INTEESAR 2

daga motar ya shiga gidan yyi bangaren
inna ba tare da ya kalli kowa ba duk da
tsokanarsa da aka dinga yi, bbu kowa falon
inna duk ta koresu ta kunna TV tana kallo
fuskar nn tata a tsuke, da yake sun san halin
innar kuma da sha’anin tsufa bbu wanda ya
kawo komae a ransa sae dariya ma da suka
dinga yi suka bar mata falonta, basu san
inna da gske take ba, bakin kofa Aliyu yaci
karo da Haisam ya fito daga falon ransa
abace, Aliyu ya tambayesa me ya faru, yyi
tsaki yace ka shiga ka gani, snn yyi gaba,
.
ya shiga falon yana kare ma ko ina kallo,
inna na ganinsa ta dada tsuke fuska tana
xare masa ido tace”inji dae da takardar
jikata ka shigo” yyi mata wani irin kallo na
rashin fahimta, da kmr xae yi magana sae
kuma ya fasa yyi hanyar bedroom dinta, ta
bi sa da gudu ta shige gabansa tana huci
tace “wllh wllh ka ba jikata takardarta kar na
tara maka jama’ar kano yau gaba daya,Abin
ma dariya ya ba Aliyu, ya tsaya kallon innar
yana gyada kai, yace “kan wani dalili xan
bata takardar,” inna ta gyara tsayuwa tace
“sbda saura kiris ta amaye hanjin cikinta
yau” dariya Aliyu ya dinga yi har da buga
kafa yana kallon innar, inna ta bude baki
tana binsa da kallo daga sama xuwa kasa a
fusace tace, “ka maida uwarka Aisha
mahaukaciya ba ni ba,” nan da nn ya hade
rai yace”kika ce me?” tace “abinda
kunnenka ya jiye mka,” bae sake ce mata
komae ba ya bi ta gefenta xae shiga dakin
ta tare hanyar da sauri tana huci, “nace
takardarta kawae xaka bata,” wani irin
tsawa da ya raxanata ya daka mata, “da’alla
ki fice ki ban waje hajiya, naki bada
takardar,” inna ta fasa ihu mai kara tana
kiran jama’ah su xo su taimaketa duniya
taxo karshe Aliyu ya bangajeta gefe, abun
dariya abun takaici, Anty nafisa dama tuni ta
yafa gyalentata bar gidan, momy kuwa can
uwar dakanta ta shige, su hajiya da umma
kmr suce wayyo Allah don ddi, ga gida cike
dam da mutane
.
Hka inna ta dinga gabxawa da Aliyu kan sae
ya ba intisaar takardarta kuma taki barinsa
ya fita, dariya kam wasu har da hawaye,
intisaar dae duk wnn abun da ake bata sani
ba, bacci mai nauyi yyi gaba da ita. Aliyu
kam ya kasa ce da inna komai sbda
mutanen da ke wajen sae binta yake da ido
tana ta xuba masa rashin mutunci, can dae
ganin abun nata gaba yake ba baya ba yace
“ke wllh baki da maraba da tsofaffin
yarbawan lagos, dama can cikinsu kika je
kika xauna da yafi maki alkhairi, haba
mutum bashi da aiki sae masifa da fadan
rashin gskya, wnn wllh duk halin tsofaffin
yarbawa ne,” nn fa Aliyuya sama ma kansa
lfya, don xube wa inna tayi gun ta dinga
rusa ihu wae jikanta ya hadata da kafurai
yace mata tsohuwar bayerabiya, hehehe
gidan Bukar dae ya tashi daga gidan biki ya
koma gidan comedy, hmm bari kawae mu
tsallake nn wajajen sisters. Karfe takwas aka
gama walimar da Anty Nafisa da kawayenta
suka shirya don kmr yanda Aliyu yace baya
son ko wani irin party, Abba bae bari anyi
komai ba duk da Anty Nafisa ta so ko dinner
ne ayi, ynxu kam intisaar ta daina kukan da
take yi sae dae ta xama kmr wata gunki ga
muguwar ramar da tayi duk tayi wani irin
sanyi tun bayan nasihar da Alhaji mukhtar
yyi mata daxu da wani abokin abba, karfe
tara aka fara shirye shiryenwucewa da
amarya don abba yace ranar xa a kaita, inna
ta shigo dakin rike da kofi tana wangale
baki tace “maxa ki shanye wnn jikalleta,
shine na karshe,” sae ka rantse kace ba
innar daxu bace.Anty Nafisa ta dago intisaar
tana kallonta tana murmushi bayan matar
da ta kawo musamman dongyaranta ta
gama tsantsara mata kwalliya na fitan
hankali bayan ta gama mata gyaran karshe,
lace ne mai laushi da shegen kyau, shi ba
milk colour ba, kuma ba light brown ba, da
ratsin orange colour a jiki sae daukar ido
yake, fuskar nn tata tasha cool make up, ga
design din lallenta da yyi ma fara fatar ta
kyau sae sheki yake, Anty nafisa ta dago
fuskartatana kallon idonta, ta girgixa mata
kai hade da bata rai ganin hawaye makale a
idonta suna neman xubowa, ta dauki
hankerchief ta goge mata hawayen, snn ta
dauki babban mayafinta fari ta yafa mata a
ka,
.
ta dauko mata takalminta shi ma farin ta
saka, snn ta ja ta tayi bangaren Abba da ita
yan rakiyarsu na biye dasu a baya, Nasihar
karshe abba xae mata, fuskarta a rufe yake
Anty Nafisa tayimata jagora har cikin falon
Abba, ta xaunar da ita har lkcn fuskarta a
rufe yake tana hawaye duk da Nafisa bata
san kuka ma take ba, kamshin turaren Aliyu
ta dinga ji a gefenta hkn yasa gabanta ya
shiga faduwa, ta juya da kyar ta kalli gefenta
taga Aliyu xaune shima kansa a kasa, yana
sanye da shadda ruwan kasa yyi masa kyau
sosai, cikin dubara ta dan matsa ganin kusa
kusa suke,”fateemah” taji abba ya kirata
cikin nutsuwa, ta amsa da dashashiyar
murya tace “Na’am Abba,” abba yyi
murmushi yace “kin san abinda nake so
dake,” ta girgixa kanta ba tare da ta dago
ba, nn daeabba ya dinga mata nasiha tun
tana daure wa har ta kasa ta fashe da kuka
sosai, hkn yasa Abba ya kyaleta ya juyo kan
Aliyu, shi ma dae har Abba ya gama bae
dago kai ba, sae maganar abba ta
karshegareshi ne yasa sa dago kai yana
kallon abban,”kuma Ali idan ka cutar min da
fateemah bana tunanin xan iya yafe mka,”
Aliyu yyi wani kasaitattcen murmushi tare
da maida kansa kasa, Abba ya sa masu
albarka snn yace su tashi suje Allah ya basu
xaman lfya, intisaar na gaba yana binta a
baya mutanen da suka rakota falon suka
rufa masu baya, anty nafisa kuwa ta tsaya
don tana son magana da yayan nata kafin ta
fita, sae ga inna ta shigo tana murmushi
tace “Bukar Bukar, wae da ca nayi don Allah
ko xan iya binsu na koma can da xama, don
gskya gidan nn naka duk ya fitar min a rae
barin da xasu barni ni kadae, dama ga
matanka ba gani na da gashi suke ba gaba
dayansu, can ko kaga muna tare gaba daya
snn suna gani na da mutunci, idan ya so
duk bayan wata biyu sae na dinga kawo
maka xiyara nn ko ya ku ka gani…..” abba ya
juya cike da takaici yana kallon Nafisa da ta
kauda kanta, ya mike tsaye rae bace yace
“ae saeki bi su to” snn ya shige bedroom
dinsa, Nafisa ta mike ba tare da ta kalli
uwartata dake nn tsaye kmr gunki baki
bude ba ta fice. Momy ta kasa ce da intisaar
dake durkushe gabanta tana jiran tata
wordof advice din kan xamantakewar aure
komai, Nafisa dake kan su a tsaye tace “kiyi
magana mana maman ihsaan lkci fa na
wuce wa,” momy tayi murmushi tace “Allah
ya basu xaman lfya, kuma ya albarkaci
aurensu, shi knn abinda xan iya cewa knn,”
anty Nafisa tayi murmushi ta dago intisaar
dindake kuka sosae tace “mamanki ta maki
addu’a fateemah, kice ameen,”
.
intisaar ta xube jikin uwartata tana kuka
sosai tace “momy ni bna son nabarki baxan
iya ba, don Allah kice su bar ni, bana son
naje ko ina,” da kyar Anty nafisa da kawar
momy suka fitar da ita daga falon don
haukace masu tayi, momy duk iya dauriyarta
sae da ta xubdama ‘yar tata hawaye don taji
tausayinta sosae, kuma sae gashi Allah bae
sa tayi dacen miji ba, da har su Anty nafisa
xasu kai ta wajen inna tayi mata tata
nasihar aka ce masu ae fa inna na can tana
ta rusa ihu, ba shiri suka saka intisaar a