NOVELSRAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE

RAHIMA COMPLETE HAUSA NOVELS

                  1

 *Bismillahir Rahmanir Raheem*

Gaba daya yau cikin garin Kano an tashi cikin fatsakin rana ne duk da cewan an shiga watannin da ya kamata a rinka samun ruwan sama ko da yaushe. Al'amarin sai addu'a kenan domin wasu jihohin da kauyaku tuni sun sami ruwan sama, banda wannan ma sau da yawa hadari zai hadu a sararin samaniya tamkar ruwa zai sauko kafin kiftawar ido amma cikin hukuncin Allah sannu a hankali hadarin sai ya washe garin yayi haske , abu gwanin ban tsoro.

A kalla a kan jera kwanaki ana hakan kafin Jalla sarkin sarauta Yai nasa hikimar a saukar da ruwan kamar da bakin kwarya, wani lokacin har a yini a kwana ana shekawa. Idan anyi dace da wannan baiwa, garin ya kanyi sanyi, duk inda mutum ya taka zai ji taushi da kamshin kasa wanda sansanyar iska ke yadawa ko’ina, alamun an samu ni’imar Allah kenan don zafi zai ragu matuka, daga nan kuma sai manoma su dukufa su koma gona, malamai da sauran jama’a kuwa mu ci gaba da adduar samun damina mai albarka don kasarmu ta Kara samun yalwar abinci da kyakkyawar ci gaba, Allah yasa mu dace, ameen.

 Duk da cewan ranar tayi yawa wacce ta haddasa zafin dake bugawa  ta ko'ina bai hana jama'a bayin Allah zirga-zirga da kaiwa da komowar su wajen sana'oinsu ba, matan aure a gidajensu sun dukufa neman na kansu, halayen Kanawan Dabo dake burgeni kenan. Ba dai kaga suna zaman kashe wando ba mazansu da matansu, babba da yaro sun san hanyar da zasu maida taro sisi, sisi ya zama sule, sulen nan ya koma naira ba tareda girman Kai ko kyashin juna ba.

A daya daga cikin wadannan gidajen dake unguwar Yakasai ne Hajiya Kaltume, dattijiya ‘yar kimanin shekaru hamsin da biyar ke zaune cikin dakinta tana ‘yan kulle-kullen kayan sana’arta, kamarsu kuka, kubewa busashahiya, maggi vedan da mai tauraro, tana sayarda omo, gishiri da suga, ga dakakken yaji da take masa hada-haden kayan kamshi, tafarnuwa dasu magi harda soyayyar gyada,kana ta durasu cikin robobi ko kwalabe tana saidawa.

Sha biyu da rabi dai-dai babban danta Dr Haseeb yai sallama ya shigo gidan ya tarad da ita ta baje kayan a gabanta tana ta faman kulli, ganin haka ya kara tamke fuska ya murtuke babu alamun walwala ko kadan. Itama sanin halin likitan yasa ta daure nata fuskar, ko banza Dan fari ne,daman can ba sakin fuskar yake samu ba. Ya gaisheta ta amsa a ciki. Ya gyara zamansa tare da kurawa tafukan hannunsa idanu na ‘yan dakikoki ya saki ajiyar zuciya. An ce tsakanin da da mahaifi sai Allah, ajiyar zuciyar da yayi yasa uwar ta dago Kai ta kallesa tace “Kai lafiya, wani abu na damunka ne?”
Ya kada kau “Komi lafiya ba abinda ke damuna, sakon da kika bari a gida ne yasa na garzayo inji ko lafiya kike son ganina da hanzari?”
Kafin ta bashi amsa Saida ta kulla kullin gishiru uku, hakan ya kara tunzura shi nan take ya kasa daurewa ya bara “Wai Hajiya don Allah me yasa kike son wahalar da kanki ne? Meye naki na zama kina wadannan kulle-kullen?”

Ta kallesa ta kau da kai kana ta amsa ” Tun shigowarka na lura ranka a bace yake, amma so nawa zan fada maka cewan ni rayuwata ta duniya iyayena basu yi min tarbiyyar zaman banza ba tunda kuruciyata, nasan muhimmancin dogaro da Kai ta hanyar neman na kaina, naga Kuma amfanin sana’a tun duniya na kwance kudin nada daraja ba yanzun da muke muna sana’a ba, muna buga-buga.”
03/09/2020, 10:52 – Anty saliha: ….RAHIMA..doc by jami
3

 Karfe biyar na wannan ranar yana kwance cikin dakin barcinsa, tunanin al'amarin 'yanuwansa kaf suka addabesa, ya juya can, ya juya nan....
 Aka bude kofar dakin a hankali, ta shigo da dauke da cup data doro bisa faranti mai dauke da tatacciyar abarba ta tsaya gefensa ta mika masa, bai karba ba Saida ya tashi zaune, maimakon ya sha ya rinka karkada 'yan kololon kankarar da aka jefa cikin juice din don yai sanyi. Kafadarsa ta dafa tace "In tambayi Daktan wani abu?"

Ya dago ya kalleta yana shafar goshinsa da yatsunsa biyu wanda alama ce ta nuni da yana cikin damuwa, ita tasan haka don ba banza kawai take takamar ta fahimci halin wannan murdadden mijin nata da suka kwashe shekaru shidda suna tare ba.
Kafin ta bata amsa Saida ya kurbi juice din ya hadiye sannan Y
Ya dago ya kalleta yace “Meye?”
Ta amsa “Lafiya na ganka cikin wani yanayi tunda ka dawo?”
“Ba wani abu ya bata amsa a taikaice kafin ya ci gaba batun auren Rabi’u ne ya taso, Ina ganin karshen watan nan za a daura auren ayi bukin kowa ya huta.”

Zuwaira ta bugi kirji “Wane Rabi’un, ba dai autan Hjy ba, karatunsa fa?”

“Saurara! Ya fadi ba tareda kallonta ba, Hjy na ganin danta ya girma don haka gara ayi auren, idan da halin ci gaba da school to, but for now ayi auren dai…
Ta so taji karin bayani daga bakin maigidan nata amma tsawon minti goma sha biyar ta fahimci iyakar abinda zata ji kenan daga bakinsa, taja jiki ta fita ta koma kicin.

Karfe shidda kanninsa suka yi sallama gidan babban Yaya, ya fito falonsa suka zauna, Hayatu da Rabi'u suka zamo daga Kan kujeru domin su gaishe shi, ya amsa musu cikin fara'a har suka ji mamaki dalili da a zatonsu bom zai tashi!

Ba bata lokaci ya fara magana “Ba wani abu yasa na nemeku ba sai don inji daga bakinka bayan na Hajiya dangane da batun aurenka.”
Rabi’u ya gyara zama ya fara kare kansa “Wallahi Yaya ban taba tsammanin abu ya zama haka ba, yes nasan mun fara sa mutunta juna tun shigowarta makarantarmu don shekara daya kacal na wuce ta, duk da ba course dinmu guda ba muna fahimtar fannin karatun junanmu da inda muka dosa. Da farko relationship dinmu tamkar yan uwa har a kan kiramu wa da kanwa, cikin ikon Allah myka shaku da juna fuye da zatonku, Kuma wallahi bamu taba furtawa juna batun soyayya ba sai watanni biyu da suka wuce har muke ganin zamu iya zama abokan rayuwa, sai dai ko da muka gasgata muka yanke shawarar bamu kawo batun aure kusa ba don gaskiya na fada mata sai na kare karatu ta amince saboda itama tana shaawar karatun sosai. Ashe muna namu ne Allah na nasa, kwatsam kakanta na wajen uba ya tada kayar baya cewa shi sam bai San da batun wani karatu ba aure ya sani, Kuma dole Rahima ta fidda miji ko yayi mata na dole. Ta taho ta zayyane min batun cikin tashin hankali da rashin sanin madafa, na tausaya mata kwarai, sannan naga ga alkawarin auren juna da muka shine naga ya dace dole inyi wanu abu a kai in taimaka ayi aurenmu in yaso ma ci gaba da karatun later.”
Hayatu ya daka masa harara “Kaji dan ka iya, watau ma har ka riga ka tsara yadda za’ayi, in hakane meye na neman shawarar ko yardarmu, ba ka shirya ba? Yaro da shegen rigiman tsiya, muna zamanmu lafiya ka tayar Mana zaune tsaye.”

Rabi’u ya gyada Kai “Kunji Yaya Hayatu da kayi naka wa ya hanaka ko shawara wa ka dauka, gashi nan saboda zara ka kasa zama da mace guda sai biyu duk sun hana maka sakat “

Haseeb yai gyaran murya “Ni ban kiraku gardama ba, shawara na taraku muyi, Kai Hayatu hakuri za muyi ayi abinda ya dace, Hjy ma na goyin bayansa. Amma Kai Rabi’u Ina son kasan cewan wallahi ba da son raina za ayi auren nan ba, na amince ne gudun bacin ran mahaifiyarmu Kuma bamu san alkhairin dake ciki ba so karka damu ba zaka ji kunya ba in Allah yaso. Yanzun su waye ne iyayenta, wace unguwa take?”
Baki yaki rufuwa saboda murna, Hayatu ya kallesa ya bushe da dariya yace “Ka daina wani murna in har munji bata da usuli batun aure ya tashi ehe, uhhmmm Kai muke saurare:
03/09/2020, 10:52 – Anty saliha: …RAHIMA..doc by Jami
2
Dr Haseeb yai murmushi bayan jin kalaman tsohuwarsa yace “Tuni na amince da batunki Hajiya shiyasa na sayo miki wadannan kayan masarufin yadda kika bukata bisa yarjejeniyar aunarwa za ki rinka yi ba ki zauna kina irin wahalar nan ba.”
Itama tayi ‘yar dariya ” Ina wahala a nan? Ku fa likitoci kuka ce mutum ya rinka motsa jininsa, Kuma idan kace sai tiya ko mudu zan rinka sayarwa kenan sana’ar tawa bata talaka ba ce, in kuwa hakane to ci gabanmu ragagge ne domin talaka shine jigon kowacce irin sana’a, ni don Allah ka bar wannan zancen, Kai kenan kullum kazo gidannan da sabon tsirkun da zaka kirkiro alhali ni din nan ban gaza ba da sauran karfina, to Wai ma Ina wahalar take? Mai aiki fa ka ajiye min musamman babu abinda ni keyi kullum sai dai in wanke goma in tsoma biyar, inci mai kyau, insha mai kyau, in daura zanin da wata yarinyar macen bata daura na, inyi barci na ya isheni, in bautawa Ubangijina gwargwadon karfina, bani da sauran buri a duniya da ya wuce illa inga auren Dan autana, baya ga shi sai rokon cikawa da imani. Haba wace wahala, lokacin da akayi ta can da anyi yanzun kuwa albrkacinku sai godiyar Allah da fatar Allah ya baku masu yi muku fiye da yadda kuke yi mana.”
Ya amsa “Ameen Hajiya, shikenan ba zan kara magana kan hidimar sana’arki ba Allah ya bada sa’a, amma don Allah ki rinka samun isashshen hutu, bayan haka nace ki tambayeni duk abinda kike so cikin ikon Allah ba zai gagara ba.”

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button