GURBIN IDO

GURBIN IDO 21

Safiyyatulkiram: 21

  "Kai.....kai,meye hakan?" Anni ta dakatar dasu cikin tsawa,ganin zasu fara sa'insa a tsakaninsu

“Ya zaizo ya samemu zaune,sannan kawai yace sai ta tashi ta shiga daki anni?,wannan wanne irin raini ne?” Khalid ya fada cikin jin ciwon abinda hisham yayi masa,yana jin ya disgashi abinda ba’a taba yi masa ba

“Anni,dawowarta kenan daga makaranta,da alama ko ke bakisan ta dawo ba,don nace ta shiga ta ajjiye qur’aninta sai ya zama laifi?” Shuru ne ya biyo baya,anni tana nazartar kowannensu cikin sakannin da basu wuce biyar ba,sai taji hankalinta ya dan tashi,zata iya cewa bata taba ganin irin wannan sabanin ba a tsakanin jikokinta,wannan shine karon farko da hakan fa faru,duk da tasan dama tsakanin khalid da hisham ba jituwa bace can can,amma kuma basa cecekuce,tabbas ya kamata ta yuwa tufkar hanci da wurwuri

“Wuce ciki maimunatu” anni ta bawa maimunatu dake daskare a wajen umarni,da hanzarinta kuwa qafafunta na rawa tayi ciki,kamar ta tashi sama haka takeji,har ta samu ta isa ga dakinta,ta tura qofar ta shige,ta zame a hankali a qasa ta zauna qafafunta suna rawa saboda tsabar tsoro,me ya kaisu fada a kanta?,shin wai basu duba kamanninsu da darajarsu ba da zasu tsaya suna fada a kanta?,kamar ita maimunatu?,wadda bata da komai?,bata kuma mallaki komai ba?,me yasa?,abinda ta dinga tambayar kanta kenan cikin mamaki da kuma tsoron abinda ya farun yanzu.

   "Ku zauna" anni ta fada musu itama tana lalubar wajen zaman

“Ka zauna mana nace!” Anni ta fadawa khalid tsaye cikin matuqar bacin rai a tsawace.

   Sun kusa minti biyu shuru kowanne anni tana karantar fuskarsa,kafin daga bisani ta kirayi sunan kowa a cikinsu

“Me idanuna suke gani?” Ta jefa musu tambayar da ba wanda ya shirya amsa mata,sai cin d’aci da kowannensu yakeyi

“Tun ina raye hakan zata fara faruwa ina ga ace qasa ta lullube idanuna?……to in sha Allahu wannan abun ba dai cikin ahalina da zuria’ta ba,haihata haihata,bazan lamunta ba kuji da kyau,na meye zaku dinga sa’insa akan maimunatu?,to dukkaninku ku dauketa a matsayin qanwarku,banason kowa ya sanya wani abu a ransa bayan wannan…….kuma inaso a yanzu yanzu ku baiwa junanku haquri”

“In sha Allah” kowa ya fada a cikinsu saidai murya ciki ciki,hisham ne ya fara bawa khalid din haquri,tunda ya girme masa da watanni kusan shida,shima khalid din ya maida masa,sannan khalid din ya miqe hannayensa zube a aljihunsa yana shaidawa anni zai tafi

“Aiba yanzu k saba tafiya ba,ko don na muku fada?” Kai ya girgiza yana duban agogonsa

“A’ah,dama da wuri naso na koma yau din,ina da abinda zanyi” tabe baki anni tayi

“Oho maka…..a sauka lafiya” qaramin murmushi ya sake ya juya yana ficewa daga falon,qasan ransa yana juya maganar anni da tace su dauketa matsayin qanwa kawai,shikam.dai Allah ya sani ya gani yana so,zai kuma yi duk iyakar bakin qoqarinsa,zai kuma fafata da kowa don ganin ya samu maimunatu,bawai ya haqura bane.

    Sun fita sun bar anni ne da dogon nazari da tunani,tana tsoron kada abubuwa suzo su kwabe ba kamar yadda take shiryawa ba,tana hangen al'amura masu nauyi a idanun kowannensu tsakanin hisham din da khalid,wannan tunanin ya sanyata daga waya ta laluba number dr marwan,ta shaida masa idan ya shigo gida da wuri a yau tana son ganinsa,idan kuma bai shigo akan kari ba gobe da sassafe ya nemeta kafin ya fita ya amsa mata da to,saita maida akalar kiran nata zuwa number jabir.

    "Me kuke har yanzu a qasar nan ne jabiru?" Ta tambayeshi kai tsaye ba tare data tsaya bi takan tambayarsa,sumarsa yaci gaba da tsanewa da towel

“For now dai ni na gama duk schedule din da nake nasu a turkey,matsalar tana ga mutuminki,sam bashi da sha’awa ko nufin tahowa” gyara zamanta anni tayi sosai

“Nan da yaushe kake ganin harshi xai iya dawowa gida?”

“Karshen watan nan nan da 2weeks kenan komai nasa zai kammala”

“To ka shaida mana,lalai dakai da shi din ina da buqatar dawowarku qasarku zuwa farkin sabon wata……kai kaga ma,hadani dashi a waya”

“Okay, hold on karki kashe” yayi maganar yana maqale da wayar,gami da ajjiye wandon hannunsa da yake da niyyar sanyawa ya fita a dakin.

   Kofar dakinsa da sassanyar qamshin turarukansa suka kamashi ya tura,luf luf dakin yake,saidai bashi a nan,ya kalli a gogo,lokacin da yake shiga gym ne,tabbas yana can,don haka ya juya da 'yar sassarfa yayi can.

  Sanye yake da farin wando qal me ratsin green daga gefe da gefansa,iyakar wandon wasan gwiwarsa,hakan ya sanya sambala sambalan qafafunsa dake cike da gargasa suka bayyana,sai rigar kayan armless shirt,yana tsaye daga bakin window,hannunsa riqe da qaramin towel yana goge zufar jikinsa,idanunsa kuma na ga waje.

   Duk da yaji sautin bude qofar amma bai juyo ba,haka ya sanya jabir din takowa ya iskeshi a wajen da yake tsayen

“Anni na magana” ya fadi masa a taqaice,kamar bazai motsa ba,sai kuma ya cilla towel din gefe yana juyowa duk da har yanzu idanuwansa naga wajen

“Duk randa mutanen can suka shiga gonata zasu gane shayi ruwa ne” ya fada fuskarsa na nuna alamu na bacin rai,wajen jabir yakai idanunsa,wasu ‘yan asalin turkey dinne,baisan me yasa mutanen suke da jin kansu da alfaharin su turkawa bane,ba yau ba sun saba wulaqanta baqar fata kamar yadda yanzun sukewa wasu,duk da laifinsu ne,yawanci suke zubar da kansu

“Kar ka fara,ka rufa mana asiri,a qasarsu kake fa?”

“And so what” ya fada cikin nuna halin ko inkula,kana ya miqa hannu ya zame wayar daga kunnen jabir ya maidata kunnensa,yana qara taku zuwa gaba gami da gaida anni.

    Waje ya samu ya zauna bayan ya gama jin dukka bayananta,yatsunsa ya nutsa cikin lallausan gashin kansa,baisan me zai gayawa anni ta fahimta ba,kamar yadda ya rasa gane taqamaimen dalilinta na birkice masa,tare da bashi umarnin tahowa gida next month,bayan kuma shi bai shirya hakan ba,banda amna ma,baya tunanin xai koma nan kusa

“Zan duba,zanyi qoqarin zuwa” wannan itace amsar daya bata.

    Sanda anni ta ajjiye wayar saita qwalawa tabawa kira

“Ina maimunatu ne?”

“Tana dakin karatu,kinsan lokacin karatunta ne yanzu,kin santa kuma da himma” murmushi anni tayi,ita kanta tasan yarinyar daban take cikin dukka yara data sani,ba sawa ba fitarwa ba,babu hayaniya hakanan babu hargowa,uwa uba bata dauki rayuwarta da zafi ba,har cikin ranta kullum kwanan duniya tana jin nutsuwa da kuma gamsuwar hadin da take shirin yi da yarinyar

“Kiramin ita tabawa,wannan maganar ce ta taso,inajin lokaci yayi da zata san da zaman maganar,saboda ta sama zuciyarta tun kafin qarasowarsa,bawai sai daga bisani taji maganar sama taka ba,uwa uba ina hango wutar rikici dakeson ruruwa,gwara na yima tufkar hanci” kai tabawa ta gyada

“Gaskiya ne wannan haj anni,ubangiji ya tabbatar mana da alkhairi,yasa komai yazo mana cikin nasara da sa’a,ya kuma sanya qarshen abun ne yazo” cikin jin dadin addu’o’in tabawa anni ta amsa

“Ameen,ameen ya hayyu ya qayyumu tabawa” daga haka tabawan ta juya ta fice.

    Sosai yau din takejin dadin karatun,hakanan Allah ya sallada mata qaunar hadith,dalilin da yasa zaiyi wuya ayi musu qarin hadith bata haddace su ba,kamar yau din,saura guda biyu ta gama haddar qarin da akayi musu jiya juma'a tabawa ta turo qofar tare da sallama ta shigo.

   Qaramin murmushi ya wanzu saman fuska da siraran labban maimunatun,ta rufe hadith din tana duban tabawa

“Yau ban shigo kitchen ba ko?,karatu ne ya tsaidani amma na kusa kammalawa” murmushi itama tabawan ta maida mata,maimunatu nada saurin shiga rai saboda sauqi da dadin mu’amalarta

“A’ah muna,bansan me yasa kike takura kanki ba wajen zuwa kitchen kullum”

“Bana takura baaba tabawa,inajin dadin zuwan sosai,na qaru da kalolin girke girken da bansan ana yinsu ba,ina kan qaruwa ma,hakan yana min dadi”

“Gaskiya ne” tabawa ta amsata tana murmushi,don ita shaida ce,tuquru maimunatun ke maida hankali tana koyar duk wani girki da tazo ta samu zasuyi,daga inda taga anyi sau daya a gabanta to tabbas ta haddaceshi kenan,idan ta maimaita irinsan kuwa zakayi mamakin yadda ya bada ma’ana,kamar wadda ta jima tanayi.

“Yanzun ma anni ce take kiranki”

“Tom,gani nan zuwa” tace da baba tabawan tana qoqarin ajjiye Hadith dinta a take,ta kuma miqe tabi bayan baba tabawa,suna dan zancan islamiyyarsu,har zuwa sanda suka isa qofar dakin annin

“Tana ciki,zan koma kitchen mu qarasa hada abinci,don yau anan Alhj Dr(haka tun da baba tabawa take kiran dr marwan) zaici abincin dare”

“Idan na fito zan sameki a can saimu qarasa in sha Allah” ta fada saboda gwada kyautatawarta akansu itama komai qanqantarsa

“To ba laifi” ta amsa mata tana komawa zuwa hanyar kitchen,ita kuma ta tura dakin anni ta shiga,bakinta dauke da sallama.

    ,kamar ko yaushe,cikin nuna matuqar kulawa ta amsa mata tana gyara zamanta

“Kinga miqon wancar jakar kafin ki zauna” anni tace da ita tana mata nuni da wata jaka dake gefan gadon,miqa matan tayi sannan ta zauna tana fuskantar annin.

  Zuge jakar anni tayi,ta fiddo wani abu,sannan ta daga kai tana duban maimunatu tana sakin qaramin murmushi

“Yau hira zamuyi dake” murmushin nan nata dake nuni da nutsuwarta gami da kamun kai ta sakewa anni

“So nake naji samari nawa kika taba yi maimunatu,sannan a cikinsu wa kikafi so?,inaso kuma naji har yanzu kina sonsa?” Sosai maganar anni tayi mata nauyi fiye da zaton ita annin,taji kamar qasa fa tsage ta shige ciki,ta yaya zata fara irin wannan hirar da anni?,bayan ko dasu laila ba zata iya wannan maganar ba?.

“Uhmmm,ina jinki,ki bude baki ki gayan” sake daureta kunyar annin tayi,sai kawai ta hau kada kai a hankali,dan bata fuska tayi

“Kina nufin ba kowa?” Da sauri ta daga kai alamun eh,sai annin ta motsa tana ajewa maimunatu hoto a gabanta

“To ga jikana,zaki iya aurensa?” Kasa daga kanta tayi bare ta kalli hoton,tanajin kamar ta kulle idonta ta bude taga bata a gaban anni,kayan kunyar yayi yawa

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button