INTEESAR 2

kashe ac dake dakin ta lulube tadalilin rawar
sanyin da takeyi, ranar dae daga ita har
momy basuyi bacci ba, momy ta rasa abinda
ke damun ‘yar tata, duk ita ma hnklinta ya
tashi.
Gari na wayewa momy taje ta sami abba
ganin yanda jikin nata yyi tsanani, gashi sae
aikin kuka take, duk ita ma tabi ta daga
hnklinta don akwae soyayya da shakuwa
mai karfi tsakaninta da ‘yar tata don ita
kadae take gani taji ddi idan ta tuna mijinta
na farko umar, har daki abba ya shigo duba
intisaar din, “me ya sameki fatima, ina ke
maki ciwo?” ya tambayeta dadamuwa yana
yaye bargon da momy ta lullubeta dashi, ita
dae ba baki sae kuka, abba yashiga
lallashinta yana cewa”damabaki da lfya ne
fatima, kuma bakiyi maganaba tun jiyan?” ta
girgixa masa kai kawae, xainab tashigo
dakin hankalinta a tashe bayan ta tambayi
ihsaan ina intisaar don ita har tayi shirin
islamiyya da yake tare suke wuce, ihsaan
tace mata “my aunty is sick,” hkn yasatayo
bangaren nasu da saurinta, abba ya dubi
xainab da tashigo yace”je ki ki kiramin Ali
xainab,” tace to sannan ta fice da sauri, a
hanya suka haduda kursum take tambayrta
ko intisaar ta shirya don ita ma shirin
islamiyyar tayi, tunda Aliyu yyi masu mugun
duka ranannan suka fara xuwa makaranta
gaba dayansu dama, xainab tace “bata da
lfya baxa taje ba,” kursum tace “hva de me
ya sameta,” xainab ta yarfehannu tace nima
bn sani ba ynxu ma ya Aliyu xan kira abba
ma yana can, kursum tayi sashin nasu da
sauri xainab kuma ta tafi kiran Aliyu, tana
isa tayi sllma ta shiga palon, baya nan, tayita
kwada sllma ko yana cikin daki amma shiru,
sanin halin yayan nata ne ya sanyata
karasawa cikin bedroom din nasa yana ko
xaune laptop a gabansa yasa earpiece
kunne daya yana danna laptop, ya daka
mata tsawa a fusace yana cewa”baki da
hnkli ne don ubanki ko ke jahila ce,baki san
idan kika yi sllma a waje kika ji shiru gaba
xakiyi ba, xaki afko min cikin daki, ban
hanaki wannan habit din ba,” au ashe ma
yana jinta, ta tabe baki cikin rashin damuwa
tace “dama abba ne ke kiranka” ta juyafuu
xata wuce ya mike da sauri yana cewa
“xainab, xainab,” amma bata tanka masa ba,
ya fito palon da sauri har ta fice ya bita da
sauri yana kiranta, ta dawo tana kallonsa
fuskarta a hade tace”gani,” me yasa abba ke
kirana, ya tambayeta yana kallonta don dae
yasan sae da dalili ake kiransa, don kan
abba ya kirasa sau daya ya kira haisam sau
goma,”nima ban sani ba, intisaar dae ce
bata da lfya shine yace naje na kiraka” ta
fadi tana kallonsa, gabansa ya fadi yace “to
menayi ake kirana” tace “ni kuma ina xan
sani” hnklinsa ya tashi yace “me tace wa
abban?” tace “oho, ni ina shigowa abba
yace nayi maxa naje na kiraka” don ta gaji
da tambayoyin nasa, bai damu da ohon
datace masa ba ya kara tambayrta “ya mood
din abba yake” tace a kage “kai yaya ni ma
ban sani ba abba nacan yana jiranka,” ta
juya ta yi gaba ta barshi nan a tsaye. Ya bita
da sauri kuma yana kiranta, ta juya rai bace
tana kallonsa yace “ina abban?” tace”yana
can dakin momy” ya xaro ido yace”yana
me?” tace “oho! tayi gaba abinta” ta fara
suspect dinsa ita kam. Tana komawa
sashinsu intisaar abba ya tambayeta meya
tsayar da ita kuma ina Aliyun, tace”nemansa
nke a gidan abba amma gashi nan xuwa” ya
dubi momy da ta xauna tayi jigum yace “ki
hado mata tea xainab,” ta mike tace to
sannan ta fita, tana fita sae ga inna, tun
daga waje suka dinga jin muryarta kmr
speaker tana cewa”me ya samu intisaar din,
ni rahmatu,” abba ya juya rai bace yana
kallonxainab yace “donuwarki ca nayi ki ji ki
gaya wa inna taxo ta daga mana hnkli a nan
ynxu?” xainab ta mike da sauri ido a waje
tace “wllh tllh abba ban je wajen inna yau
ba ni,” abba bae sake cewa komai ba har
inna ta shigo dakin, “bukar me ya sameta
wae” abba ya dubeta yace “shine ae xa a
dubata don bbu wanda yasani,” inna tasaki
salati tana girgixa kai tace “Allah ubangiji
dae ya bata lfya wllh duk hankalina ya tashi
da aka je aka gya min,” abba bae sake tanka
mata ba tana ta surutanta, illa Aliyun da yake
jira, murya can ciki Aliyu yyi sllma, duk
jikinsa yyi sanyi, ynxu yarinyar nan sae ta iya
bude baki tace yyi mata wani abu dama,
inna ce ta amsa masa da karfinta tana cewa
“maxa shigo,” hankalinsa ya kara tashi ya
shigo palon ya tsaya yana waige-waige kmr
munafuki, abba yace”karaso mana” da kyar
yyinamijin kkri ya shiga dakin, ya rusuna ya
gaida abba don duk yau bai je gaisheshi ba
gashi har karfetara, ya juya ya gaida inna
ma sannan yace”abba gani,”
.
Dama fatima ce bata da lfya, shine nace a
kiraka ka dubata, abba ya fadi yana kallonsa,
Aliyu ya saki ajiyar xuciya, sannan ya maida
dubansa ga kangadon yana kallonta, idonta
a lumshe yake, duk da dae ba bacci take ba,
ya karaso kusa daita yace “meke damunki?”
tayi shiru kmr mae bacci, hkn ya bata masa
rai don yasan idonta biyu, a dan fusace
yace”kinajina xakiyi min banxa?” inna cikin
tsawa tace “kai mahaukacin wani gari ne,
baka ga bacci take ba yarinya tana fama da
kanta xaka dinga mata ihu,” xainab ta
karasa kusa da ita tana bubbuga kafarta a
hankli tana kiran sunanta, ta bude ido tana
kalln xainab din, Aliyu ya juya yana kallon
abban nasa yace “ko dae a wuce da ita clinic
kawae abba” inna tayi karaf tace”wllh bbu
inda xa a kaita, gamu da likita a gida kace
xa a wuce da ita wani wajen, meye amfanin
ka” Aliyun ya dubeta rai bace yace “to ni din
Allahn musuru ne da xan san abinda yke
damunta,” cikin tsawa inna tace “shiyasa
naga an kai fadila asibitida bata da lfya, don
ubanka ba kai ka dubata ba ka bata
magunguna da allurori ba kuma gashi nan
ta warke,” Aliyu ya dubeta a walakance ya
kauda kai kawae, abba yace “shknan bari a
kaita asibitin ka iya tafiya” da sauri yace “aa
abba bance baxan dubata ba ae, guri nake
jira su ban na dubata,” ya fadi yana
kallnsuinna, haisam ya shigo dakin da
sllmrsa ya karasa kusa da intisaar din ya
xauna cike da damuwa yana kallonta yace
“intisaar me ya sameki, dama jiya baki dalfya
baki yi magana ba,” ta sunkuyar da kanta
kawae sae hawaye, nanya shiga lallashinta,
ya dube abba yace “asibiti xamu wuce
abba?” inna tace “asibitin lfya ga likita a
gida, ynxu xae dubata ae” sllmrsu hajiya da
umma ne yasa kowa yyi tsit a dakin, momy
ce kadae ta amsa masusuka shigo suna
cewa ashe abinda ya faruknan, momy ta
basu waje suka xauna sannan suka gaisa,
suka tambayeta mae jiki tace masu da sauki,
hajiya tace Allah sarki duk ta rame sae kace
warce tayi sati tana jinya, umma tace wllh
kuwa baiwar Allah, inna ta tabe baki tace
“ikon Allah” xainab ta girgixa kai cike da
takaici, ynxu har anje an barbada masu
shine suka kwaso jiki suka xo gulma,
kumatasan baxae wuce kursum ba ko
rahma, abba ya dubi gaba dayansu yace “to
ae kwa bashi waje yyi aikinsa de ko” hajiya