INTEESAR 2

albarka snn yace su tashi suje Allah ya basu
xaman lfya, intisaar na gaba yana binta a
baya mutanen da suka rakota falon suka
rufa masu baya, anty nafisa kuwa ta tsaya
don tana son magana da yayan nata kafin ta
fita, sae ga inna ta shigo tana murmushi
tace “Bukar Bukar, wae da ca nayi don Allah
ko xan iya binsu na koma can da xama, don
gskya gidan nn naka duk ya fitar min a rae
barin da xasu barni ni kadae, dama ga
matanka ba gani na da gashi suke ba gaba
dayansu, can ko kaga muna tare gaba daya
snn suna gani na da mutunci, idan ya so
duk bayan wata biyu sae na dinga kawo
maka xiyara nn ko ya ku ka gani…..” abba ya
juya cike da takaici yana kallon Nafisa da ta
kauda kanta, ya mike tsaye rae bace yace
“ae saeki bi su to” snn ya shige bedroom
dinsa, Nafisa ta mike ba tare da ta kalli
uwartata dake nn tsaye kmr gunki baki
bude ba ta fice. Momy ta kasa ce da intisaar
dake durkushe gabanta tana jiran tata
wordof advice din kan xamantakewar aure
komai, Nafisa dake kan su a tsaye tace “kiyi
magana mana maman ihsaan lkci fa na
wuce wa,” momy tayi murmushi tace “Allah
ya basu xaman lfya, kuma ya albarkaci
aurensu, shi knn abinda xan iya cewa knn,”
anty Nafisa tayi murmushi ta dago intisaar
dindake kuka sosae tace “mamanki ta maki
addu’a fateemah, kice ameen,”
.
intisaar ta xube jikin uwartata tana kuka
sosai tace “momy ni bna son nabarki baxan
iya ba, don Allah kice su bar ni, bana son
naje ko ina,” da kyar Anty nafisa da kawar
momy suka fitar da ita daga falon don
haukace masu tayi, momy duk iya dauriyarta
sae da ta xubdama ‘yar tata hawaye don taji
tausayinta sosae, kuma sae gashi Allah bae
sa tayi dacen miji ba, da har su Anty nafisa
xasu kai ta wajen inna tayi mata tata
nasihar aka ce masu ae fa inna na can tana
ta rusa ihu, ba shiri suka saka intisaar a
motar ita da kawayen nata, wato su zainab,
Anty nafisa ma ta shiga motar suka kama
hanyar gidan Aliyu dake can Hotoro, su
Hajiya da umma dama tun da rana suka
kulle kofofinsu kmr bbu kowa a ciki, don
cikin lodin jama’ar da suka xo bikin bbu
dangin hajiya ko daya bare kawayenta hka
ma umma.karfe goma da kusan rabi motar
da ta taho dasu tayi parkin cikin gidan Aliyu
bayan mai gadi yabude gate din, abokinsa
ne Mujaheed yyi drivin din, gida ne babba
mai kyan gaske ya kawatu da shuke shuke
ta ko ina masu daukar hankali, ginin tsarin
duplex ne, dakuna uku da bathrooms a ciki
each, sae babban falo da bathroom da toilet
a ciki daga downstairs don sae ka hau
stairs xaka tafi dakunan,kitchen din babba
ne sosai sai kuma store dake cikin kitchen
din, stairs uku xae yi lead dinka xuwa
dinning din da aka xagaye da labule snn
akwae kawatattcen garden dake ta bayan
gidan, Anty nafisa ta fito da intisaar daga
motar fuskarta a lullube suka hau stairs na
balconyn, Anty Nafisa ta fadi mata adduar
da xata karanta a kunne kafin ta shiga
gidan kuma ta tabbatar da kafar damanta ta
shiga gidan, sun tar da mutane da dama
cikin gidanmasu jiran kawo amarya, har
bedroom Anty nafisa da yan rakiyar suka yi
ma intisaar jagaro suna guda, ita dae
intisaar ji take kamr ba ita ba binsu kawae
take kmr wata gunki, Aminiyar inna ta
xaunar da ita gefen gadon tana ce ma
mutanen da suka shigo suka cika dakin su
fita su bata waje xatama intisaar magana,
duk sae da ta koresu dakin ya rage daga ita
sae Anty nafisa da xainab, maganganun da
intisaar bata yi xato ba masu nauyita dinga
gaya mata ga anty Nafisa tsaye, xainab
dama tsum tsum tayi ta fice daga dakin, ita
dae fuskarta a rufe yake, daga karshe ta
dada mata nasiha sosai, Anty nafisa na
tayata, kuka sosae intisaar ke yi tana
tausayin rayuwarta don tana da tabbacin
kila farin cikinta ya gama karewa a duniya,
.
karfe sha daya bakin suka watse gida ya
rage daga Anty nafisa sae xainab don har ta
kawayen amarya ma sun tafi, su ma suna ta
shirin wucewa ne, dama Anty nafisa ta ajiye
mata kayan baccin da xa ta saka snn ta
nuna mata turarrukan da xata shafa kafin ta
kwanta, ta tambayeta tana jin yunwa ne,
tace A’a, ta fita kitchen ta hada mata wani
tsumi ta bata ta shanye gabanta, lkcin da
xasu tafi kuwa intisaar rungume anty nafisa
tayi tana kuka sosai wae kar su tafi su barta
don Allah tsoro take ji, sae da xainab tayi
kuka don tausayin intisaar don gigicemasu
tayi, da kyar Anty Nafisa ta lallabata bayan
tayi assure dinta cewar yanxu su Aliyu xasu
shigo don ta kirasa yace suna hanya da
frndx dinsa kuma gobe in’sha Allah xata xo
da safe snn ta samu suka bar gidan don
mijinta na busstop yana jiranta, gidan ya
rage daga intisaar sae halinta, kuka take
sosae kamr ranta xae fita, ta kasa xaune ta
kasa tsaye don tashin hankali, yau ga ta ga
babban makiyinta xasu kwana gida daya,
duk tabi ta takure kanta waje daya tana
rawan sanyi tsoro. Karfe kusan sha biyu taji
shigowar motar Aliyu, xumbur tamike a
tsorace ta daura hannu a ka tace “nashiga
uku ni fateemah,” ta koma ta gefen
madubinta ta tsaya jikinta na bari tana
hawaye sosae, tana ji ya shigo gidan ya rufe
kofofin, tun kan ma ya hayo sama ta dinga
jin kamshin turarensa da ya shiga tada mata
xuciyarta don tsabar tsoro. A hankali taji
yana taka matakalan benen yana hayowa
sama, xuciyarta ya tsananta buga wa, ta
rumtse ido cike da tashin hankali tana yarfe
hannu hade da shesshekar kuka, can kuma
sae taji tsit kmr ba mutum a wajen, ta bude
idonta a hankli tanakallon kofar dakin a
tsorace, taji an bude kofa, saurakiris ta saki
ihu jikinta ya dau rawa, kafanta suka kasa
daukarta ta durkushe wajen tana maida
numfashi kmr warce tayi gudu, a hankali taji
an rufekofar da aka bude.
ba dakinta ya shigo ba ta fadi a xuciyarta
tana kkrin maida hawayen dake neman
saukowa a idonta, ta xaune kan tiles din
dake shimfide a dakin ta jingina jikin
gadonta kanta a kangadon, kmr xata fara
sabon kuka kuka, to ta tabbatar baxae
shigo din ba, tayi jigum ta xuba ma kofar
ido tana tunanin irin abinda Aliyu xae mata
indae har ya shigo dakin nn, kila ma jefar da
ita xae yi ta tagan dakin gaba daya, tunda
wanda ya iya bude mota ya wurgota waje
ae komai ma xae iya yi. A hankali intisaar ta
bude idonta jin haske da ya addabi fuskarta,
ta fara waige waige a tsorace tana kallon
inda take, har lkcn tana jingine jikin gadon
nea xaune, sun ray ne ya shigo dakin ya
sauka kan fuskarta, ta mike da sauri tana
kallon agogon dake manne a dakinta taga
karfe bakwae, ta xaro ido hade da dafe kirji
don ko sllh bata yi ba,ita bata ma san
yaushe baccin ya dauketa da har gari ya
waye ba, budewar gate din da taji ne ya sa
ta xuwa kusa da window ta bude curtain
dinta a hnkli tana lekan ma xa ayi, Aliyu ta
gani cikin motarsa yana gaisawada mai
gadi snn ya ja motar ya fice daga gidan mai
gadi ya kulle gate, intisaar ta sauke ajiyar
xuciya ta jingina jikin wall din dakinta tana
tausayin kanta, ganin hkn ba shine gabanta
ba yasa ta shige bayi tawanke bakinta tayi
alwala ta fito, tana idar da sllh tashiga gyara
bedroom dinta ta tabbatar komai yyi mata
yanda take so ta feshe dakin da turaren da
anty nafisa ta nuna mata xata dinga sawa a
daki ta hada da room freshner snn ta shiga
wanka tana gama wankan ta wanke
bathroom dinta tsaf ta feshe ko ina da
freshner snn ta fito dakin, tana cikin fito da