INDO MAKATA COMPLETE NOVEL

INDO MAKATA COMPLETE NOVEL

INDO MAKATA COMPLETE NOVEL

“To Anty risy kinkawo kuka gidan mutuwa dukda dai suran ya shafe mun a ynxu,bitar dandaƙa mukeyi da babana maganar da nike maki muna iza waƙa…amma ki biya kuɗi zan zo har gida jibi a fara karatu”

“Aikuwa dai na gode don kuɗi ba matsala in takama ma abuɗe maki islamiyya ai sai ayi,wallahi indo ke er baiwace bacin haka da tuni an jefeki….”

“A’aaah a’ahhh barni da taɗin islamiyyar nan bar ganin ana cewa ku yarbawa akwai ku da amagu to wallahi kwashafamun lahiya don namana tauri da ɗaci garai kuna matsamun saidai mutum ya baƙunci barzahu don naga idonki na sauya kala…ko daima ke mayyace? To kurwata ƙur don banta6a manta malama ladi daga ta buɗe makarantan addini kuka lasheta saidai ta buɗe ido ta ganta a kabari to wallahi ban iyawa…kuje can ku nema wata malamar amma ba indo ba.”

“To daga abun arziƙi? Indo in baki iyaba ai basai kin mun ƙazafi ba ,don sharian maita wuya garesa ,kuma malama ladi ai ita tajawa kanta da ace ,bata tsokani mayyah tayi mata waazi bada baayi partyn kurwan taba”

“Oho dai nidai nayi maki warning aha”

Tawice fuuuu kamar wacce akayiwa laifi


Ranar laraba

Ƙarfe 11 na safiya agogon Washington tayi ma su kamal da yarorinsa uku a filin jirgin don zuwa abj a nigeria kafin su wuce garinsa zaria.


Tun duku duku na gama kintsa kayana ,kiran sallan farko nakwashi kayata sai tasha,ƙarfe bakwai na safe a babbar tashar warri tayi mun ,nayi jira soaai kafin motarmu tacika kafin muka ɗauki hanyar kaduna wanda zai kaimu har zariya….tafiya fa bana wasa bane gashi an kwararan mun kuɗin mota dubbai nikuma dubu uku gareni.
Saidai na faɗa masu inada ɗan uwane dazai zo ɗaukana a can tashar zariyar damun iso zai biya….

Ko ya zasu kwashe da drivern motar ,saidai mun tara a episode na gaba

Taku har kullum
Oum aphnan
[3/31, 12:14] Bamalli✌️: ????????️????
????????️????

  _*INDO MAƘATA????*_

????????️????
????????️????

Na….Oum Aphnan????
Marubuciyar✍️
Jarababben namiji????

ALHERI WRITERS ASSO.

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 13/14

___Muna tafe yunwa na ƙwarzabata amma naƙi taɓa kuɗin hannuna barema su gani su amsa,saidai innaga en motan nacin breadi ko wani abu in masu zuru da ido,in sun kauda kai in kwasa hamma inyi pillow da ƙunshin kayata na kan cinya in koma barci.

Sai la’asar sakaliya muka iso kaduna,nan ko duk fasinjojin motar suka sassauka ,saura ni da wata dazataje jaji….Gyaran murya mai motar yayi.

“Hajiya zamuyi maku juye kusauka mu saku a wata motar ku bamu kuɗinmu”
Gabana ne ya yanke ya faɗi.zare ido nashigayi ina kallo mutanen da bansaba da ganin irinsu ba ,a tsalelen gari mai kyau da kyawun titina…Liƙis jikina yayi sanyi wannan shine ake cewa ,Kin kawo kanki mahallaka cikin sassanyar murya nasoma magana
“Dan allah an kawo zariyan ne?”
“Wani irin zariya ? A kaduna muke kibiya mu haƙƙinmu

“Tabɗijan lallai borin namijine,to aiko ficika ban maganinsa,don saidai ku juya warri dani”

“Ke karki kawo mana zancen banza , duk inda kuɗi suke dole ki fiddosu ko muyi maki dukan kawo wuƙa,mu ɗaureki mu sakaki a boot mu yasar a dauji” cewar futunannen kondostan da shike basakwacce.

Gabaɗaya dariya ya bani”hhhh kaji wani murya uwa na alade…ƙyalƙyal” na hau dariya harda hawaye da riƙe ciki.

Ɗaga hannu yayizai kwasa mun mari ,da hanzari na tare fuskata da hannuna….,wani tartsatsin sperk ne ya fito daga jikin zobena yayi cikin idanun mutumin.

Fasa ihu yayi yina juyi ,garin na juyawa dashi ɗif ya daina ganin komai

“Wayyo allah wuta…wuta…wuta yina shigamun ido bani ganinku ,ku taimakeni “take wajen yacika damƙam da jama’a ,aikuwa tuni na sulale sa en kayana na yanki hanya.
Saida naci gudu mai isata kafin na tsaida ɗan taxi…Ina numfarfashi nace “Bawan allah zaria zaka kaini”
“To aini ban aikin gari gari” “toh dama zarian ba akaduna yike ba amma driver na ya saukeni a nan yace zai wuce gareji ya gyaro mun motata,allah barshi ni in samu na haya ya biyoni daga baya?”

Wani kallon sheƙeƙe na rainin wayo yayi mun ,kafin ya kware da dariya
“Ciftsi ke yanzu haka wata hajiyace mai mota da ƙullin kaya a hannu?”
Juyar da kai nayi ina hura hanci .

“Lallai yaro bakasan omo yaroba ba,toni da kake ganina nan er sarkice,mu in zamuyi tafiya ɓadda kama mukeyi ,yanda en kidnapping bazasu kamamu ba ko en fashi…amma kakaini zariyan zakaga dangina”

Kallon tsaf ya bini dashi ,kyar idonsa ya sauka akan zobena dayike sheƙi daga gani kaga zunzurutun gold

“Tom inkin yarda dubu ashirin zaki biyani don ke kaɗai zan ɗauka”
“Times 2”
“Me kike nufi?”
“Ina nufin na ninkama biyu ,arba’in kenan ko? Allah ya kaimu lahiya”

Daga nan nashige bayam mota ya ɗauki hanya


Daga airport wani jirgin dazai kaisu zaria suka shiga tin anan arfat ta soma ƙorafi “Wannan wata irin getto countery muke ?”

“Ai bamu zoba love yanzu zamu hau jirgin da zai kaimu can”
Amrah ce ta katsesa da sauri “amma ai mukanje spain….japan..china dasu dubai da momy amma ko zamu hau wani jirgin zakaga airport ɗinsu dakomai fine”
“Shshshhhh????”
Alamar taishiru yayi mata da yatsa
Tuni idonta ya ciko da ƙwalla ,muna masa magana wato muna damunsa ko?

Jan hannun little yayi suka shige jirgin suma suka biyosu a baya.


BIRNIN ZAZZAU
Fadar mai martaba sarki Abdu since 1976.

Abinda aka rubuta kenan agaban rangajejen ginin get ɗin masarautar mai ɗaukeda ƙananun get get kusan biyar tako ina zaka iya shiga fadar mai ɗaukeda titin sama tamkar zakashiga wani gawurtaccen birni a irin manyan ƙasashen duniyan nan ,irim su japan da india.

Fadan kam a yau tagama cika da batsewa da manyan mutane da sarakai da masu gomnati don ɗaiɗaikun shuwagabannin ƙasashene basu samu halarta ba, banda wainda suka turo wakilinsu gadai dukkan alamu tarone ake gudanarwa mai matuƙar muhimmanci

Tsaro kam antanadar dashi don in da hali ƙuda bai iya wucewa sai an lacceshi.

Wannan hoton fadar kenan….amma ta6angaren mutan zazau yau kam jiniya da algaitu har sun gode allah ,Hakan ta kasance da kamal da yaransa ,tun da suka sauka a airport na aviation yaga jirage suna aikin sassauka ana kawo baƙi…ya ciro wayarsa kenan yaga motocin fada jere guda sha biyu farare sol sol sai baƙaƙe biyu a tsakiya ɗirka ɗirkan motoci masu numpashi a gurin numbern ansa prince and princesses
Sauran fararen zungura zunguran lexurios ɗin na excort ne cikin suit da sojoji duk a wajen numbobin numbern ansa emirate palace.

Wani guguwar mulkine yaji yina dawo masa ,cikeda isah yaɗauko shadow glass ɗinsa ya manna a fuska ya riƙo hannun er autarsa Lil. Suna gangarowa daga cikin jirgin

Wani irin jan kafet doguwa aka malala har gabansa yayinda duk excort ɗin suka yi layi gefe da gefe suka ƙaƙame tareda saita bindigoginsu ,takawa sika shigayi shida lil. Agaba amrah da arfat na biye dasu.
Har gaban baƙaƙen motocin ɗaya yashiga shida Aphnan ɗayar amrah da arfat suka shiga ,ji kake ana maida bingigogi ƙuwai kuwait..kafin motocin suka fara fita daga cikin Filin jirgin.

Suna kaiwa bakin fadar ,get ɗin fadar suka shiga zugewa da kansu suna cinna hancin motocin ciki kaf saida aka laccesu kafin nasu yarima abarsu su wuce gaban taron direct su kuma sauran na excort ɗin aka wuce dasu parking lot.

Ya kwashe fiyeda minti 20 kafin ya sako da sawunsa waje lokacin kam tuni ,su amrah sunyi tsaye suna jiran fitowarsa….wajen yayi tsit ana jiran fitowar yarima.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Leave a Reply

Back to top button