INTEESAR 2

kayan da xata saka taji an bude kofar, ta
juyaa tsorace tare da sakin abinda ke
hannunta a gigiceta fasa wani raxanannen
ihu tace “wayyoo Abbana nashiga uku,”
Zainab ta tsaya baki bude da mamaki tana
kallon intisaar, a hankali intisaar ta sulale
kasa ta xauna tare da dafe kirjinta da ya
kasa daina bugu da sauri,ta galla ma zainab
din harara duk da taji dadin ganinta tace ”
dubeta don Allah, baki iya sallama bne
malama xaki tsorata mutane,” zainab tayi
dariya tace “xa ma ki fadi gskya ne, wae ta
tsamman angonta ne, shine xata wani
wayance ma mutane” intisaar ta galla mata
harara da wasa tace” angon bnxa, meye
hadina dashi, ” zainab ta tabe baki tace ”
kya ji dashi dae,” snn ta karasa cikin dakin
ta ajiye basket din dake hannunta da leda ta
shiga fiffito da kulolin dake cikin basket din
da flask,intisaar ta xauna gaban madubinta
tana shafa mai zainab ta dago tana kallonta
tace “kin tashi lfya amaryarmu,” tayi kmr
bata ji ta ba, zainab tayi dariyar tsokana tace
“kice sae ynxu ma xakiyi sllhn, ina yayana,
nasan kin sa shi makara yau da gani,”
intisaar dae bata kara kallon inda zainab
take ba ta gama shafa mai ta shiga sa
kayanta wani material mai kyau orange n
milk colour,
.
Zainab ta sauka kicin ta dauko plates da
cups ta dawo dakin tana kallon intisaar
dake gyara fuskarta gaban madubi tace ”
wae yaya fa?” intisaar ta baxa mata hannu
alamar ita ma bata sani ba, xainab tace
“joke apart intisaar da gske baya nn,”
intisaar tace ” Allah ni ban gansa ba ma tun
jiya, daxu dae naji fitar motarsa” zainab ta
tabe baki tace “to Allah ya kyauta, kice jiya
ma baki ci ‘yar kazar nn da madara ba”
intisaar ta sauko kasa ta xauna kusa da
xainab kmr xata yi kuka tace “inna fa?”
xainab tayi dariya tace “ke dae bari, ai yau
karfe 5 duk muka tashi a gidan nn wae xa
tayi maku waina kuma a murhu xatayi, snn
xata dama kunun gyada ta dafa muku
ruwan lipton hadadde, ae mun aikatu yau,
har da su farfesun kaxa da kayan ciki, duk
ga su nn” intisaar tayi dariya sosai tace
“Allah sarki innata, amma de ba yanxu xaki
tafi ba ko xainab?” xainab ta galla mata
harara tace “to uban me xan maki, ni de
daukokuloli ki juye abincin nn don dasu xan
wuce gida , kuma islamiyya xan wuce,”
intisaar ta kamo hannunxainab din hawaye
ya cika idonta tace “Zainab ni kadae ce a nn
tsoro nke ji wllh,” zainab tayi dariya tace
“xaki saba ne ai, kuma naga ai yaya na
dawowa da yamma,” intisaar ta goge
hawayen idonta tace ” aa ni dae ki bari
anjima ki tafi don Allah,” xainab tace to naji
je ki dauko abu na juye maki abubuwan nn,
intisaar tace “ni ban san ina ne kitchen din
ba ai,” xainab tayi dariya tace “yaya bai xaga
dake gidan ba knn,” intisaar ta harareta
tace”wnn yayan naki mutum ne,” xainab ta
dinga dariya ta ja ta suka sauka falo suka
xaga ko ina na gidan, intisaar dae bbu
abinda ya burgeta game da gidan hasali ma
ita tsanar gidan tayi, dakinsa kadae taki
shiga duk da irin tilasta mata da xainab ta
dinga yi tace baxata shiga ba, xainab din
dae ta shiga ta fito.sae kusan karfe goma
suka karya da xainab, ta dinga ji kmr xainab
ta dawo gidan da xama kwata kwata. Karfe
sha daya xainab ta tattara ina ta ina taxata
tafi gida intisaar ta dinga kuka wae don
Allah kar ta tafi, xainab tayi ta kwantar mata
da hankali tare da assure dinta ae xata
kawo mata abinci da yamma.
.
Da yammar kuwa Zainab ta kawo mata
tuwan shinkafa da cous-cous sae dan
fankasau da miya kusan kala uku, sae
farfesun naman rago, intisaar tace ” xainab
na safen da kika kawo fa na nn har ynxu, ya
xanyi da wa innan kuma” xainab ta harareta
tace “to shi kuma yayan fa, ai ba ke daya
inna ke yi ma ba, ke dashi ne,” intisaar ta
tabe baki tace “to ai sae ki jira randa ya
dawo sae ki kai masa,” xainab ta girgixa kai
tace “intisaar knn, baki san ke mace bace
kece xaki jawo hankalin mijin ki gare ki, duk
wani tsoro da fargaba ki ajiye sa gefe ki
daure…..” intisaar ta dakatar da ita a fusace
“kinga idan baxa ki min maganar arxiki ba
kiyi shiru, ni fa ban dauke ya Aliyu matsayin
mijina ba fa, yanda aka tilasta masa aurena
nima tilasta min akayi, wllhwllh bana sonsa,”
xainab ta mike tace “to ai yyi kyausae kuyi ta
xaune a hkan, kinga tafiya ta sae da safe.”
intisaar bata ce mata komai ba duk da bata
ji ddin tafiyartata ba har ta fita daga dakin,
karfe goma tana kwance kan gadonta rike
da littafin hisnul muslim tana dubawa taji
shigowar motar Aliyu, gabanta ya fadi ta
mike xaune ta kashe wutandakin gaba
daya, ta takure gefe daya xuciyarta na
mugun bugu, har taji ya hayo sama ya bude
dakinsaya shiga ya rufe. Ta sauke ajiyar
xuciya ta koma kangadon tayi kwanciyarta
ta lullube da blanket. Washegari tana kan
darduma tana tilawa bayan ta idar da slln
asuba taji fitan Aliyu da motarsa daga gidan,
a xuciyarta tace ae indae irin xaman da
xasuyi knn baxae dinga cin ubanta ba
Alhamdulillah.Yau kwanan intisaar hudu a
gidan Aliyu, amma ko sau daya basu taba
haduwa dashi ba, in ya fita tun bakwae na
safe baya sake waiwayo gidan sae
karfegoma wani lkcn ma har sha daya na
dare, ko kadan hkn bae taba damunta ba
don ita gaba ma ya kai ta, ita kam bata taba
tunanin Aliyu xae bar ta ta kai har wnn lkcn
a gidansa ba tare da ya cuceta ba, sae daefa
bai san cin ta da shan ta ba. Yanxu kam ta
fara kwantar da hankalinta a gidan ta fara
sabawa da xaman kadaici, dama yana fita
xata fito ta gyara ko ina na gidan ta share ta
goge snn tayi moppin, ta fito da kwanukan
da taci abinci a daki ta wanke a kitchen ta
gyara kitchin din ta tsaftace ko ina, ta kanyi
mamakin inda Aliyu ke cin abinci safe da
ranadon tasan shi ba gwanin cin abinci a
waje bane da daddare kuma yafi shan tea
ko coffee, indae ta shigo kitchen da safe ta
kan ga mug din da yasha coffee da daddare
sae ta wanke ta maida inda yake.
Duk safe da yamma inna na ba xainab
abinci ta kawo mata wani lkcin zainab ta
dan tsaya taya ta hira wani lkcin kuma tace
sauri take duk da tafi tsayawa ma da
yamma, don da safe tana xuwa islamiyya,
intisaar ta sa zainab ta kawo mata novels na
turanci dayawa don ita bata fiye karanta
littafin Hausa ba kuma kallo ishenta yake
don wani lkcin sae ta yini bata kunna tvn
dakinta ba, karatun da take yi yana matukar
taimakonta don yana debe mata kewa
sosai, wani lkcin idan ta gaji da karatun ta
kan tafi garden tayi xamanta tana kallon
tsuntsaye, yau ma kmr kullum intisaar na
falo tana goge gogenta da ta saba, wajen
karfe karfe sha daya na safe ne don Zainab
duk ta bata mata lkci ta cika ta da surutu da
ta kawo mata abinci da safe bata barta tayi
aikinta ba don bata fi minti goma da barin
gidan ba intisaar ta fara gyare gyaren gidan
har lkcin kuma kayan barci ne jikinta,
muryar Aliyu taji bakin kofa yana waya duk
da bae shigo falon ba amma ya bude kofar,
gabanta yyi mugun faduwa ta mike a
tsorace tayi bayan kujera da gudu ta
durkushe a wajen tana xare ido, taji ya
karaso cikin falon tare da rufe kofar, bata
kara jin takunsa ba ko ina yyi tsit, ta rasa