HAUSA NOVELINTEESAR 3

INTEESAR 3

dankwalinta ta ja dogon tsaki tace “sannu

balagaggu, kuma ba girmata ba har haifata

Safeena tayi,” tayi masu kallon bnxa xata

haura sama ya bita da sauri ta saka gudu

amma duk da hka sae da ya kamota ya

shaketa yace “uban waye sa’anki a nn,” ta

fashe da kuka tana kiran Abbanta ya jefar

da ita kan kujera yana kallon safeena yace

“in ta maki ki gyara mata xama ni na sa ki,”

xata mike daga kan kujerar yace “in kika

tashi sae na watsa maki mari,” ganin bbu

wasa a tattare da shi yasa ta koma tana

kuka, yana kallon Safeena yace “kije ki shirya

mu siyo abinda kika ce,” murna fal cikinta

ganin abinda aka ma Inteesar tace “ni a

shirye nake,” ya ciro makullin motarsa, ta

mike ta bi bayansa suka fice daga gidan

tana ma Inteesar wani irin kallo tana jujjuya

ido. Basu dawo gidan ba sae kusan karfe

sha biyu, inteesar na kwance bayan ta gama

cin kukanta har lkcn bata yi bacci ba, muryar

safeena taji tana cewa “bby ka bari mu

shiga ciki mana don Allah ka bari,” cikin

kissa take maganar, Inteesar ta mike ba tare

da ta shirya ba kuma bata san dalili ba ta

shige bathroom ta kulle

.

Yau safeenah ta cika sati uku gidan Aliyu ko

sau daya kallon kirki bae taba hadata da

Inteesar da ta xame mata jaraba a gidan ba,

gashi ba dama tayi mata ko da kwakkwaran

kallon bnxa Aliyu ya hau ta da bala’i don

yace mata baya so, ta kyaleta kawae

yarinyace kuma yarinta ke damunta, bbu

yanda Safeena ta iya don tana mugun son

Aliyu kmr rayuwarta duk abinda Inteesar

tayi mata sae dae ta gaya masa, wani lkcn ya

shareta wani lkcn kuma ya samu Inteesar

din ya tsoratata ko kuma ya sa ta kuka,

shima ta lura ba a son ransa yake yin hkn

ba, ko sau daya Inteesar bata taba shiga

kitchen tayi masu girki a gidan ba ko da

kuwa ranar girkinta ne sae dae Safeena tayi

a bisa umarnin da Aliyu ya bata, don ca yyi

ta rabu da ita kawae ta dinga girki kullum,

littafin girki kadae ne ke taimakonta don

bbu abinda ta iya da ya wuce tafasa ruwan

xafi, cikin ikon Allah kuwa idan tayi sae ya

dan yi ddi da taimakon littafin, ta adana

littafinta ssae, iyaka idan ta fito inteesar ta

shiga ta dafa indominta ko taliya, ganin

rashin amfaninta a gidan yasa Aliyu ya kai ta

da kansa tayi registratn din jamb ana saura

sati daya a rufe, kila idan ta fara xuwa

makaranta xae samu kwanciyar hankali don

bata tsinanasu da komai sae tashin hnkli a

gidan, wani lkcn yakan yi mamakin ashe

yarinyar nn na da baki hka, kuma

fitsarewarta lkci daya da rashin tsoran

kirkin da take masa yana mugun basa

mamaki shi dae ba wasa da ita yake bare

yace kuma tunda ya auri safeena bae

nemeta ba, gaba daya ta daina tsoransa sae

taga yyi kanta xae doketa ta marairaice

masa tana kuka, gashi abu kadan sae ta

bara masa baki ta fasa masa ihu a gida ba

gaira ba dalili, shi kuma yana kyaleta ne

kawae sbda Abbansa don ko kadan

Inteesar bata gabansa don bbu abinda

Safeena ta rage shi da barin a wajen

kwanciya shi yasa yake ji da ita, duk da

yakan yi murmushi idan ya tuna 1st nyt

dinsu da Inteesar, da yanayin da ya shiga da

har yau bae ji hkn gun Safeena ba, darajar

da Inteesar ke ci kadae a gunsa knn banda

hka da bata isa ta taka masa matarsa da

yake ji da ba, Safeena kanta na mamakin

yanda Aliyu ke share Inteesar duk da

iskancin da take xuba masa, ita bbu abinda

yafi daga mata hankali ma irin mugun

rainata da Inteesar tayi, amma tasan duk

Aliyu ne ya ja mata tunda ga irin tonan

asirin da yyi mata washegarin ranar da aka

kawo ta gidan, wani lkcn takan yi murmshin

takaici tace nasan tanadin da nayi maki

yarinya kiyi yanda kike so lkcn ki ne ynxu.

Ranar da ya kaita tayi registratn din jamb

can ya barota ya bata kudin mota ya wuce

office, bata bari adai daita sahun ya shigo

da ita layinsu ba ta sauka ta basa kudin don

yau tana son ta kare ma anguwar kallo

tunda dae ba fita take ba, tana isa bakin

gate dinsu taga wata yarinya da baxata

wuce ta ba rike da wani kyakkyawan yaro a

hannunta tana waya, Inteesar ta dauke

kanta ganin sun hada ido, yarinyar tace

“sannu fa,” inteesar tace “yauwa, ngdd,” ta

danna bell mai gadi ya bude mata ta shiga,

taji yarinyar ta burgeta yar kyakkyawa da

ita, safeena na kwance a falo da kawayenta

ta wucesu tana yatsine fuska ta haura sama,

bayan kwana biyu Aliyu ya hadata da driver

taje ganin centre dinta, tana dawowa ta

sake haduwa da yarinyar a bakin titi ita ma

xata karasa layin da kafa tana rike da danta,

bayan sun gaisa Yarinyar tace “amma aure

kike a gdan nn ko,” Inteesar tayi murmushi

tace “eh,” yarinayr tace “to ya sunanki,”

inteesar ta gaya mata yarinyar tace “ni kuma

sunana Aneesah,” Inteesar tayi murmushi

tace “to yaron ki fa,” yarinyar tace “sunansa

Abdush-shakur,” Inteesar ta karbi yaron

tana murmushi tace “fyn shakur,” har suka

isa dai dae gidajensu, yarinyar tace “kina da

kyau ssae, ina son mu xama kawaye,”

inteesar tayi dariya tace “to ai kema kina da

kyau,” Aneesah ta bata wayanta tace “sa

min nmbrki to inteesar,” Inteesar tace “wllh

wayan mijina ne a hannu na ki bari idan na

samu waya,” Aneesah tace “to mu shiga

kiga gidana mana” inteesar ta xaro ido tace

“mai gidanki baya nn,” Aneesah tace “A’a a

Abuja yake aiki sae wkend yake dawo wa,”

inteesar ta bi ta suka shiga gidanta, gidane

babba kmr nasu bbu abinda ya xama

bakonta a gidan don duk suna da shi a

nasu gidan, har bedroom ta shiga da

Inteesar, inteesar ta shantake suka dinga

hira kmr da can sun san juna, ta girka masu

abinci ta kawo masu dakin suka ci suna ta

hira tana ba Inteesar labarae kala kala,

Inteesar taji kmr kar ta bar gidan, karfe

shidda saura ta rako Inteesar har bakin

gate kmr kar su rabu, har shakur ya saba da

Inteesar don har da kukansa, wae sae da ta

isa jikin gate tukunna gabanta ya shiga

faduwa a xuciyarta tace “Allah yasa ya Aliyu

bae dawo ba,” mai gadi ya bude mata gate

ta shiga taga motarsa a parke a garage

xuciyarta yyi mugun bugawa da kyar tana

jan kafa ta shiga gidan.

 

Bata tarda kowa cikin falon ba tayi sum sum ta

haye

sama ta bude kofar dakinta a hankali ta

shige,

xama tayi kan gado ta sauke ajiyar xuciya,

jin an

fara kiraye kirayen sllh Mahgrib yasa ta mike

ta

tashiga cire kayan jikinta xata dauki xani ta

daura ta shiga wanka don bata sllh taji an

bude

kofar dakinta, ta tsorata ssae tace “wayyoo

Abbana,” ta durkushe da sauri tana kare

kirjinta

da hannunta don undies kadae ne jikinta, ya

karaso cikin dakin yana kallonta yace “daga

ina

kike,” taki cewa komai kuma taki dago

kanta

tana durkushe inda take, ya karasa gabanta

ya

dago ta ta shiga nonnokewa a tsorace tace

“wayyo ya Aliyu ban sa kaya ba,” ko kulata

bae

yi ba ya jinginar da ita jikin bango yana

mata

wani irin kallo nn da nn yanayinsa ya canxa,

duk

ta tsure tana son durkusawa yaki barinta ta

fashe masa da kuka, ya sauke ajiyar xuciya

ya

sake ta ya fice daga dakin ta tajawo xaninta

da

sauri ta shiga wanka, tana fitowa ta gama

shafe

shafenta ta saka kayan baccinta, ta saka

gashinta cikin net ta fita dafa indominta,

xaune

ta tarda Aliyu a falo safeena na jingine

jikinsa

suna kallo, ya bi ta da kallo har ta wuce su

tana

tabe baki ta isa kusa da fridge ta dauki five

alive ta bude ta sha ta rufe ta mayar da

sauran

don bbu mai shan five alive a gidan sae ita,

ta

juya ta watsa masu harara ta shige kitchen

yin

abinda ya sauko da ita ya mike da sauri

safeena

na tambayarsa inda xa sa bae kulata ba ya

haura sama ya shiga dakinsa bae dau lkci

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button