HAUSA NOVELINTEESAR 2

INTEESAR 2

tallabota, ta fada jikinsa ya turata da sauri

sannan yyi maxa ya riko hannunta dn

faduwa xatayi, ya fara fixgarta kmr wata

dabba tana binsa jikinta ba kwari sae jiri

dake kwasarta amma bae bari ta fadi ba, yyi

sashinsu daita, har bakin kofarsu ya kaita ya

bude kofar yana kallonta, duk a tsorace

take, ya tura ta ciki har tana faduwa yyi

gaba, momy ta taso da sauri ganin yanda

‘yar tata ta fado falon tana cewa “lfya

intisaar,”

 

Karfe tara abba ya shigo duba intisaar, har

lkcn inna na falonsu bata tafi ba, abba ya

shigo mata da fruits da tsire a leda ya ajiye

mata yana tambayarta ya jikin, tace “da

sauki abbana” sannan ta mike ta shige

bedroom ta bar masu falon, abba ya dubi

inna yace “nan xaki kwana knan yau?” tace

“aa dama kai nake jira, kasan iskancin da

wannan dan naka yyi mana yau” abba yyi

shiru yana kallonta, ta tabe baki tace “wllh

bkayi sa’an da ba bukar, shanya mu yyi a

nan ya gudu da dubu taran da kuka bashi,

sae wannan yaron faruuq yaxo ya dubata

kmr xata mutu” abba ya tsura mata ido yana

kallonta ya kasa cewa komai, “wllh ko minti

goma ba ayi da fitan yaron ba ka shigo, tun

safe yaki barin gidan nan yana kanta, gashi

ynxu jiki alhmdllh, yaron mutunci ne wllh”

abba ya jinjina kai cike da takaici yace “to

shknan yyi masa kyau, hkn yaga yafimasa

alkhairi,” inna ta mike ta tabe baki tana

cewa “ka rakani bangarena” yace “to

sannan yyi sallama da momy, ta rakosu har

bakin kofa tana ma inna sae da safe. Karfe

goma haisam ya shigo duba intisaar, momy

tace “kar dae ynxu ka dawo haisam” yace

“wllh kuwa momy,” bae bar sashin nasu ba

sae kusan karfe sha daya, suna ta hira da

momy da intisaar da ynxu bata jin ciwo a ko

ina na jikinta. Da safe ita da ihsaan suka je

gaida abba, kmr ba ita tayi ciwo jiya ba,

Aliyu na xaune a falon kansa sunkuye bayan

abban nasa yyi masa tatas, intisaar ta nemi

gefe ta xauna ganin Aliyu duk sae jikinta ya

mutu, ta gaida abba ya amsa da fara’arsa

yana tambayarta jiki, tayi murmushi tace

abba da sauki, ta kalli Aliyun da har ynxu

kansa a kasayake tace “ina kwana yaya,” ya

dago yana kallonta idonsa yyi jajir ya kauda

kai murya can ciki yace “lfya lau,” ta mike

tana kallon abba tace”abba sae anjima,”

yace “yauwa intisaar, kin dae sha

magungunanki dae ko,” tace “eh abba

nasha” yace “to yyi kyau” sannan suka fice,

Aliyu ma ya mike yana kallon abban nasa

yace “Allah ya huci xuciyarka abba,” abba ya

dauki kudin da Aliyun ya ajiye masa ya

watsar masa dasu yace “nace kaje da su

bama bukata,” Aliyu yyi jim sannan yace

“kayi hkuri abba, ita ma kanwata ce bbu

yanda xa ayi na karbi kudi wae don xan yi

treatn dinta, na gya mka dalilae na nayin

hkn, kuma bayan hka ma ni bn samu na yi

treatn dinta ba ” abba ya galla masa harara

yace “dalilanka na bnxa, ina ruwanka da

uwartaka da har xakayi hkn wae sbda taji

ddi, wae kae me uwa, ka burge uwarka

amma kuma ka xubda kimarka a idanun

mu, kai ko kunya ma bka ji ba, wawa

kawae, da’alla get out malam” Aliyu ya juya

jiki ba kwari ya bar falon. Da yammar ranar

ummi kanwar faruuq taxo duba intisaar,

yayan nata ya ajiye ta sannan ya wuce, sun

jima suna hira da intisaar da xainab kmr da

can sun saba sannan suka kaita gun inna,

inna ta rasa inda xata sata don farin ciki,

tsaraba ta hada mata lkcn da faruuq din ya

kirata wae yana waje don baxae shigo ba

wae, momyma ta hada mata nata abun

arxikin sannan intisaar ta rakota don xainab

tuni hajiya ta aika khadija ta kira mata ita, a

bakin gate suka gaAliyun a xaune fuskar

nan tasa bbu alamar rahama, ummi ta

gaisheshi, ya dago kai yana kallonta fuska

daure yace “lfya,” intisaar ma ta gaidashi

gabanta na faduwa yyi bnxa da ita har suka

fice, ummita juya tana kallonta tace “waye

wannan kuma,” intisaar ta kirkiro murmushi

tace “babban yayanmu ne” don ita ynxu

tunanin yanda xatashiga gidan yana bakin

gate din take, har bakin motar faruuq din

intisaar ta rakata suka yi sllma faruuq ya

kashe mata ido yace “sae nakiraki bbyna,” ta

kauda kanta da sauri tana murmushi ta bar

wajen, ya ja motar suka wuce, ta kasa shiga

gate din ta tsaya a waje, har wani bari

jikinta yake yi don tsoro.

Dago ta momy tayi tana kallon ta tace “jikin

ne intisaar?” ta girgixa kai ta mike da

kyartace “aa faduwa nayi,” bedroom ta

shige momy ta bita da kallo ta kasacewa

komai tausayin yar tata ya cika ta, ita ta rasa

abinda ke damunta. Washegari da ciwan

kan ta tashi amma bata bari momy ta gane

ba don bata son tana daga wa uwarta ta

hnkli, faruuq ya kirata da safen yana

tambayr jikinta tace yyi sauki sosae, tare

abba ya shigoda Aliyu falon nasu wajen

karfe tara, lkcn innana nan a xaune don tun

karfe bakwae ta iso sashin nasu da kunun

ta da kosae ta kawo ma intisaar, ihsaan ta

rungume abban nata ya daga ta sama yana

cewa”how re yhu momyna” tace fyn sir, ya

dubi intisaar yana murmushi yace “ya jikin

fatima? Tayi murmushi tace “da sauki

abbana,” to Allah ya kara sauki, kina shan

magani dae ko? Tace “eh abba ina sha,”

Aliyu ya nemi guri ya xauna yana satan

kallon momy dake xaune tana linke kayan

ihsaan, ba tare da ya kalleta ba murya can

ciki-ciki yace “ina kwana,” tayi kmr bata ji sa

ba, ya tabe baki ya gaida inna ita ma tayi

masa bnxan, ya dake yana duban intisaar

din yace “ya jiki,” ta sunkuyar da kanta tace

“da sauki,” sannan tace masa”ina kwana” ba

tare da ya kalleta ba yace”lfya lau,” ya sata

kallonabbansa da ke kallon Tv, yace ba tare

da ya kalleta ba”kwaso min medicines din

da kike sha nagani,” ta mike jiki ba kwari ta

shiga bedroom ta kwaso masa

magungunan da faruuq ya bata ta durkushe

gabansa ta xubesu tana kallonsa, inna ta

tabe baki tace “ko uban me xae yi dasu idan

ba gulma ba,” bae tanka mata ba ya shiga

dudduba magungunan ya cire guda biyu a

ciki yace “ki ajiye wa innan kar ki sha,” to

kadae tace, inna tayi karaf tace “akan wani

dalilin, kafi sa sanin aikin nasa ne malam,”

da’alla kwashe magungunanki ki maida

kirabu da wannan gantalallen, dariya ma

abun yaba Aliyun, abba ya dubesa

yace”sbda me xata ajiye su,” ya shafa kanshi

yace “sbda aikinsu kusan iri daya ne gaba

daya, dama xan karo mata wasu ne shiyasa

nace ta ajiyesu,” abba yace “no ka bari ta

gama da su tukunna sae ka bata wanda

xaka batan, shima yasan abinda ykeyi ae

yaron,” Aliyun yyi shiru bai ce komai ba, inna

ta galla masa harara tace”munafukin bnx

kawae, idan yaga ubansa ya dinga yi kmr na

Allah,” Aliyun ya mike yana kallon abban

nasa yace “abba xan wuce clinic sai na

dawo,” inna tace “kaji makaryacin bnxa, ca

xakayi xaka je gantali,kai din aiki kke xuwa,”

ya tabe baki bae tanka mata ba, ya dan kalli

intisaar din ya watsa mata hararar tsana

yace “Allah ya sauwake,” ya juya ya fice.

Suna tsakar gidagaba dayansu intisaar na

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button