INTEESAR 3

wanda ya rikesa,” ta mike fuskarta a daure
ta haura sama ta bar su nn falo, a step duka
hadu da Aliyu ya galla mata harara, don me
baki tashe ni ba, ita ma ta galla masa
hararan tace “sbda baka isa ba,” tayi gaba ta
bar sa nn tsaye, ya sauko suna ta
tsokanarsa wae tsoron uwargida yasa ya
makara, dole suka jirasa yyi wanka snn ya
fito shima sanye da farar shaddar, ba
karamin kyau yyi ba don ko hmm bari dae,
ya shiga dakin Inteesar tana xaune gaban
madubi, kallo daya tayi masa ta madubin ta
dauke kanta yace “kinyi break,” tayi bnxa da
shi, ya daga kafada yace “sae na dawo kiyi
mani adduar Allah yasa ayi a sa’a,” ya juya
xae bar dakin ta fashe da kuka ba tare da ta
shirya ba, ya juyo yana kallonta, ya karaso
cikin dakin yace “an maki wani abu ne ko
kawae jin ddin kukan ne ke damunki,” bata
tanka sa ba, ya tabe baki ya juya ya fita, suka
fita gaba daya da abokan nasa suna masa
mitan ya bata lkci dayawa ko mantawa yyi
yau ce ranar daurin aurensa da sahibarsa
shi dae bae ce masu komai ba har suka
shiga mota suka bar gidan, suna fita daga
gate yace “kun san wani abu ku je kawae
gani nn xuwa, ina son na kai fateema can
gida daga can sae na wuce,” namesake
dinsa yace “wae meye hka kke yi ita bata
san hanyar gidan ba sae an kaita baka
ganin saura yan mintoci,” Aliyu yace “ni dae
kuje kawae ina nn xuwa, ya bude motar ya
koma cikin gidan,” suka yi tsaki kusan gaba
dayansu suka yi gaba, yanda ya barta hka ya
dawo ya tarar da ita, ya dauki hijab dinta ya
mika mata yace “tashi to na kai ki gida,”
bata yi musu ba ta mike ta karbi hijab din
tasa takalminta suka fita, motarsa ya fito da
ta bude sit din baya ta shiga, bai ce mata
komai ba ya ja motar suka bar gidan, suna
isa gida bata jira ya gama parkin ba ta bude
mota ta fice, ya dakatar da ita da sauri ko
kallonsa bata yi ba ta shige gidan da gudu
sae sashin inna, hkn yyi mugun bata masa
rae kuma yasan da mutane cikin gidan shi
yasa bae bi ta ba, ya ja motar kawae yyi gun
daurin aure, mutanen dake tsakar gidan har
da su Hajiya suka bi ta da kallo murna fal
cikinsu, umma ko ta dinga tuntsira dariya
tana guda kawayen Hajiya na taya ta.
ta xube jikin inna ta fashe mata da kuka, a
rude
inna ta shiga tambayarta “meye faru, ke da
waye,” ta kasa cewa komai, inna ma ta bare
baki
ta fashe da kukan, Anty Nafeesa ta fito daga
daki
da sauri tana kallon Inteesar tace “wa ya
kawoki,”
inteesar tayi kkrin tsayar da kukanta tace
“shi ya
kawo ni,” Nafeesa tace “ynxu kuwa muke
shirin
tafiya can gidan, kukan meye hka kike yi, ke
dae
baki ji ddi ba wllh,” a fusace cikin kuka inna
tace
“ban son iskanci ke uwar wa yyi maki
kishiya,”
inna ta mike ta daga inteesar tana share
hawayenta suka shiga daki tana cewa “ki
rabu da
shi, bbu abinda xaki koma gidan nn kiyi,
kuma
bbu uban da ya isa yace ki koma tunda nace
baxa ki ba, ina nn ina jiransa daga shi har
ubansa,” Anty Nafeesa tayi murumushi ta bi
su
cikin dakin. Gida ya cika fal da yan uwan su
Hajiya da umma da abokanan arxiki ana ta
shagalin biki har da su Dj a gidan, inna na
daki
xaune gefen Inteesar da ta kwanta tana
bacci
tana mata fiffita ita ma tana gyan gyadi, jin
kide
kide yasa inna ta farka ta fito da gudu har
Anty
Nafeesa da wa inda ke falonta suka tsorata
suka
dinga tambayar lfya, ko kallonsu bata yi ba
ta fita
xuwa tsakar gida da gudu, Anty Nafeesa ta
ma
xaci abu ne ya sami Inteesar suka shiga
dakin da
sauri suka tarar baccinta take, wasu kuma
suka
bi inna da sauri a baya suna tambayar wae
Hajiya
mai ya faru, inna na isa tsakar gidan cikin
daga
murya tace “nashiga uku uban wa ya
gayyato wa
innan shaidanun gidan nn” ta fadi hkn a
fusace
tana nuna masu Dj da kayan kide kiden
nasu, aka
kashe wakar dake tashi, Umma tace “to
naga dae
yau ranar farin ciki ne inna kuma dae daga
yau ba
sake ganinsu xa ayi ba,” inna tace “kin ci
ubanki
mai dattin hula, kaji min rubabbiyar
yarinya,” ta
karasa kusa da masu dj tana huci ta shiga
bubbuga speakers din tana cewa “ku fitar
min
dasu kar na babbake su, gidan da na ba
gidan
yan iska da shaidanu bane” ba shiri Hajiya
tasa
aka shiga kwashe su a barrow ana fita
dasu, hka
ma canopies din duk sae da tasa suka fita
dasu
tana jaraba an cika gidan dan’ta da tarkace,
hka
mutane suka dinga kallon inna wasu na
dariya
can ciki ciki, “kuma duk shegen da ya xauna
kusa
da flawowin da na ban yafe masa ba duniya
da
lahira tunda dae ba shi ya dasa masa ba, ko
tsinke kuma kar a wurgar a tsakar gidan
nn,” ta
fadi tana huci kmr kirjinta xae fashe, Hajiya
dae
shigewa daki tayi kunya kmr ta nutse, wae
juyawar da inna xata yi sae ganin momy tayi
xaune suna hada salad, ta saka salati kmr
xata yi
kuka tace “Allah ya wadaranki Zainabu, ynxu
uban me ya kawo ki cikinsu idan ba
shisshigi da
neman suna ba, ca suka yi maki yi suke
dake
mara xuciya kawae wahalalliya, ni dama
nasan
tun ba yau ba kika tsani yarinyar nn kike
son
ganin karshenta, idan ba hka ba taya xaki
kwaso
kafafuwa ki taho nn cikinsu, wllh daga yau
kar ki
sake nuna kin san Inteesar, ita ma bata
sanki ba
wllh, shi yasa ma da ta xo daxu bata nufi
inda
kike ba dan tasan ba sonta kike ba” ta
karashe
maganar da kuka ssae har da tari, ta bar
wajen
tana cewa “kuma yau bbu ubanda ya isa ya
bar
min tsakar gidan da’ na hka, duk sae an
wanke
shi an goge wllh,” dariya wasu har da
xubewa
kasa, ranar dae a dari dari su Hajiya suka yi
shagalin bikinsu, jefi jefi inna kan fito taga
ko an
xauna kusa da flowern da tace kar a xauna,
bbu
wanda yyi gigin xama kuwa. Da Magrib
bayan
kowa ya watse inna ta tasa su Hajiya gaba
sae
da suka wanke tsakar gidan su Zainab da
kursum
da Maryam din Anty Nafeesa dariya kmr
cikinsu
xae fashe, dama momy tun daxu ta shiga
ciki
amma sae da inna taje ta fito da ita wae har
da
ita yar bakin ciki maxa su gyara ma dan ta
tsakar
gidansa, sae da taga sun kusa gamawa snn
ta
koma sashinta tana cewa “wahalallun bnxa
kawae” karfe takwas abba yyi kiran Inteesar
falonsa, ta karasa falon a sanyaye tayi
sallama ta
shiga, Zaune ta tarda Aliyu a falon yana
sanye da
shadda brown colour, ta nemi gefe ta xauna
tana
kallon Abba tace “ina yini Abba,” Abba ya
amsa
yana kallonta yace “ya gidan,” ta sunkuyar
da kai
tace “lfya Abba,” Abba ya nisa yace “ranar da
nace ku taho da Zainab don me kika ki bin
ta,” ta
daga kai tana kallon Aliyu dake kallonta,
Abba ya
gyada kai yace “to yyi kyau, kuma har ynxu
baki
fara karatun ba ko?” a hankali tace “Abba na
kusan farawa,” Abba yyi shiru yana kallonta
snn
yace “to Allah yasa, ki tashi ki bi mijinki, a
cigaba
da hakuri, Allah yyi maku albarka” Aliyu ya
mike
yana kallon Abba yace “nagode Abba,” ko
kallonsa Abba bae yi ba, Inteesar ta yi shiru
kmr
xata yi kuka tace “Abba inna tace ba
ynxu…….”
Abba ya hade rae yace “inna tace me, tashi
maxa
ki koma dakin ki, kuma bance ki shiga cikin
gida
ba,” bata san tayi mugun ba Abba haushi
ranar
da ya aika Zainab kiranta taki xuwa ba, a
sanyaye Hawaye na kkrin sauko mata ta
mike
tace “Abba sae da safe,” yace “Allah ya tashe
mu
lfya,” Aliyu ma yyi masa sai da safe ya bi
bayanta
suka bar falon
.
.. Suna fita Aliyu ya kamo hannun Inteesar
da sauri ganin bata son jerawa da shi, ta
juya tana kallonsa yace “mu fara shiga na
gaida momynki,” tayi masa mugun kallo tace
“ae ko baka fada ba dama momyta ce bance
taka ba,” bai ce mata komai ba yana rike da
hannunta suka isa sashinsu, shi yyi sallama
ganin tsaya kawae tayi ta rike kugu, duk da