,
Hakama dawo da zancen kokuma tambayarsa akan Gaskiar zancen kaman cin mutuncin mahaifintane zatai bayan Babu ta Inda ya gaza a matsayinsa na uba Wanda ya maye gurbin uwa.

Ko danginsu da kakanninta Bata sake tambayaba sbd tsananin dokar daya kafa Mata akan hakan shiyasa Bata sake shaawa ko marmarin tambayaba.
Abu daya tasani takuma tabbatar shin,
Koma menene ya Raba mahaifinta da mahaifiyarta harma da danginsu ba abune Mai dadiba,tashin hankaline.

****Bayan kwana biyu da fashin auren jama’ar da suka sani sunyita yawo da zancen Wanda har gurin abokan aiki da huldarsa zancen yaje na cewa bada aure ya Haifa yarsaba,

Da yawa basu wani damuba sbd harkace data shafesa bawai aikinsaba
Haka zalika dukiyarsa da matsayinsa ya hana kowama daga zancen saidai mamaki da la shakka mutane sunyita fada.
Inda ma zancen yayi sauki bai wani shiga media ba sbd a Nigeria din ba kowane ya sansaba tunda baa qasar yake zauneba,

Manyan mutane abokanan huldodinsa ne kawai suka Sansa sosai sai jama’ar da baa rasaba.

AA MAJEED mutum ne da Baya damuwa da Al’amarin kowa sai Wanda ya shafesa,
Kuma Sam Baya damuwa da abinda kowa zai fada akansa Dan Bai taba damuwaba sbd yasan iya bayan fage ne bazaa iya zuwa afada a gabansaba sbd iskancinma gurin yinsa ake samu
Ko su Alhaji baba duk wannan abin daya faru basu iya zuwa sun fada a gabansa ba sbd kwarjini da cika idon da Allah yayi Masa akan mutane Dan haka shima baiga amfanin nemansuba ko ji daga garesu tunda sun Kai sakon gurin Aminsa CM Kuma ya isar musu da sakonsu ga AA din,

Sun dauka zaizo ya rokesu akan janye maganar tunda sunsan Babu abinda bazai iyaba akan farin cikin ‘yarsa saigashi sunga sabanin hakan,

Abinda basu saniba da akan wani dalilin ne suka soke auren zai iya nemansu a sulhunta Amma Kuma har abada bazai iya bawa Wanda ya sheganta asalin ‘yarsa aurenta ba Dan hakan take ya toshe duk wata sauran hanyar dazata ma tunatar da Inayah wannan Al’amarin.

Private hospital din da aketa kokarin budewa da sunanta aka sake bada himma sbd ko aikin tafara sosai yanda hankalinta bazai zauna akan damuwar matsalar da aka samuba.

Dole ta sakawa kanta dangana da tawakkali sbd ganin Abbinta daya tattara maganarsu faruk ya watsar duk da tasan abin Yana damunsa tunda shi ubane da aka fasa auren yarsa Rana tsaka saidai Kuma bayyanarda damuwar batada wani amfani shiyasa basa gane Inda yanayinsa yake dosa.

Umma yaganah ma haka suka hakura suka dauki dangana suka cigaba da adduar Allah yakawo Mata wani mijin yasa hakan shine yafi Zama Alkhairi.

Yanzu Bata wani fita asibiti sbd baa kammala tasu asibitin ba gashi Dr Abdul ma Dole yanzu zai dawo yaci gaba da aiki a asibitin tasu idan angama tare.

Da labarin lalacewar auren ya samesa baiji dadiba sosai sbd tunanin halinda Inayah Zata shiga Dan haka Saida ya matse ayyukansa yazo Lagos din hankalinsa ya kwanta.

Da farko Inayah na ganinsa daya iso gidan nasu Batasan lokacinda ta fashe Masa da kuka ba tana sake maimaita Masa abinda yafaru.

Hankalinsa Bai tashi da abinda ya faru dinba kaman yanda hankalinsa yatashi da kukan datakeyi Wanda taketa riqewa da dannewa cikin ranta sbd gudun daga hankalin umma yaganah da Abbinta,

Amma tsakani da Allah har cikin ranta tanajin tsananin quncin rashin faruk Wanda gabaki daya yanzu idanma yakira bayan kuka Babu abinda take Masa harya daina kiranta sbd kukanta ba qaramin daga hankalinsa yakeyiba,

Kukanta zai iya sakasa bijirewa iyayensa ya dauketa suje suyi aurensu wani gurin Amma Kuma hakan ba qaramar fitina zai tadaba dan kuwa Yana shakkar mahaifin Inayah din sosai tako ina.,
Bayason ya jawa iyayensa ‘daurin da zai taba tsufa da mutuncinsu Amma badan hakanba Babu abinda zai hanasa guduwa da Inayah wani gurin a daura musu aure.

Hankalin Dr Abdul ya matuqar dimauta da kukan Inayah wadda yakewa wani irin boyayyan son da yafara fin qarfin qarfinsa,

Shi mutum ne Mai tsananin zurfin ciki da iya danne Abu shiyasa son nata yake boye cikin ciki da zuciyarsa Amma irin son dayakejin yanai Mata a yanzu bazai iya barin wani ya auretaba koda zaaita saka ranar auren nata ana warwarewa har sai ranarda ya sameta.

Ita kanta tanajin Dr Abdul cikin ranta sosai Amma ba amatsayin masoyiba sai matsayin aboki wanda batada tamkarsa bayan Neesah.

A gidan ya qarasa wuninsa Yana rarrashin Inayah shida umma yaganah daketa qara gode Masa kan damuwarsa dayake nunawa sosai akan Inayah din.

Yana gidan Abbi yadawo Dan hakama Dole atare dasu yaci abincin dare dukkaninsu a dining.

Dr Abdulsamad yasamu shiga sosai agurin Abbi Wanda da farko harsu Inayah din sunyi mamaki sosai tunda sunsan shi mutum ne Mai wuyar sabo da mutane,
Bakowa yake yarda yashiga jikinsaba sosai
Amma Dr Abdul lokaci qanqani yashiga ran abbin ya kwanta Masa sbd sanin kansa dakuma qaunar Inayah Mai girman gaske daya hanga atareda Dr Abdul din.

Ya jima Yana fira agurin abbin kusanma duk akan aikin asibitin ne nasu da ake gab da kammalawa,
Sai dare yabar gidan yatafi lokacin INAYAH ta jima da yin bacci sbd yanzu Bata wani jimawa take bacci.

Neesah Takoma Abuja gurin momy datazo ta jajanta musu suka koma tareda Neesah din Abuja.

Ahankali Dr Abdul ya Dage sosai gurin mantar da ita faruk dukda da Kamar wuya
Amma Kuma dagewar tasa da tsananin kulawarsa akanta yafara cin nasarar hakan Dan yanzu ba laifi tacirewa ranta faruk din ta hakura saima hankalinta data maida sosai akan Dr Abdul din kan aikinsu.

Faruk yakoma Malaysia qaro karatu Dan haka yanzu wayar tasu ma kusan kwata kwata sun daina saidai idan sunga juna a social network.

***Lokaci ya ‘dan sake ja son da Dr Abdul ke Mata yafara juyewa zuwa wani Al’amarin daban,
Yanzu gabaki daya ya sauya akanta yakoma kaman ba Natsatsen Dr Abdul din dakowa ya saniba,

Wani irin so Mai zafin gaske yake Mata Wanda harya fara bawa umma yaganah tsoro gashi dai Bai fito yafada Mata Sonta yakeba Amma dai kowa ya kallesa yasan yagama zautiwa a Sonta Dan ko kallonta idan yanayi mantawa yakeyi da kowa.

Ita kanta Inayah lokuta da dama tsananin kulawarsa da abubuwan dayake Mata na kauna tsoro da shakka suke Bata Amma har lokacin batajin tana Masa son soyayya saina aboki,yanzuma ya wuce abokinta ya Zama wani bari na rayuwarta.

Abbinta ma ya lurada halinda Dr Abdul yake ciki akan Inayah,

Baida matsala akan bawa Dr Abdul aurenta Amma Kuma Yana shakkar irin son dayake Mata zai iya cutatar da ita akan kishi kokuma cutatar da duk wanda zai shiga tsakaninsa da ita Dan haka son shima yake sakasa shakku,
Ta wani bangaren Kuma tausayinsa yakeji Mai tsanani sbd son mace irin haka kaman ba so bane ciwo ne.

Anty Hafsat koda aka fasa auren Inayah da Faruk Bai taba alaqarsuba saima sake shaquwa dasukai Dan haka yanzu tazama antyn Inayah tamkar wata qanwar uwa ko qanwar ubanta
Komai na Inayah tasani da ita suke shawara so da dama
Hakama Umma yaganah ta zamar musu tamkar uwa a gurinta suke wasu shawarwarin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button