INTEESAR 2

hnkli irin na wnn rana ba, momy tayi
lallashin har ta gaji ta kyaleta ganin kamar
kara tunxurata take, ita gani take kmr momy
ba sonta take ba tunda har taki cewa
komae a falon, Zainab da maryam ma sun
gaji da lallashin sun kyaleta, hka ma Anty
Nafisa da ta hau ta da fada ganin lallashin
nata da ake kmr xuga ta ake tayi ta kuka,ita
kam ta rasa abinda ke mata ddi a duniya.
Karfe tara da minti biyar na dare Haisam ya
shigo falon nasu, momy na xaune ita da
ihsaan suna cin abinci, ita ko tana kasan
tiles a xaune ta kife kanta da kujera tun safe
take a hkn, sllh kadae ke mikar da ita kuma
da tayi xata dawo ta xauna taci gaba da
aikin kukanta, dama tuni momy ta fita
harkarta, don abincin ranar da ta xubo mata
ma kin ci tayi, hkn ma yasa bata xubo mata
na daren ba tunda abun nata kmr iskanci
- Haisam ya gaida momy taamsa da
fara’arta ta bar masu falon, ya dawo gaban
intisaar ya durkusa yana kallonta kmr shima
ya taya ta kukan, wani sabon kukan ta fashe
da tana kallonsa gwaninban tausayi, ya
xauna gaban nata hade da dago kanta cike
da damuwa yace “haba intisaar, so kike ki
janyo ma kanki wani ciwon ko,” xubewa
jikinsa tayi cikin kuka tace “ka taimakeni ya
Haisam, ka ba ma Abba hkuri wllh bna son
ya Aliyu, kasheni xae yi idan…..” ya rufe mata
baki hade da rungumota yace “ya isa hka
kanwata, bbu abinda ya isa ya maki wanda
Allah bai maki ba,” a hankli ta fara kkrin
hadiyekukan nata sae ajiyar xuciya da take
yi, har lkcin yana rungume da ita, murya can
kasa tace “ya Haisam,” shima murya can
kasa yace “kanwata” ta girgixa kai a hnkli
tace”da ma kai ne” ya dagota yana kallonta
yace “ni ne me?” wasu sababbin hawaye
suka gangaro bisa kuncinta, ta maida kanta
ga kafadarsa cikin rawar murya tace “dama
kai ne Abba ya bani,
Bayan sati biyu da faruwar lamarin, tana
xaune ita dazainab da kursum a tsakar gida,
su suna cin gyada suna hirar irin abubuwan
da xasuyi a bikin fadila da ya rage saura sati
biyu don abba ya maido dashi kusa a dalilin
fitsarar da taje tayi ma inna wae sae tace
ma abba ya janyemaganar aurenta da mai
‘ya ya har uku tunda ita ce ta xugasa ya
hadasu dama, kowa dai yasan umma ce ta
sa taxuwa tayi ma innar hka, inna ko ta
kwashe abinda ya faru da wanda ma bai
faru ba duk ta tsara mar abba tana
matsarkwalla, har da ce masa da bulalarta
taxo wae xata mata duka, kuma daga Aisha
har shafa bbu wanda ya hanata suna
kallonta, abba yasa Haisam ya xane ta snn ya
maida bikin kusa. intisaar tayi xurfi cikin
tunanin da tke yi, xainab ta kwashi bawon
gyadar da suka gama ci ta watsa mata su,
ba shirita dawo daga duniyar tunanin da ta
shiga, ta hade rae tace “meye hka xainab,”
xainabta dawo gefenta taxauna tana
kallonta tace “haba intisaar ke baki da aiki
ynxusae tunane tunane, dubi fa yanda duk
kika bi kika lalace,” intisaar tayi narai-narai
da ido kmr xata yi kuka amma ta kasa cewa
komai, xainab tace “ynxu tsakaninki da Allah
meye matsalarki ki gya min,” nan da nan ta
fara hawaye tana kallon Zainab din tace “ya
faruuq,” xainab tayi tsaki tace “yyi pick din
cal din naki ne,” ta girgixa mata kai a
hnklitace “A’a, he ix nt still respondn,”
xainab ta tabe baki “to tunda ke kuma
shashasha ce ‘yar wahala ae sae ki ta
kiransa, nan a gabanki ya haisam yyi ta
kiransa ranar kinga ya daga, mutumin da
har office ma ya bi sa, sae dae ace masa
baya nn, alhalin kuma yana nn din,
kwanakin baya kusan kullum sae inna ta
kirasa kinga yana daga wayar, mutumin
daya gujeki lokaci daya idan ba ma wauta
ba meye na damuwa dashi,” cikin kuka
intisaar tace “haba xainab ba dole ya guje ni
ba, ai tunani xae yi na yaudaresa ne, kuma
ko…” xainab ta buga tsaki tace”gskya ne, sae
ki tayi ai,” snn ta bar ta wajen tayi gaba,
kursum ma ta mike tace”duk kin bi kin daga
ma mutane hankali akan wanda bai ma
damu da ke ba, idan har sonki yake da
gskya, ai baxae guje ki lkci daya ba, kuma
idan shi dan mutunci ne bai ci ace ya ma ya
Haisam abinda yyi masa ba” ita ma tana kai
wa nn tayi gaba, ta kife kanta kan
gwiwowinta, kuka take kamar ranta xae
fita, ita kam ta ga rayuwa, ynxu bbu wanda
xae fahimce abinda take ji a ranta, momy
damatuni ta dawo daga rakiyarta, ga wani
irin sabon tsana da hajiya ke mata a gidan
don ji take kmr ta kasheta ta huta, hkn yasa
bata da ikon ko lekowa compound, ynxu ma
bata gidan shine dalilin fitowar ta tsakar
gidan dasu xainab. Budewar gate din da taji
ne yasa tadago kanta a tsorace don tayi
tunanin su hajiya ne suka dawo, wani irin
muguwar faduwar gaba yaxo mata ta dalilin
hada idoda suka yii da ya Aliyu, tuni jikinta
ya fara bari tayi saurin mikewa tsaye, tana
kakkabe jikinta duk na karfin hali. Sae da
taga ya wuce ta snn murya na rawa tace”ina
yini,” shima don gudun kar yace bata
gaishesa bane, ta ga ya juyo yana
dawowata inda take kuma, salati ta shiga yi
a xuciyarta gabanta na ci gaba da bugu, shi
knn ta ja ma kanta, da ta sani da bata
gaishesa ba ma, gab da ita ya tsaya yana
kallonta, ta kasa dago kai ta kallesa don
tsoro,”kika ce me?” ya tambayeta cikin daga
murya, ta fara kame-kame. “aa.. Dama ni em
gaisheka nayi dama,” ya fixgota hade da
dago kanta yana kallonta, ta tsura masa ido
ganin yanda ya rame sae idanuwa, lips din
nn nasa yyi wani irin pink sae sheki suke.
Wasu sababbin hawaye sukagangaro bisa
kuncin ta.
.
Abba na barin wajen, Aliyu ya fito yyi hanyar
gate yana hararan inna da har ynxu ke tsaye
tsakar gidan tana kuka, inna ta bisa da
gudu ta datse gate din tana cewa gidan
uban wa xaka? Sae kuma ta shiga kwada
ma Abba kira”Bukar maxa ka fito gashi nn
xae gudu wllh,” Abun dariya abun takaici, su
fadila da kursum dake leke ta taga suka
dinga dariya har da faduwa, nn da nn Aliyu
ya saita murya ya marairaice mata yana
rokan ta ta bude gate ya fita ynxu xae
dawo, inna taki sae faman kwala ma Abba
kira take tana cewa xae gudu, Haisam ya
fito yyi bangarensu intisaar, ba a dau lkci ba
suka fito tare da momy suka shigafalon
Abba, duk wnn abun da ake akan idonsu
hajiya dake leke ta taga ne, wayar Aliyun yyi
ring ya duba ya ga Abba ne, ya maida aljihu,
yace “don Allah inna ki bani waje na wuce,
kati xan je siya,” inna ta galla masa harara
tace “ae wllh bbu inda xaka sae bukar ya ci
min ubanka yau,” dariya ta kubce masa, ya
ko dinga yi har da buga kafa, karar da
wayarsa ta sake yi ne yasa yyi saurin juyawa
yyi bangaren innar, inna tace “gidan uban
wa xaka, kar ka kuskura ka dosa falona,” ko
kallonta bai yi ba yyi saurin shan kwana, sae
ga Abba ya fito fuskar nn tasa bbu alamar
wasa xae yi bangarensu Aliyun inna tace
“yyi bangarena maxa ka bisa” bai kara bin
ta kanta ba yyi sashin nata, Aliyu kam bae
tsaya sashin inna ba don yasan biyosa abba
xae yi, yyi nisa da bangaren inna ya tsaya
kare ma fence din gidan kallo duk electric
wire ne, baxae yiwu ya dira ba, yayi jim kmr
mai naxarin yanda xae yi sae kuma ya xaga
kawae har bangarensu intisaar, ta gama
dauraye kwanukan da suka ci abinci knn a
bakin famfo ta juya xata shiga falonsu ta