INTEESAR 2

gansa, ta tsorata ainun, ta yo waje da ido
cikin tashin hnkli,shiknn ta shiga uku gashi
Abba ya kira momy ta tafi, ita kadae ce
wajen don ko ihsaan ma na bacci a sashin
inna, ihu ta bude baki xata kwada jikinta na
bari yyi saurin fixgota hade da rufe mata
baki ta fado kansa ya ja ta suka shige falon
nasu ya kullo kofar.
.
69….. Suna shiga falon ya turata yyi xamansa
kan kujera, sai kuma ya mike ya bude fridge
ya dauko ruwan gora ya dawo ya xauna
yana sha, ita ko jingina tayi jikin bango
xuciyarta na harbawa tana kallonsa,ya
xabga mata harara”da’alla get out malama
ki bar kallona idan ba hka ba na fasa maki
ido,” da sauri ta dauke kanta tayihanyar
bedroom, ya daka mata tsawa,”cum back
hia dabba gidan uban wa xaki, ba aiki kike
ba” ta tsorata da yanda yake mata maganar
ta dawo da sauri kuma ta bude kofar falon
ta fita ta dauki broom ta fara sharan dole, to
me ya kawo sasashinsu, Abba ta hango
yana tahowa inna na biye da shi a baya
“Bukar wllh yana cikin gidan nn baxae yu
ace ya fita badon na datse gate din, bari dae
mu duba ko nn ya yo,” itakadae ke xubar ta
don Abba ba sauraranta yake ba ma,
intisaar taajiye broom din hannunta ta
shige falonsu da sauri ganin basu ganta ba,
kwance ta gansa kan kujera yana kallon
tashar Mbc2,shi ynxu ko shakkar momy ta
xo ma ta sameshi bayan abinda yyi mata
yau baya yi, ya galla mata harara yace “ke
fice ki banwaje kar na taka ki a nn, kar ki
sake shigowa falon nn sae na fita,” ta
girgixa kaitace”A’a Abba ne naga yana
xuwa nn…..” ya mike xaune da sauri yace
“nan yake xuwa?” ta gyada masa kai, yyi
shiru sai kuma ya tabe baki yace “Allah ya
kawosa lfy, get out ke kuma,” ta juya xata
bar falon sae kuma ta sake waigowa tace
“har da inna fa,” ya xaro ido yace “wat?
inna” kawae sae ya mike yyi bayan kofa da
sauri jin muryar innar, don yasan inna
akwae xugi, xatai ta xuga abba ne shi kuma
ya dauka yai ta xauna wa a ka, yasan hkn
kuma baxae sa yaji da ddi wajen abban
nasa ba in dae hajiya inna na gun. “ae yau
kam mai raba mu dashi sae Allah ko Bukar?”
Abba dae bai ce komai ba ya budekofar
falon suka shiga, intisaar dama tuni tayi
hanyar bedroom tun kan su shigo, inna ta
kwado mata kira ta fito da sauri tace “abba
sannu da xuwa,” inna tace”Aliyu ya yo nan
hka?” intisaar ta girgixa kaida sauri tace “aa
ban gansa ba,” inna kamrtayi kuka ta dage
ita fa Aliyu na cikin gidannn bai fita ba, Abba
ya sake dialin nmbrsa xae kira, intisaar
dama na ganin yana danna waya tasan
kiransa xae yi, duk ta rikice ta fara kame-
kame”aa,.. Ab.. Abba aibai taho nan ba, emm
kila de yana falon Hajiya ne, amma baya nn
wajajen,” kmr ance ta juya taga wayoyinsa
har uku kan kujerar da ya xauna, ta xaro ido
a tsorace ga abba ya dage sai neman kiran
wayar tasa yake, cikin dubara tayi ta wajen
kujerar da wayoyin nasa suke ta xare
dankwalin kanta ta jefa kan wayoyin, sae
kuma ta xube kan kujerar da karfi, gaba
daya suka juya suna kallonta har suna hada
baki “lafiya, me ya faru?” ta dafe kanta
murya can kasa tace ” kai na ke mani ciwo,
jiri nake gani,” Abba yace”subhanallahi, tun
yaushe,” ta sake marairaicewa tace “tun
daxu,” inna tace”bari ina da maganin ibba ki
sha nasan shi ne,” Abba ya bata dubu biyuta
siyo magungunan da take sha ya juya ya
fice, inna ta bi sa a baya tana cewa “wae to
yanxu ina Aliyu ya shiga jama’ah, Allah yasa
dae ba tserewa yyi ba,” suna fita tayi ajiyar
xuciya ta mike tsaye ta dauki dan kwalinta
ta daura tayi hanyar kofar da saurixata rufe,
ta kusan cin karo da momy, ta xaro ido cikin
tashin hankali tace “mo momy kin dawo,”
Kallon mamaki Aliyu ya tsaya yi ma Haisam,
“ka mareni?” Haisam ya matso gabansa
yana kallonsa da kyauyace “an mareka din,”
inna tuni ta ja intisaar suka shige daki da
sauri suna rusan kuka, cikin sanyin murya
Aliyu yace masa “xaka gane kuranka,” snn
ya fice daga falon, hajiya da umma na labe
bakin kofa tun bayan ihun inna na farko da
ya fargar dasu suna lekan duk abinda ke
faruwa, Haisam na fitowa umma ta bi sa da
masifa kmr ta rufe sa da duka, “wawa
kawae ko ina ruwanka oho,” ko kallonta
baiyi ba yyi gaba abinsa. Karfe shidda na
yamma abba ya dawo gida bayan inna tasa
su fadila su kira mata shi ya maxa ya dawo
gida ynxun nn, abba ya dafe kansa bayan
yagama sauraren surutan inna, gashi sai
wani irin ihu take masu a falon , dama da
belt din ta shigo falon dan abba ya gani da
kyau, “kalle jikina” ta fadi tana nuna ma
abba hannayenta da kafafuwanta, sai kuma
ta sake fashewa da kuka har da kwantawa
inda take tana cewa “wllh yau idan baka
dau mataki kan wnn shegen hatsabibin
yaro naka ba bar min gidan nn xakuyi daga
kai har shi ba mae kwana gidan nn” su
xainab sae boye fuska suke suna dariya,
intisaar kanta ma dariyar take yi, su hajiya
sai faman tabe baki suke suna hararta,
momy kam kallon tv kawae take yi a falon,
Haisam kuwa na gefen abbansa a xaune,
Abba ya jinjina kai cike da takaici ya sake
kiran Aliyun da ya kira yafisau goma sae dae
yace masa yana xuwa, har ya gama ringin
dis tym around ma bai daga ba, abba ya
sauke ajiyar xuciya yana kallon innar da ta
hade rai, ita kawae jira take taga hukuncin
da xai dauka kan dan nasa, ya dubi haisam
yace “je ka kace masa ko na xo na samesa
ne,” haisam ya mike knn xae fita sae ga
Aliyun ya shigo da sllmarsa wanda idan ba
kunne kasa ba ma baxa ka ji ba, ya nemi
gefen khadija ya xauna, yana kallon
abbansa fuska a daureyace “gani nn abba,”
inna tace “to uban waye bai ganka ba,
mugu kawae munafuki algungumi,
shaidanin mutum kawae, ma dae kam Allah
ya isa bamu yafe mka ba” sae kuma ta fashe
da kuka ta kwanta kan intisaar tana rerawa,
har Haisam sae da ya dan dara a falon, su
fadila ma sae yi suke yi, intisaar kadae ce ta
hade rai kanta sunkuye, Aliyu yyi ma innar
wani irin kallon bnxa ya tabe baki ya maida
hnklinsa wajen TV, Abba yyi nisa yana
kallonsa rai a bace yace “me intisaar tayi
mka ka doketa da belt daxu?” inna ta mike
da sauri tana xaro ido tace “kaji wani
shirme irin na Bukar, intisaar kadae? Ae ca
xakayi me intisaar da inna suka yi maka
xaka xanesu da belet daxu, kai jama’ah ni
saenaga ma kamr tsoron dan iskan dan nan
naka kke yi wllh, idan ba hka ba kai ba ka
tashi ka rama min Bukar, dukanmufa ya
dinga yi yana kwallo damu kamr wasu ‘yan
cikinsa, yana xaginmu wae yau sae ya
hallaka mu, da kyar Haisam ya kwacemu a
hannunsa, duba jikina duk shatan belet ne,
hka ma na yarinyar nn” ta gama magana
tana huci, abba yyi murmushi yana gyada
kai yace, “to miko min belt din baaba,” ta
mika masa da sauri har tana tuntube, ya
mike tsaye ya mika mata belt din kuma yace
“gashi nn baaba ki rama bugun da yyi maki,
snn ki mika ma fateemah ma ta rama
wanda yyi mata,” abba ya koma ya xauna,
inna tuni hakoranta suko yo waje, intisaar
ta rike hannunta murya can kasa tace “inna
kawae ki kyalesa don Allah, ki daina biye