INTEESAR 2

duk abinda xa ayi min a min, amma sae
nahallaka ta. Hajiya tayi ajiyar xuciya
tace”shknan son, na baka go ahead kayi
mata duk abinda yaxo knka.” ya juya ya fice
ba tare da ya sake cewa komai ba, yana
tunanin irin abinda xae yi mata idan ya
kamata, sadeeq kuma har gidan ubansa xae
je ya samesa.
.
. Yau tun da gari ya waye intisaar batafita
ba, duk ta rasa abinda ke mata ddi a gidan
ga yawan faduwar gaba da take yi duk ta
rasa sukuni, ko islamiyya ma taki xuwa da
yake ranar lahadice, tun bayan abinda tayi
ma ya Aliyu jiya da daddare ta kasa samun
nutsuwa har ynxu, tayi da ta sanin abinda
tayi masa yafi a kirga, tasan baxa ta ji da ddi
ba idan tashiga hannunsa,to ma wae me ya
kai ta, kai xuciya ma dae ba a iya masa, jiya
ce rana ta farko da tayi ma ya Aliyu hk,
momy tai tayi da ita ta gyamata me ke
damunta taki fadi, sae dae tace ita bbu
abinda ke damunta, ta mike daga kwance
da take tana kallon agogo karfe goma da
minti goma na safe, hijab din ta ta dauka ta
leka bedroom tace ma momy ta tafi wajen
inna, momy ta dan ji ddin hka don ta rasa
kan ‘yar tata, tace “to ki gaida min ita,” tace
“to” sannan ta fice gabanta na mugun
faduwa, gudu-gudu sauri-sauri take tafiyar,
gidan tsit don duk ‘yan matan gidan sun tafi
islamiyya, sllma tayi kofar falon abba
jikintana rawa, abba ya amsa ta shiga ta
nemi gefe ta xauna tana gaida abban, abba
ya amsa da fara’arsa yace ta tashi ta xauna
kan kujera,takoma kan kujerar, abba yace
“me ya hanaki xuwa makarntar yau?” ta
kirkiro murmushi ta lafta masa karya,
“wanki nayi abba,” yace “to yyi kyau” bbu
matsala ko? Ta dan fara kame-kame,
tace”aa…dama…abba..” wayr abba tayi ring
ya dauko yana duba mae kiran nasa, ya
daga.Shiru intisaar tayi ta jingina kanta jikin
kujerar tana tunanin me xata ce da abba,
sllmr da taji da muryar mae sllamar yasa
xuciyarta ya kusa shigewa cikinta don tsoro,
da kyar ta iya amsa masa tayi saurindauke
kanta, Aliyu ya shigo palon sanye da bakar
jallabiya, kallo daya yyi mata ya dauke kansa
ya nemi gefe ya xauna ya tsura ma A.cn
dake ta aiki a falon ido, ta mike jiki a sabule
xata bar falon don har ynxu abba waya
yake, abba yyi mata alama da hannu ta
koma ta xauna, ta koma cikin rashin kuxari
ta xauna tana wasa da long fingers dinta, ta
saci kallon Aliyun taga kallonta yake yi, da
sauri ta dauke kanta xuciyarta na bugawa,
abba yagama wayan ya juya yana kalln
Aliyun yace “sae ynxu garin ka ya waye knan
malam,” ya shafa kansa ya danyi murmushi
yace “kayi hkuri abba, yau na tashi da ciwon
kai ne,” abba baice masa komai ba illa Allah
ya sauwake, yace”ameen” sannan yace “ina
kwana abba,” lfya lau, ka tashi lfya?” abba ya
amsa yana kallon intisaar da har ynxu kanta
a sunkuye yake, kun gaisa da yayannaki ne?
Ta dago kai da sauri tace “ina kwana yaya?”
Aliyun yace “lfya lau, da kina jiran na gaida
ke ne halan” ya fadiyana kirkiran murmushi
ganin yanda abban nasa ya kafa masa ido,
ita din ma murmushin ta kirkiro tace cikin
muryar da ba tata ba”kayihkuri na sha’afa
ne” abba ya dubi intisaar din yace “yauwa
ina jinki fatima,” ta gwalo dara-daran idonta
ta rasa me ma xata ce da abban, sae kawae
ta samu kanta da cewa “aa dama abba
gidan momy nke sonnaje ne yau,” abba yace
“wace momyn knan?” da sauri tace
“momynsu maryam” yace “ohhk gidan
nafisa xaki” tace “uhm,” abba yace yaushe
xaki dawo idan kinje? Da yamma xan dawo
abba, ta fadi da sauri tana kallonsa, duk da
tasan idan taje ba lallai bne ta dawo kuma,
kila can xae fiye mata xaman lfya. “wa xae
kai ki knan?” tayishiru sannan tace “xan hau
tricycle abba” abba yace “aa Aliyu dae ya kai
ki, tunda yana gida.
Intisaar ta dago kaida sauri tana kallon
Aliyu, taga yyi wani murmushi irin
tamugunta, ta girgixa kai gabanta na
faduwacikin tausasa murya tace “abba ya
haisam yace xae kai ni kuma..,” Aliyu ya
kalleta yana murmushi yyi saurin cewa “ni
cinyekixanyi a hanya knan?” ita din ma
kirkiran murmushin tayi tace “aa ba hka
bne, kaga na riga da na fara gya masa, da
bn gaya masa bne sae ka kaini,” to ai ni da
haisam daya ne, meye a ciki idan ni na kai ki
din? Ya tambayeta yana kallon tsakiyar
idonta, Ta xaro ido xuciyarta na bugawa
tace”gskya ne,” abba yace “toma wae a ina
kika ga haisam din?” ta fara kame-kame
tama rasa abinda xata ce masa, abba
yace”tun asuba ya shigo yace min xae tafi
jigawa, ko ya fasa ne?” ta dan sata kallon
Aliyun da ya kafa mata ido yana murmushin
da ta san na mugunta ne, ta rumtse idonta
cike da tsoro tace “na manta ne, hka ne
abba,” Aliyu yyi ‘yar dariya yace “to yanxu
kin yrda na kai ki?,” tace “uhm” yace “aa kiyi
magana mana, ta mike tana cewa “bari naje
na shirya,” abba ya kirata ya dauko dubu
biyar ya bata, yace”ki gaida min dasu
shaheed,” ta durkusa har kasa tayi masa
gdya sannan ta fice da sauri kafarta na
hardewa, abba yyi murmushi, yana jin ddin
alakar ‘ya yan nasa, don a nasa tunanin,
Aliyun son intisaar din yake, ganin actions
dinsa. Intisaar na fita da gudu tayi sashinsu
don tana tsoron kar ya biyota, momy ta
kalleta tace “har kin dawo?” tace “uhm,
momy manta da innar nan, gyangyadi take
ta minna gudo,” bedroom ta shige da sauri
ta fada kan gado, ae xuwa gidan anty nafisa
kam ya sha ruwa ysu don ko hauka take ita
kam baxata bi Aliyu ba. Aliyu kam yana barin
falon abba ya shige bedrom dinsa cike da
jin ddi ya shirya, irin abinda xae mata ya
dinga kitsimawa a ransa, rannasa na dada
baci, ya gama shirinsa tsaf ya fito,hajiya na
tambayrsa inda xa shi amma baetanka mata
ba, kujera ya ja a tsakar gidan ya xauna
jiranta, amma har kusan karfe sha daya da
rabi bata fito ba, ya gaji da jiragashi bbu
kowa a gidan bare ya aika kiranta, shi kam
yau idan bae ma yarinyar nan abinda ke
cikin ransa ba ciwon xuciya xae iya kamasa,
yyi huci me xafi ya mike tsaye yana waige-
waige, kasa daure wa yyi yaje sashin nasu,
yana isa ya bude kofar falon momy na
xaune tana duba wani littafi, intisaar ma
lkcn ta fito falon tana kwance tana kallon
Mbc2, ya kalli intisaar din ya dake yace “kin
shanya ni ina ta jiranki?” ta mike tana
kallonsa tace”tafiyar nan fa ina ga na fasa
kayi wuce war ka kawae,” ta juya ta shige
bedroom xuciyarta na bugawa, don taga
kkrinta na fada masa hkn, tsaye yyi bakin
kofar kmr ruwa ya cinyeshi, ya juya ya bar
wajen xuciyarsa na harbawa, lallai yarinyar
nan tadauko hnyr raina shi ne kuma xae yi
maganinta, ransa a bace ya bar gidan
yanatunanin me xae ma intisaar yaji ddi
idan ta shiga hannunsa?” kiranta momy tayi
bayan ya fice fuskarta daure tace “meya
hada ki dashi, kuma ina xakuda?” nan ta
koro ma momy yanda sukayi momyn ta
hade rae tace “karki kuskura, ko da wasa
kuma.” yau kusan sati biyu knan suna wasar
‘yar buya da Aliyu duk inda tasan xasu hadu
bata xuwa, bangaren inna ma ba kasafai