AMANAR AURE HAUSA NOVEL

AMANAR AURE 85-86

??84 and 85??

Via OHW???? www.gidannovels.blogspot.com

Koda hilal yafito daga asibitin su umma sunbar gurin, motarsa yashiga jinine kaca kaca, amma ahakan yashigeta yanufi gidan umma,

Koda yakarasa gidan yashiga umma da hajna suna zaune a falo, rankowa a bace yashigo falon yayi sallama, umma ta kyalesa hajna ta amsa,
Kujera mai dubin tasu yazauna yana fuskarta su ya saukar da murya yace ” ummana kiyi hkr, nikaina bazan iya zama da ameelah ba amma inasone idan natashi hukuntata akan abinda tamun namata horo mai tsanani, yadanyi jim kafin yacigaba dacewa ” sannan kuma cin fuskar zaiyi yawa ace agaban iyayenta zan saketa, dan Allah umma kiyi hkr”
Yana gama maganar yayi shiru,

Umna tayi shiru nakusan minti biyu kafin tajuyo gurin sa tace “shikenan naji zanbarka kazauna da ameelah amma da sharadi,
Umma tayi shiru tana kallon hilal,

Hilal yace “ummana wanne sharadi”

Umma tacigaba dacewa “sharadi na shine, inaso kakara aure, kuma bakowa nakeson ka auraba face kanwarka HAJNA, daman tun farko ita naso ka aura amma kabijiremun kaje ka aure ameeelah”

hajna datake gefen umma kunya tacikata dasauri tatashi da gudu ta wuce daki,

Hilal yace “umma hajna fa kikace, kifa tuna asanadiyarta na hadu da ameelah, kawarfa ameelah ce”

Umma tace “toh kuma aurenta haramun ne eh, ko shikenam dan tana kawarta babu aure a tsakaninku kenan, to bari kaji wannan umarni nake baka ba shawara ba dan haka tashi katafi kuma auren nan banaso ya wuce nan da sati daya,

Hilal yayi matukar girgiza shifa baitaba jin son hajna zuciyarsa ba, taya zai zauna da ita, amma bai musawa umma ba yatashi yatafi,

Hajna tana komawa dakin tadaka tsalle,
Tadanyi ihu kadan yadda umma bazata jiba, cike da jin dadi take magana tana dariya “Allah na godema daka cikamun burina, ashe mafar kina zai zamo gaske” takara daka tsalle, ta fada kan gado, wakar Adamu hassan nagudu tashiga rai raiwa inda yake cewa “Farin ciki yasameni tunda kace kayarda dani, shaukin bege yakamani acikin mata kanai dani, nazama tauraruwa acikin mata nice adon gari” ta kara tallatsa ihu, akan murna harda su hawaye, tana cikin murna kuma saita tuna da ameelah, ta murtuke fuska sai kuma tayi murmushi tace “kawata ameelah, kishiyata ameelah, hmm yanzu za a fara wasar”…

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button