INTEESAR 2

ta firfito da ido tace “ni?” ya daka mata
tsawa yana cewa “yhu re vry stupid,
tambayata kike yi ko waye?” a tsorace tace
“Allah ni bngne abinda kke nufi ba….” ya
gallamata wani mugun harara yace”fito min
da dubu biyar dina” ta xaro ido tace “lah ni
na mnta wllh kayi hkuri” sannan ta mike da
sauri ta shiga ciki, sae gata ta fito dasu, ta
mika masa ya fixge ya kirga sannan yyi
gaba. Xainab tace “an shiga uku,” momy dae
bata ko kallesu ba ta dauki doyarta tayi
hanyar kicin, intisaar tace “uhmm ni har na
manta ma wllh” xainab tace “amma yaya
Aliyu bai yi ba a lyf wllh, Allah ma yaso baki
taba kudin ba” intisaar tayi dariya tace “me
xae kaini dama, ni wllh har ma na mnta da
kudin, tun fa ran sunday gashi yautuesday”
xainab ta tabe baki tace”Allah ya kyauta toh”
yauwa na mnta ban gya maki ba jiya faruuq
ya bni dubu biyu wllh, intisaar tace “Allah
sarki, ihsaan ma ya bata” ni kuma dubu
goma ya bni har ynxu ma yana wajen inna,
xainab tace “bawan ALLAH, shine ake
neman a maki tijara kan dubu biyar ynxu,”
suka kwashe da dariya gaba dayansu. Suna
sashin inna gaba dayansu yau amma bnda
khadija da rahma, intisaar na tsife ma
kursum gashi,xainab na kwance suna kallo
sukaji hayaniya a tsakar gidan, da sauri
suka fiffito har da inna dake binsu a baya
da gudu, fadila suka ga ya Aliyu ke duka da
belt yana ball da ita, ita kuwa bakinta bai
mutu ba yana dukanta tana xaginsa, hajiya
da umma na ta masa ihun ya rabu da ita,
inna ta karaso da gudu tana yarfe hannu
tace “an shiga uku, wae kai Aliyu wani irin
shaidani ne, ynxu me tayi mka kke neman
kasheta?” cikin xafin nama Aliyu ya kaita
kasa ya dinga xuba mata belt din tana ihu,
“ae wllh sae ta gya min gidan uban da take
xuwa yau, idan ba hka ba na rantse sae na
sumar da ita,” “ayyo ynxu naji bayani, ae
fadila ana kiran sllhn farko take barin gidan
nan ba ita xata shigo gidan nan ba sae
karfe sha dayan dare,” inna ta fadi tana
kallon su hajiya da kamar su shake ta, hva,
nan inna ta dinga xuga Aliyu ya dinga
dukanta kmr xae kasheta, ita kuwa bakin ta
yaki mutuwa sae xaginsa take tana ihu, inna
ta dauko wani katako da gudu ta kawo
masa tana cewa “muka mata wannan Aliyu,
wa yasani ma ko karuwanci take fita yi,
tsinannun iyayenta sun xuba mata ido,”
haisam ya shigo gidan, inna ta tsiri yi masa
bayani shima yasa kafa ya kwasheta ta xube
kasa hka suka dinga dukanta inna na xuga
su, kmr xasu kasheta, umma da hajiya ba
baki tunda inna na wjen sae matsar kwalla
suke, intisaar da su xainab duk jikinsu yyi
sanyi ganin yanda akayi ma fadila, xainab
tace “ae gwara suyi mata hka kila ta nutsu
wllh”
.
Momynta tashiga kwada ma kira tana bata
hkurin ta bude mata kofar tana kuka,ta juya
taga ya kusa iso inda take, tasa tafin
hannunta ta rufe fuskartata dinga ihu tana
bubbuga kafa tana cewa”wayyo kayi hkuri
ya Aliyu wllh tllh ni ina xuwa makaranta naje
kitso ne yau shi yasabnje ba yau, don Allah
ka rufa min asiri kar ka dokeni, ina
rokanka,” kuka take yi sosae hannunta a
fuskarta tana tsalle-tsalle sae kace ihsaan.
Shiru bata ji an kamata ana duka ba, ganin
shirun yyi yawa ne yasa ta xamehannunta a
hnkli daga fuskarta jikinta na rawa, wayam
taga wajen ba kowa, ta fara waige-waige
tana gwalo ido amma bata ga kowa ba a
gun, a hnkli ta dinga kuka tana kallon kofar
palon nasu, takai hannu ta bude, taji shi a
rufe gam, jikinta a sanyaye tayi bangaren
inna tana goge hawayen fuskarta, xaune
taga Aliyun kan dakali kusa da wani flower
yana ta tuntsira dariya kmr mahaukaci,
haisam dake kan kujera yyi tagumi yana ta
kallonsa, gabanta yyi mugun faduwa xata
juya ta koma da sauri, haisam yace”intisaar
wa ya saki kuka?” tsit Aliyu yyi ya sha mur
kmr bashi ke dariya ba ynxu, ta girgixa kai
tace”ba kowa,” sannan ta maxata bar
wajen. Xainab na xaune a palonsu intisaar
suna kallo intisaar na kwance, wayan
xainab yyi kara, ta daga,masifar da take tayi
ne yasa intisaar ta mike xaune tana ta
kallonta har ta gama ta kashe wayan,
intisaar ta tambayeta wanene,
cikinfushitace “wannan gantalallen da na ke
gya maki ne, tun ranar yake sintirin xuwa
gidan nan, nace ya rabu dani bana yi yaki
saurarana, wannan wani irin jaraba ce?”
intisaar ta tabe baki tace “ae duk hka suke
kmr mayu,” sannan ta mike ta dauke cup
din da kanwarta tasha corn-flakes ta fita
dashi tana taya xainab mita. Tana fita tayi
hanyar gate, ta ko gansa a tsaye tayi
masaiso har wajen inna, tayi sallama inna ta
amsa daga can kuryar daki, ta shiga tana
cewa “inna bako kikayi,” inna tace “hva don
Allah, daga ina? Gani nan xuwa” intisaar na
‘yar dariya tace “saurayin xainab ne,” inna ta
sake kabbara daga cikin dakin tana cewa
“gani nan xuwa, ya shigo don Allah,”
intisaar na dariya ta juya xata fita tayi masa
iso xuwa palon, suka hada iso da Aliyu dake
gefen kujera a xaune yana danna laptop,
wani mugun faduwar gaba ya xo mata, ita
bata ma gansa ba, wani irin kallo yyi mata
yana girgixa kafa, ya hade girar sama da ta
kasa,jikinta a sanyaye tace ma bakon ya
shigo, ya shigo yana gdya, ya mikawa Aliyu
hannu suka gaisa Aliyun ya dan saki
fuska,inna ta fito ta dinga wangale baki
tana masa sannu daxuwa, kusan duka
lemukanfridge dinta ta dire masa a gabansa
sannan ta xubo masa cin-cin da alkaki, tana
cewa “ci ka koshi yaro nan ma gidanku ne,
ae xainab jikata ce, ni na haifi ubanta, kmr
an baka ita an gama kaji ko,” gdya ya dinga
yi shima yana murmushi, intisaar kuwa
dama tuni ta nemi lungu ta xauna tana
satan kallon Aliyun da shi din ma satar
kallon nata yake, suna hada ido ya galla
mata harara, ta mike jiki a sanyayexata bar
palon, inna dake ta faman xuba da
Abdurrahman, tace “aa ina xaki,” takirkiro
murmushi tace “xainab din xan kira, inna
tace “yauwa maxa kije ki kira min ita yar
kwal uba, ashe dama tana da santalellan
yaro kyakkyawa hka taki gya min, maxa kira
min ita,” ta fice da sauri tana yake, Aliyu ya
mike inna tace “ina xaka malam bayan kaga
munyi bako,” ya kirkiro murmushi yana
kallon Abdul din yace “ina xuwa ynxun nan
ae xan dawo,” sannan ya juya da saurinsa
ya fice, shit, ya fadi da karfi ganin har tayi
kwana, bae san ta fisa wayo ba, dama tasan
sae ya biyo ta don hka da gudun ta tayi
sashinsu, tana shiga palon nasu, xainab tace
“ina kika je ina kiranki tun daxu kixo ki ga
abu,” intisaar ta tabe baki tace “kicin na tafi,
inna tana kiranki fa.” xainab ta kalleta tace
“a ina kikaga inna?” tsakar gida tana neman
ki, intisaar ta fadi ba tare da ta kalle xainab
din ba, xainab ta mike tayi sashin innar,
intisaar ta dinga dariya bayan ta wuce, ita
ma ta rama abinda xainab din ta mata ranar
da faruuq ya fara xuwa gidan. A hanya taga
ya Aliyu ya watsa mata harara ta kauda kai
tare da xumburo baki tayi gaba da sauri, yyi
kwafa tare dacewa “xakuci ubanku gaba
daya ae, ke mai saurayin da me kawo shi
cikin gidan dukxan kama ku, yara basu kai
ko ina ba amma sun san su ajiye samari,”