INTEESAR 2

ta mike tana cewa”me xae hana, Allah dae
ya bata lfya yasa xakkan jikine,” suka mike
gaba dayansu har da yaran xasu bar dakin,
Aliyuyace “to..to abba ya xa ayi treatin din
nata?” abba da har ya kai bakin kofa xae fita
ya juya yana kallonsa cikin rashin fahimta
yace “kmr ya fa?” yace”aa…dama…emm, to to
ae naga sae da magunguna da allurori xa
ayi treatn din nata, kuma ni….” sae kuma yyi
shiru yana kallon tagan dakin, abba
yyimurmushin takaici ya girgixa kai yace “to
nawa xa a baka?” inna ta mike ta saki salati
tana girgixa kai tace “ita intisaar din sae…..”
da sauri abba ya katse ta yace “aa baaba ae
hakkinsa ne bari a basa” nawa ne kudin
treatment din gaba daya? Abba ya tambaya
yana kallonsa, cikin bacin rai haisam yace
“abba ka bari na wuce da ita asibiti kawai,”
abba yyi saurin cewa “aa haisam ka bari xae
dubata,” abba ya sake tambayrsa nawa xae
basa, yyi shiru kmr me lissafi sannan yace
ba tare da ya kalli abban nasa ba “dubu
takwas da dari biyar gaba daya,” abba yyi
murmushi, haisam cike da takaici yace “to
yyi kyau, ka dubatani xan baka,” da sauri ya
juya yana kallon haisam din rai bace yace
“to da baki na xan siyo kayan ne koya? Ko
kuma ina da kudin xan tsaya cewa abba ya
bani,” inna cikin ihu tace “Allah ya babbake
mae krya sannan ya tsinemasa,” Aliyun ya
juya ya galla mata harara sannan ya dauke
kansa, haisam ya ciro dubu biyar daga
aljihunsa ya mike xae fita abba yace ina
xaka, yace xan dauko kudi ne,abba yace
nawa ne a wajen ka ynxu, yace dubu biyar,
abba ya ciki dubu hudun haisam ya mikawa
Aliyun ya karbe yana kirgawa, duk wannan
abinda akeyi a kan idonsu hajiya ne, hajiya
taji kmr ta maida dan nata ciki don murna,
sae murmushi take yi, umma kuma ji tayi
kmr ta tsine ma haisam da bai yo hali irin ta
Aliyu ba, shekaranjiya tace ya bata dubu
goma yace bai da, amma sae gashi ynxu ya
kirgo har dubu biyar ya bada don a duba
wata bnxa ita kam bata san irin dan da Allah
ya bata ba, momy kam sunkuyar da kanta
tayi tana jin duk abinda sukeyi cike da
takaici, intisaar kuwa idonta ta rufesbda
axabar da take ji ko ina na jikinta ciwo yke
mata barin ma kanta sannan kuma ga
ciwon mara shima ya kunno kai, abba kam
tuni ya fice su hajiya suka bi shi a baya a
xuciyarsu suna fatan Allah yasa cikita yo,
don rahma ca tayi masu amai take ta
kwararawa, Aliyu ya dube inna yace”a bata
tea kafin na dawo, xan je siyo abinda ya
kamata,” ya fice haisam ya bisa a baya da
sauri, sai da suka kai tsakar gidan sannan
yace “canjin nawa xaka dawo da knan?”
Aliyu yace kmr ya, haisam yace eh ae dubu
tara aka baka, kuma dubu takwas da dari
biyar kace, Aliyu yyi masa wani irin kallo
sannan yace “to da kafa xanje siyo
magungunan?” sannan yyi tsakiya wuce
yana cewa “dn ma kun samu xan bata lkcn”
.
. Su Aliyu na fita inna ta mike tana tambayr
intisaar din me xata ci, ta girgixa kai alamar
ba komai, xainab tace”to ki daure kisha tea
din” inna ta dauki kofin ruwan shayin ta isa
kusa da ita tana cewa “tashi ki sha kafin ya
dawo to” intisaar ta girgixa kai murya can
kasa-kasa tace “wanka xan fara yi,” momy ta
shiga bathroom ta hada mata ruwan
wankan sannan ta mike da kyar jiri na
kwasarta ta shige bayin, ko da ta fito rawan
sanyi ta dinga yi, inna ta lullubetatana cewa
“ikon Allah, ciwan lkci daya ya kwantar da
ita,” ya haisam ya shigo dakin yana tambayr
ko Aliyun ya dawo,inna tace “ina fa! yana
can yana sokwanci” haisam ya girgixa kai
yace “ni dae wllh inna nafi son a kaita
asibiti,” inna tace “wae ni kuna bani mamaki
wllh, ga likita a gida kuyi ta kiran asibiti,”
haisam yace “to shknan, ni xan wuce kd ne
ynxu ina da wani aiki a can amma yau xan
dawo in’sha Allah,” inna tace “to Allah ya
kiyaye” yace “ameen” sannan ya karasa kusa
da intisaar yana kallnta yace “Allah ya
sauwake kanwata kinji” tayi murmushi, a
hnkli tace “ngdyayana” yyi ma momy ma
sllma sannan ya fita. Da kyar inna ta lallabata
tasha kunun da ta dama mata, xainab sae
fama kallon agogo take yi dn har sha daya
ya wuce, tun kusan karfe goma da Aliyu yaje
siyo magunguna har ynxu bai dawo ba, tuni
bacci ya dauke intisaar din bayan inna ta
bata paracetamol kafin Aliyun ya dawo,
amma har karfe sha biyu bbu Aliyu bbu
lbrinsa, “kai jama’a ko dae wannan yaron
bata yyi ne” inna ta fadi tana kallon momy
da xainab dake dakin bakinta a bude, momy
dae bata ce komai ba, xainab ta tabe baki
ita ma bata ce komai ba, wasa-wasa har
karfe biyu bbu Aliyu, inna na idar da sllh
tana xaune kandarduma cikin ihu tace
“amma wannan anyi tsinannan yaro,” daga
momy har xainab sae da suka raxana sbda
irin bude muryar da inna tayi, momy tace
“kai inna, kika san uxurin da ya tsayar
dashi,” a fusace inna tace “yaci ubansa shi
da uxurin,” ku bni waya na kira bukar,
momy tayi ma xainab ido alamar kar ta kira
mata abban, inna ta mikawa xainab din
wayar tana cewa “maxa kira min uban
nasa” xainab ba don ranta yaso ba tace ma
inna baya xuwa bayan ta kara wayr a kunne
kmr me kira, don ita da momy ta barta kiran
abban xatayi, ita kam bata san irin yayan
nata ba, basu san tuni abba ya kira momyn
yana tambayrtajikin intisaar din ba tace
masa da sauki sosae, yace Aliyun ya bata
duka magungunan tace masa eh sannan
sukayi sllma, xagi kam Aliyu ya sha shi a
wajen inna ba adadi, har da dan hawayenta,
“ni da nasan abinda tambadadden yaron
nan xae yi knan da asibiti kawae na bari
muka wuce, gashi ynxu yrnya na ta shan
axaban ciwo ba magani, shi kuma bukar na
rasa uban me xae sa ya dinga kashe
wayarsa ni kam, ynxu wa xae kai mu
asibitin gashi haisam ba ya nan,” daga
momy har xainab bbu wanda ya tanka
mainna, intisaar kam jikinta yyi xafi sosae
kmr wuta, hka inna ta ishesu da mita tana
hawaye, wajen karfe uku da rabi wayan
intisaar yyi kara xainab ta dauka tana kallon
me kiran, faruuq ne, da har xata ajiye don
bacci intisaar din take yi sae kuma ta fasa ta
daga, suka gaisa ya tambayeta intisaar din
fa, tace “bacci takeyi wllh, bata da lfya,” cike
da damuwa yace “subhanallahi, me ya
sameta” xainab ta yarfe hannu tace “wllh
bamu sani ba, tace dae ciki da kantake mata
ciwo,” yace “tun yaushe?” tun jiya da
daddare wae,yace “ya salam! kunje clinic
ne?” tayi shiru ta rasa me xata ce, yyi saurin
cewa “ohk… Gani nan xuwa,” ya kashe wayr,
inna tace “faruqu ne?” xainab ta gyada mata
kai kawai, cikin minti goma sha biyar faruuq
ya iso gidan, hanklinsa ya tashi sosae, momy
da ta bar masu dakin ya rage inna daxainab
kawae, ta tashi xaune tana kallon faruuq din
da ya sata gaba yana tambayrta inda ke
mata ciwo, cikinta t.a nuna masa da kai,
yasa hannu ya danna cikin nata ta xaro ido
tace “waii! ciwo yake min” me ya buge ki a
nan ya tambayeta yana taba goshinta da yaji
xafi sosae, ta girgixa masa kai kawae sae
hawaye, duk ya rude ya shiga lallashinta