INTEESAR 3

tym kiyi jamb,” kmr xata yi kuka tace “ni ka
kyaleni, idan baxa ka koya min ba in tashi in
tafi,” ya daga kafada ya shiga koya mata har
ya gama yace kin gane tace eh, ta mike ta sa
Hijab dinta ya bi bayanta, sae da ya fara
shiga daki ya dauki makullin motarsa snn ya
fito ya bude mata motar ta shiga shima ya
xaga ya shiga suka bar gidan, hka ta dinga
bacci a motar har suka isa, yace “ke baki jin
magana nace ki bari wani yr din, ki ci gaba
da islamiyya kin ki ko,” ko kallonsa bata yi
ba ta bude motar xata fita ya mika mata
dubu biyu yace xan xo daukarki anjima, snn
ya ja motarsa ya wuce, ita kuma ta shiga
ciki. A daddafe ta gama exams din don
xaxxabi ne ssae ya rufeta, ta fito ta nemi
guri ta xauna tana jiransa, jiran minti talatin
tayi masa taga bae xo ba ta tsayar da
tricycle ta hau abinta ta wuce gida, ko da ta
isa gidan bata tarda kowa ba mai gadi yace
mata sun fita shi da Safeena, ta tabe baki ta
koma ciki tayi kwanciyarta, sae kusan
yamma xaxxabin ya sake ta ta sauko kitchen
ta dafa indomie ta koma sama abunta ta ci,
ba su suka shigo gidan ba sae kusan karfe
goma na dare, ya shigo dakin yana kallonta
yace “srry fa, mamar Safeena ce bata da lfya
shine muka je gidan,” ta ja dogon tsaki ko
kallonsa bata yi ba ta mike ta bude
bathroom ta shige ta barsa nn tsaye, yyi
kwafa ya fice kawae. Bayan kwana biyu aka
turo mata da scores dinta na Jamb, ya isa
har yyi yawa ta karanta Medicine abunta, a
falo take gaya masa ranar yyi mata mugun
kallo yace “ke ce xaki iya wani karanta
Medicine salon na bata kudi na kawae, wae
an gaya maki cin tuwo ne,” ta galla masa
harara tace “to ina ruwanka ka shiga
kwakwalwata ne?,” ya mike tsaye yana
kallonta yace “xan fa babbalaki wataran a
gidan nn yarinyar nn,” tayi tsaki ta juya ta
koma sama tana cewa “ni wllh abba xanje
na gaya ka da abba, ina ruwanka da abinda
xan karanta, kai wa ya hanaka karanta
medicine” Safeena da aka siyo sabon
takardar koyon girki ana kitchen ana girki
tace “sae hakuri dear, ta xata wasan yara ne
medicine din Honey,” yana hararanta yace
“ke kuma wa yasa bakinki a nan,
Bayan sati daya inteesar na kwance ita
kadae a daki wajen karfe sha biyu na rana,
safeena ma na dakinta waka sae tashi yake
kmr xae tsaga gidan, Aliyu ya fita aiki,
inteesar ta gaji da kide kiden da safeena ke
sa wa gashi ba daman tayi mata magana ta
ci ubanta Aliyu baya nn, ta mike ta dauki
Hijab dinta ta fita daga gidan, mai gadi yace
“oga yace kar na bari kowa ya fita,” ta yi
shiru tana kallonsa kmr ta shakesa, can dae
tace “bae ce maka xan je duba jarabawa
bne,” mai gadi yace “aa ni bae ce min hka
ba,” ta galla masa harara ta isa kusa da gate
din tace “to sae ka kirasa kaji,” ta bude gate
din ta fice daga gidan, gidan Aneesah ta
shiga, ta tarar tana ta karatun littafin hausa,
taji ddin ganin Inteesar ssae tace “kwana da
yawa ‘yar uwa ina kikaboye gashi ba daman
na shiga gidanku,”inteesar tayi dariya tace
“ina nn ke dae, ba nace maki xan xana jamb
ba,” Aneesah tace “ohh hka fa ya scores yyi
kyau?” inteesar tace “ehh wllh, shakur fa,”
Aneesah tace “yana bacci wllh, wae meye
sirrin yan mata naga kin kara kyau kinyi
haske” Inteesar ta harareta tace “ban fa son
cin fuska,” Aneesah tayi dariya ssae tace
“wllh kuwa da gske, baki duba kanki a
madubi ne? ko dae….” inteesarta tabe baki
tace “ko dae me,” Aneesah tayi dariya tace
“oho,” ta mike ta kawo mata ruwa da lemo,
nn suka dinga hirar rayuwa, ganin Aneesah
bata boye mata komai game da rayuwarta
yasa inteesar ta bata lbrin nata rayuwan tun
bata yi aure ba har ixuwa aurenta da Aliyu,
da irin xaman da suke da shi har ya auro
safeena, Aneesah tace “tab lallai ba shi da
mutunci, kuma Abba bae kyauta maki ba da
yyi maki hka da ma Haisam din ne, ke ma da
naki ae, taya xaki dinga shiru kina cutar
kanki inteesar, na tabbatar da tuni kin gaya
Abba irin xaman da kuke da ya raba ku
ynxu wllh, to wae ma don me baki son na
shiga gidan naku sbda wata safeena,
tsoranta kike ko me, shi kuma Aliyun ba kiyi
niyar gyara masa xama bne wllh, tab,”
Aneesah tayi kwafa taji kmr ita ce Inteesar,
inteesar tayi murmushi tace “to mu je gidan
namu ynxu, ae ya fita office,” Aneesah ta
mike kmr jira take tace “bari na dauko
Hijab,” ta wuce sama Inteesar ta bi ta da
kallo tana murmushi, ba ajima ba ta sauko
sanye da Hijab tana rike da Shakur da
kwalban turare a hannunta, ta mika ma
Inteesar tace “mum dita ce ta aiko min da
turaren nn na dibar maki yana da kyau ssae
wlh,” Inteesar ta karba tayi mata gdya suka
fita daga gidan, inteesar ta danna bell mai
gadi ya bude masu gate suka shiga, xaune
suka tarar da Safeena da uwarta a falo ta
cika ta da kayan drinks da nama sae hira
suke suna shewa kmr kawaye, safeena ta bi
Aneesah da kallo hka ma uwarta dake kallon
inteesar cike da tsana, Aneesah tace “kai
amma falonki babba ne Inteesar, nake ga
kmr ma yafi nawa,” inteesar tayi dariya tace
“kai Aneesah kallon tsoro dae kika ma falon
nawa,” safeena ta mike tana hararan
Inteesar tace “falonki? Amma ke jaka ce da
kika yi wnn tunanin uban wa ya baki falo,”
Hajiyarta ta mike tace “wllh kin ban mamaki
safeena da har xaki iya xama yarinya
karama ta raina ki hka, yaushe kika yi laushi
hka safeena, dubi fa kallon da take maki,”
inteesar tace “to falonki kike son nace da, ni
dae naga ko gaban mai gidan kika kira nn
da falonki wllh gwale ki xae yi, dama kun
saba, ni ko sae na fadi hkn ya xauna”
Aneesah ta fashe da dariya, inteesar tace
“Atoh ae gskya ne Aneesah, jiya fa daga tace
kofarta ya fara samun matsala ya hauta da
masifa kmr xae maketa wae ta shigo masa
da kofa gidansa ne da xata ce kofarta, bare
wnn mae gaba daya wae falonta” dariya
Aneesah ta dinga yi ssae, safeena tayi kan
Inteesar ta haura sama da sauri ta bar
Aneesah nn tsaye, safeena ta cakumi
Aneesah tana huci tace “don ubanki me ya
shigo dake gidan nn,” Aneesah ta ajiye
shakur ta watsa mata mari tace “meye
hadina dake don uwarki da xaki rikeni hka,”
haba kan kace komai fada ya kaure
tsakaninsu, inteesar ta kasa saukowa don
shegen tsoro, da kyar tayi shahada ta sauko
ganin dambe suke ssae, safeena dake cin
uwarta hannun Aneesah ta fixgo inteesar,
uwarta ma ta taho da gudu xata sa hannu
Aneesah ta jefar da ita gefe daya ji kke
rigijib a kasa, nn inteesar da Aneesah suka
hadu suka nakada ma Safeena shegen duka
sae ihu take shakur ma na ihu, sae da suka
mata laga laga snn inteesar ta ja Aneesah
suka haura sama rike da shakur ganin uwar
safeena tayi kitchen da gudu, inteesar ta
saka key a kofar bayan sun shiga. Ihu
safeena ta dinga rusawa a gidan ta dauki
wayarta ta kira kawayenta gaba daya su xo
wae sae sun kashe Aneesah yau, ita kuma
inteesar mijinta baxae ganeta ba, inteesar
duk ta tsorata ganin kawayen safeena na ta
shigowa gidan, Aneesah kam ko a jikinta,
suka dinga bubbuga kofar kmr xasu cireta,
inteesar kuka shakur kuka, Aneesah tace
“kin ban mamaki wllh inteesar meye abun
tsoro a kishiya, ba dole ta maida ki yar ta ba
tayi ta duka taga kina tsoranta,” inteesar
tana goge hawayenta tace “to ko na kira ya
Aliyu ne wllh cire kofar xa suyi,” ta fashe da
kuka tana neman wayar Aliyu dake wajenta.
.
Inteesar tadauki wayar jikinta na rawa ta
shiga kiran Aliyu, dontsabar takaici Aneesah
kasa daukar Shakur dake ta tsala ihu tayi,
sae kallon Inteesar take kmr ta maketa, Aliyu