INTEESAR 3

na daga wayar ta fashe masa da kuka, ya
mike tsaye da sauri yace “me ya faru,”
cikinkuka tace “ko ba Safeena bace wae
xata kasheni ta kira kawayenta da yawa a
gidan har da mamarta gasu nn xasu cire
kofar wae su kasheni,” Aneesah ta girgixa
kai cike da takaici ta kinkimi danta tayi
hanyar kofa xata fita da gudu inteesar ta
karasa kusa da kofar ta rikota tace “wayyo
so kike su kashemu, don Allah ki bari ya
dawo,” da sauri inteesar ta cire makullin,
Aneesah ta ma rasa me xata ce mata, su
safeena har lkcn basu fasa buga kofar da
suke suna xage xage ba, Aneesah ta shiga
mayar masu ita ma, hka suka dinga xage
xage ta uwa ta uba, sum sum inteesar tayi
jikin window har lkcn a tsorace take ta
tsaya tana jiran shigowar Aliyu, ko minti sha
biyar ba ayi ba ya shigo gidan da motarsa,
tayi gun Aneesah da ke ji kmr ta cire kofar
ta fita suyi ta takare tace “Aneesah ya
dawo,” Aneesah ta galla mata harara tace
“da’allah ja can kin ban waje, kin ban
mamaki inteesar,” Aliyu ya hauro sama yana
kallon safeena da kawayenta kusan su biyar
uwarta ma na tsaye cikinsu, wani mugun
tsawa ya daka ma kawayen nata yace “b4 d
count of 3 duk ku fice min a gida kar na sa
a kulle min ku karuwan bnxa kawae yan
iska nn din gidan ubanku ne ko na uwarku,
kaji min bitches ” tuni jikin safeena ya dau
rawa, kawayen nata kuwa sum sum suka
shiga sauka kasa yana binsu da kallo yana
huci, ko kallon uwar safeenar bae yi ba yyi
kan safeena ya fixgota ya kai mata mari
yace “gidan nawa xaki mayar joint din yan
iska? To maxa ke ma dauko gyalenki ki bi su
bana son na bude ido na ganki cikin gidan
nn, get out” cikin tsawa ya karasa maganar,
Hajiya na kallonsa da mamaki tace “Aliyu a
kan idona kke walakanta min ‘ya ta,” ya juya
yana mata mugun kallo yace “an
walakantata din, ae dama a walakance kika
bani ita, kuma a walakance na sameta ko
kun manta ne,” yyi tsaki ya shiga buga kofar
Inteesar, inteesar na hararan kofar
tace”waye?” yace “uwarki ce, kin xo kin
bude min kofa ko sae na taka ki,” inteesar
tayi tsaki tace “to baxan bude ba,” Aneesah
ta bude baki da mamaki tana kallon kofar, a
lallai wnn gantalallene shi kuma ba shi da
gwani, a fusace ya juya ya shige dakinsa,
safeena ta fito sabe da gyale tana matsar
kwalla tana kallon uwarta, uwar tace “ke ina
xaki maxa koma ita kanta naga ba kyaleta
yyi ba, hka yake dama,” safeena tace “hka
yake wllh….” fitowar Aliyu yasa safeena tayi
tsit, ko kallonsu bae yi ba ya isa jikin kofar
inteesar da spare key a hannunsa, inteesar
na jin ya saka key cikin kofar ta mike tsaye
da sauri tana kallon Aneesah ta nuna mata
bathroom murya kasa kasa tace “ki shiga
bayi kafinya shigo,” ko kallonta Aneesah
bata yi ba, har ya bude kofar ya shiga dakin,
da sauri inteesar ta juya xata bar wajen ya
fixgota a fusace ta fada kansa ta fasa masa
ihu a tsorace tace “wllh xan gaya ka da
Abba,” idonta ya tsaya kallo da alamar
mamaki, ya sa hannu ya dago kanta yana
kallonta da kyau, a hankali ya shiga kare
mata kallo snn taga ya sake ta, Safeena da
uwarta na bakin kofa suna kallon
dukabinda ke faruwa, har ya juya xae fita ya
juya yana mata mugun kallo yace “wnn
wacece,” ta hararesa tace “kawata ce,” yyi
shiru yana kallonta, shakur ya karaso kusa
da shi yana cewa “daddy,” da maganarsa da
bae gama fitowa ba, ya sunkuya yana
kallonsa snn ya shafa kanshi yace “hw re
yhu dan daddy,” snn ya juya ya fita shakur
na biye da shia baya, sum sum safeena da
uwarta suka bar wajen, bbu yabo bbu
fallasa Aneesah tace “dauko min yarona na
tafi gida” Inteesar tace “lah har xaki tafi ki
bar anjima mana ko ruwa fa baki sha ba,”
Aneesah ta harareta tace “ae wllh kin bada
mata Inteesar, ni dauko min yaro na na bar
gidan nn,” safeena da uwarta na shiga daki
uwartata ta kira Hajiyar Aliyu, tace “maxa
maxa ki taho ki ga irin rikon da danki ke ma
‘ya ta Hajiya, hka muka yi dakudama ya
dinga dukan safeena,” Hajiya ta bude baki
tana salati tace “wllh Alhaji ya hanani xuwa
gida Aliyu ban san dalili ba, amma kar ki
damu xan kirasa ynxun nn Hajiya” inteesar
na shirin kwanciyawajen karfe goma Aliyu
ya shigo dakin, bata ko kallesa ba ta gama
abinda xata yi ta shige cikin bargo, ya dawo
gefenta ya yaye bargon yana kallonta, ta
hararesa tace “meye hka,” ya dan marairaice
mata yace “yau ma tausaya min xaki yi
kanwata,” nn da nn ta fara kuka kmr jira
take tace”ni wlh wllh ka fitar min a daki ina
gaya maka,” yyi dariya ya dawo gefenta ya
kwanta yana shafa cikinta yana murmushi
xae yi magana sae kuma ya fasa, ta turasa
tace “ni fa bana son iskancin nn ka fitar min
a daki,” yana ci gaba da shafa cikinta yace to
wacece wnn yarinyar da na gani daxu a
gidan nn,inteesar ta buge masa hannu tace
“kawata ce,” yace “a ina kika samo ta,” tayi
masa bnxa, ya rungumota ssae, sae da ya
jagwagwalata snn ya fita daga dakin ganin
irin kukan da take a tsorace
.
Inteesar na kwance a daki tun safe take ta
bacci ta kasa tashi, da ta farka xata koma
taji dae yunwa ya isheta ta mike xaune ba
shiri tana kallon agogo, taga karfe daya, ta
tabe baki ta jingina jikin gadonta bbu
wanda ya damu da ko ta karya ko bata
karya ba a gidan, kuma ranar lahadi ne Aliyu
na gida, ta sauko daga kan gadon da kyar
idonta na juya mata ta dauki xani ta daura
kan rigar baccinta ta bude kofa ta fita tana
jan kafa, xaune ta tarda shi da safeena kan
dinnin suna lunch sae hira take masa tana
dariya, shi kam sae dae yyi murmushi yana
cin abincinsa, da wuya kaga dariyan Aliyu,
inteesar ta tabe baki ta shige kitchen suka
bi ta da kallo, Aliyu ya girgixa kai yace
“yarinyar nn dae bata da amfani a gidan
nn,” safeena ta dauke kanta ta ja bakinta
tayi shiru don ta san tana iya magana ya
gwaleta ynxu ba karamin aikinsa bne,
inteesar taji bata jin cin indomie, ta dan
bude tukunyar safeena tana lekar abinda ke
ciki, cous cous ne da miyar hanta, ta dan
yatsina fuska duk da hka kawae taji abincin
ya shiga ranta, ta rufe tukunyar a hankali
tayi xamanta a kitchen din tana tunanin me
xata dafa, indomien dae at lng lst tayi decide
ta dafa ta mike tsaye ta daura ruwan, ta bar
shi ya fara tafasa snn ta shiga xuba
abubuwan da xata xuba, hka kawae taji
bata jin cin kwae, indomien na fara dafuwa
taji xuciyarta na mugun tashi, ta koma baya
da sauri tana rike da cikinta da ya hautsine
nn da nn, ji tayi amai na neman xubo mata
ta toshe bakinta da hannunta da sauri ta
fice daga kitchen din da gudunta tayi
hanyar stairs har tana tuntube, duk suka
bita da kallo Aliyu ya mike ya bi bayanta da
sauri yana tambayarta me ya faru ya ma yi
xaton yankewa tayi, safeena bata yi gigin
binsa ba don tasan halinsa, da kyar Inteesar
ta iya karasawa dakinta ta bude kofar bayi
da sauri ta durkushe nn bakin kofar ta
shiga kwarara amai kmr xata amaye hanjin
cikinta.
Aliyu ya shigo dakin da sauri ya karaso
bakin kofar bayin yana kallonta, har lkcn
amai take ssae gashi bbu komai cikinta, ya
durkusa gabanta a hankali ya dafa ta yana
mata sannu, buge masa hannunsa tayi, tayi
xaman dirshan a bakin kofar tana mayar da
numfashi ta fashe da kuka ta jingina jikin
bango duk ta rasa inda xata sa kanta, juye
juyeta shiga yi a bakin kofar tana kuka tana
kiran Abbanta, ya fixgota ya daka mata
tsawa “kina hauka ne,” ko kallonsa bata yi
ba ta rarrafa jikin gado ta xauna ta jinginar
da kanta tana ci gaba da kuka tana mayar
da numfashi, ya mike ya dawo kusa da ita