INTEESAR 3

kansa suka xube kan gado, ya fada gefenta
da sauri ganin ynda take mayar da
numfashi ya dagota ya rungumeta yana
mata sannu, cikin kuka tace “wllh ka cire
min cikin nn bana so,” ya toshe bakinta da
sauri yana kallon cikin idonta yace “ni ina
son abu na
.
Kuka ssae Inteesar ta shiga rera masa, shi
kam saekallonta yake yana murmushi, ta
fara kkrin mikewa xata sauka daga kan
gadon ya riketa da sauri yace “ina xaki,”
cikin kuka tace “wllh sae ka cire min cikin
nn bana so,” ya rufe bakinta ya hade rae
yace “kar ki sake cewa na cire maki bbyna,
sae kace wani kaya,” ta buge masa hannu,
ya harde kafarsa cikin nata tayi yar kara, ya
rungumota yana kallonta ya shiga shafa
mata cikinta yace “me xaki ci, dubi fa yanda
kika rame tun kan ba mu je ko ina ba, a hka
xa muyi rainon cikin kika san ma ko yan
biyu ne kanwata,” ta fashe masa da kuka
tana kiran Abbanta, ya rankwashi kanta
yace “ki daina min kmr ihsaan a nn, ke baki
san kin girma ba tunda ga bby nn cikin cikin
ki” bata san lkcn da ita ma ta rama
rankwashin ba tana kukan da xa a iya
kiransa da na shagwaba duk da har ga Allah
ba shagwaba take ba, ya wara ido yana
kallonta, ta koma baya da sauri nn da nn ta
tsorata ya lakaci hancinta ya ja kunnenta
yace “kin ci sa a bbyna na jikinki da yau na
maki shegen bugu, ya Aliyu kike rankwashi
” bae jira me xata ce ba ya kwantar da itaya
mike ya fita, ta mike xaune da sauri ta hade
kanta da gwiwa ta fashe da wani sabon
kukan ynxu wae ciki ne da ita da gske yar
yarinya da ita, ba a dau lkci ba ya dawo
dakin rike da kofin tea yace “maxa tashi ki
sha na saka maki ruwa aman ya tsaya,”
kallon tean kawae tayi taji xuciyarta na tashi
ya kai mata baki ta mike da sauri sae cikin
bayi ta shiga kwarara amae, ya isa kusa da
ita ya durkusa ya dafata yana kallonta yana
mata sannu, sae da ta gama snn ya gyara
mata jiki ya maidota cikin dakin, a hankali ta
kamo hannunsa tana hawaye tace “don
Allah ya Aliyu ka tausayamin ka cire min
cikin nn bana so,” ya galla mata harara yace
“wllh idan kika sake gaya min wnn maganar
sae na bata maki rae, ki cire ynxu na gani
mana,” tayi shiru tana kallonsa xuciyarta na
tafarfasa, ita ko ta fi sa iskanci xae gani
kuwa, ta juya tayi kwanciyarta tana mayar
da numfashi, tean da bata sha ba knn har
bacci ya dauke, sae kusan sha daya na dare
ta farka yana gefenta a kwance, shima amai
ne ya farkar da ita, ya cire mata ruwan dake
hannunta ganin a gigice ta farka tana
neman sauka ya raka har bayin ta shiga
kwarara amae, gashi dae ba komai cikinta,
ya xuba mata ruwa a kai ya fito da ita, daga
ita har shi ranan basu yi baccin kirki ba,
jikinta yyi xafi ssae ta rasa inda xata sa
ranta sae kuka take masa yana rungume da
ita, da kyar bacci mai nauyi ya dauketa
kusan asuba. Washegari monday bae je aiki
ba sbda ita, tana kwance jikinsa bayan ya
lallabata ta sha tea kadan yyi mata
allurorinta wajen karfe goma safeena ta
kwankwasa kofar tare da sallama, yace ta
shigo, ta bude kofar ta shigo sae da
xuciyarta ya kusan harbawa yanayin da ta
gansu, shi singlet da 3qtre ne jikinsa, ita
kuma rigan bacci iya cinya, ta kirkiro
murmushi ganin allurori a bedside drawer
tace “Ayya bata jin ddi ne dear,” ba tare da
ya kalleta ba yace “eh, ya akayi?” tace “Allah
sarki, Allah ya sauwake fateema sannu,”
inteesar ta dago kai da kyar ta watsa mata
harara, ta mayar da kanta, safeena ta dauke
kanta da saurixuciyarta na tafarfasa tace
“yauwa dear Momy ce ciwonta ya tashi
shine xanje ynxu, amma ba ddewa xanyi ba
dan da sauki,” yace “ita kuma kullum ciwon
nata ke tashi, baku da abinci ne a gida, ae
yunwa ce ke kawo ulcer ” tayi shiru tana
kallonsa ya tabe baki yace “Allah ya
sauwake, ki duba side drawer can bedroom
dina ki dauki dubu goma,” tana murmushi
tace “to ngd dear,” snn ta juya ta fice tana
murmushin mugunta. Da yamma safeena ta
shigo gidan, har lkcn Aliyu na dakin
Inteesar, lkci lkci yakan yi tunanin ko dae
kawae ya rabata da cikin nn ne ta huta
shima ya huta, don ba karamin wahala yaga
take sha ba tun kan cikin ya kai ko ina, ynxu
ma da kyar ta samu bacci ya dauke, irin
masu shegen laulayin nn ne me wahala, ya
dan yi tsaki, ita ma ragwancinta ne kawae
yyi yawa, duk ta fige lkci daya sai kace
wacce tayi wata tana ciwo, safeena ce ta
bude dakin ta shigo ya daga kai yana
kallonta, tayi murmushi tare da lumshe ido
tace “Aliyu so nake kaje duba mum dita
ynxu, kuma ka tafi mata da wnn maganin
nn da ka bata ranan nn wae taji ddinsa,” yyi
shiru yana kallonta,snn taga ya sauke ajiyar
xuciya yace “wae ynxu?” ta dan yi fari da ido
murna fal cikinta, amma ta hade rae tace “to
da yaushe kke tunani,” yace “ok,” snn ya
kwantar da Inteesar dake jikinsa ya mike
tsaye ya juya yana kallonta bacci take, kan
yace komai safeena tayi saurin cewa “to
kaxo ka wuce,” ya juya ya fice daga dakin, ta
bisa da kallo tana murmushi, dakinsa ya
shiga ya shirya snn ya fito da makullin mota,
tana hararansa tace “to haka xaka je mata
hannu rabbana,” ya koma ciki sae gashi ya
fito da kudade, ta rakasa har jikin mota snn
ta manna masa kiss a baki, yyi murmushi ya
lumshe idonsa yace “sae na dawo bbyna,”
snn ya ja motar ya fice daga gidan, ta doka
uban tsalle tashiga kiran layin uwarta cikin
murna tace “wayyoo mum, saura naki gashi
nn xuwa.
Aliyu na fita gidan ya wuce wani babban
super market ya yayiwa mum din safeena
siyayya bata wasa ba akalla ya kashe kusan
50k. Ya fito ya shiga motarsa ya dau hanyar
gidan mum xuciarsa duk a cushe ya rasa
dalili,gashi yana son kiran inteesar a waya
ta wayar sa dake hannunsa amma ya kasa a
haka dai ya cigaba da driving har Allah ya
kai shi lpy. Yana isa gidan su safeenar
maigadi ya bude masa get yana washe baki
kasancewar aliyu na hannun damansa ne
yana da yawan kyau,ko kula da gaisuwar da
me gadi yake yi masa bai yi ba ya mika masa
2k aiko maigadi ya hau godia da kiraki
hannu kawai ya daga masa yai hanyar
parkin shade dinsu ya ajiye motarsa ya
duba seat din baya cikin magungunan daya
ajiyewa a a first aid box dinsa ya dauki na
ulcer ya jefa a cikin ledar magunguna da
safeena ta bashi. Sallama yayi cikin nutsuwa
ya shiga falon dai dai lokacin mum ta fito
aiko ganin aliyu yasa ta dan yatsina fuska
shiko jiki na bari kamar yayi gamo ya sauko
dg kan kujera yana kwasar gaisuwa,fuska
ba yabo ba fallasa suka gaisa yai mata ya jiki
sannan ya mika mata ledojin hannunsa ya
mike xai mata sallama kenan tace “aliyu
baxaka tsaya ko ruwa kasha ba?” Sai ya
tsinci kansa ya kasa yi mata musu alhalin bai
taba cin komai na gidan ba. Komawa yai ya
xauna xuciarsa na cikin dumuwa yana
buqatar ya duba inteesar kuma ya san by
nw ta tashi dg baccin da ya barta tanayi.
Tunanin haka yasa ya ajiyar xucia tare da
fesar da iska mai xafi hade da lashe
labbansa da suka bushe. Mum ce ta shigo
riqe da jug a akan tray da cup da roban
ruwan c’est bon,ta tsiyaya masa xobon ta
mika masa ya kai hannu biyu tare da yin
godia…. zai kai bakin shi kenan wayarsa tai
ringing hakan ya dakatar dashi da sauri ya
ajiye xobon ya karkace ya xaro wayar dg
aljihun jeans dinsa duk a tunaninsa ko
inteesar ce ta kira shi…
Sae da Aliyu ya fara xuwa asibiti ya dauki
maganin da xai kai ma mamar safeena snn
ya ja motarsa ya kama hanyar gidan jikinsa
a mace, ya na isa yyi parkin a waje, ya fito
da maganin yana kare ma gidan kallo snn ya