HAUSA NOVELINTEESAR 3

INTEESAR 3

shiga, suka gaisa da mai gadin ya karasa

balcony ya danna bell, yar aiki ta bude masa

kmr jira take ya shiga falon ta nuna masa

kujeran da xae xauna da sauri shima kmr

wnda ake contrl ya xauna inda ta nuna

masa yana bin ko ina na falon da kallo, yar

aikin tayi sama kiran Hajiya, yana kallo

Hajiyar ta shigo falon ya dan dukar da kansa

ya gaisheta ta amsa da fara’a kmr gske snn

yyi mata ya jiki, ya bata maganin da ya kawo

mata, ta amsa tana gdya tana jujjuya

maganin, ya ciro kudin da ya dauko daxu ya

mika mata yace “ni xan koma Hajiya” ta

karba da sauri tana gdya ta mike tace to

bari na kawo maka ruwa kasha mana, yace

“A’a Alhmdlh ae daga gida nke,” tace “to

bari na baka sako ka kaima safeena,” yace

“to,” ta mike ta yi sama, sae ga ta ta sauko

da dan wani parcel, ya karba yyi mata

sallama, ta rakosa har bakin kofa tana sa

masa albarka snn ta koma murna fal cikinta,

yana barin anguwar yaji hka kawae yana

son ganin abinda ke cikin parcel din, parkin

yyi gefen titi snn ya shiga budewa, wani

ruwa ne ya xuba jikinsa ya matsar da parcel

din daga jikinsa da sauri amma duk da hka

sae da ruwan ya taba kayansa da farko wari

yaji, ya yatsine fuska kawae kuma sae yaji

wni mugun kamshi me ddi ya xiyarci

hancinsa, ya rufe da sauri ya ajiye parcel din

ya ci gaba da drivin dinsa. Safeena ta kasa

xaune ta kasa tsaye sae kaiwa take tana

komowa a falo, wayar uwarta ya shigo nata

ta daga da sauri jikinta na rawa tace “ya

xauna kan kujerar mumy, kuma ya karbi

ledan,” uwar ta kyalkyale da dariya tace

“wllh kuwa dota, ynxu fatanmu kawae Allah

yasa ya bude,” safeena ta doka tsalle tace ”

Alhmdllh amma naji ddi momy, budewa

kuma ba matsala bace ko a gida xan sa ya

bude bare ina da yakinin ma ya bude naji

sighn din da mutumin yace xan ji a jiki na,”

budewar gate din da safeena taji yasa tace

“wayyoo momyna ya dawo xamu yi waya

anjima,” ta katse kiran tana murmushin

mugunta, shknn ynxu sae yanda tayi da

Aliyu,” yana shigowa gidan ta karasa cikin

kissa ta rungumesa ya dagata sama ya

manna mata kiss a goshi yace “bbyna sae

kyau kike karawa kullum,” ta hararesa tace

“sae yau ka sani,” yace “A’a bbyna ina sane,”

kinsan me bbyna na dan maki barna wllh

momy ta ban turare na kawo maki da

karambani na na bude ya xuba jikina,” ta

kankamesa ta rasa inda xata sa kanta don

murna, tace “da gske bbyna, wllh sae ka

biya ni,” yyi hanyar stairs da ita yana cewa

“naji xan biya bby nawa ne,” inteesar kam

na xaune ta jinginar da kanta jikin gado, ji

take kmr ba ita ba duk ta rasa inda xata sa

ranta taji ddi, ga alluran hana aman da yyi

mata duk ya bi ya dameta, tana neman yin

aman ma ko xata samu sauki amma ta kasa,

yunwa take ji ssae amma bbu abinda ke

ranta, ko wani abinci ta tuna sae taji amai

na taso mata jikinta yyi mugun xafi ga

kishin ruwa da take ji kuma tana tsoron

shan ruwa, ta sauko kasa da kyar ta kwanta

kan tiles din dakin ko xata ji ddin ranta,

kasa daure kishin tayi ta mike xaune tana

mayar da numfashi ta rarrafa ta bude fridge

dinta taga ba ruwa ciki sae lemo, tana

daddafa bango ta fita daga dakin ta sauka

kasa da kyar ta bude fridge ta dauki ruwa ta

sha, snn ta koma sama, dae dae kofar

dakinta taji amai frm no where ta xube

wajen ta shiga kwarara aman kmr ranta xae

fita, suna daki shi da safeena duk ta gama

rikitar da shi, ya turata da karfi ya mike

tsaye ya karasa kofa ya bude ya fita safeena

ta bi bayansa da sauri, durkusawa yyi

gabanta yana kallonta, ta fashe masa da

kuka abun tausayi ta xube jikinsa muryarta

na rawa tace “don Allah ya Aliyu ka kai ni

gida, ni wllh na gaji ko ina ciwo yake min

wayyoo mutuwa xanyi,” ya rungumeta cike

da tausayi xae yi magana safeena tace

“dear,” ya juya da sauri yana kallonta,

kallonsa kawae ta tsaya yi bata ce komai ba,

ya sauke ajiyar xuciya yana kallon Inteesar

yace “ke kuma mahaukaciyar wace gari ce

xakiyi ma mutane amai a nn, idan kina jin

amai ba sae ki shiga bathroom din ki ba,

wnn ae kaxanta ce,” Inteesar ta daga kanta

tana kallonsa, da kyar ta shiga kkrin mikewa

daga inda take wani aman ya taso mata ta

shiga kwarara sa a wajen, kuka ssae ta

fashe da ta jingina jikin bango tace “wayyoo

Abbana,” kallonta kawae ya tsaya yi ya kasa

cewa komai, ta rarrafa ta shiga dakinta ta

xube kan tile tana mayar da numfashi,

safeena da sae kallon inteesar take da

mugun mamaki lkci daya jikinta yyi sanyi ta

ma rasa tunanin da xata yi, a xuciyarta tana

cewa amae kuma? to me hkn ke nufi, ta

sauke ajiyar xuciya tana kallon Aliyu tace

“me ke damunta????

.

Aliyu ya mike tsaye yana kallon safeena yace

“bata jin ddi ne,” bae jira me xata ce ba ya

bude dakinsa ya shiga sae ga shi ya fito da

mop ya gyara wajen aman, safeena ta koma

daki da sauri hannunta na rawa ta shiga

kiran uwarta, tana dagawa tace “momy wlh

ina ga fa kmr cikine da yarinyar nn,” uwar ta

mike daga xaunen da take da sauri tace

“mene? Ke wa ya gaya maki,” a rude safeena

tace “gashi nn tana ta amai,” uwar tayi salati

tace “bari xan kiraki,” ta katse kiran. Da

daddare Inteesar na kwance kan tiles ya

shigo dakin ya durkusa gabanta yana

kallonta yace “tashi ki sha kunu na karbo

maki a gida,” ta kasa dagowa ya dagota

yana kallonta ya kauda kansa da sauri, ya

kai mata kofin baki, ta kauda kai da sauri

muryarta na rawa tace “xafi,” ya girgixa

mata kai yace “ba xafi,” ta maido da kan

jikinta na rawa ta daura hannunta kan kofin

taji ba xafi ta kai bakinta yana rike da kofin

ya shiga bata, da sauri ta cire bakinta tace

“baxan yi amai ba? ya gyada mata kai ya ci

gaba da bata, yunwa take ji ssae don hka

rabi tasha ta koma tayi kwanciyarta kan

tiles, yace “kin koshi ne ta gyada masa kai

tace ruwa xan sha, yace “aa baxa ki sha ba,”

bata ce komai ba ya dago ta mayar kan

gadon duk abinda suke safeena na lekensu,

ta koma da sauri daki har da hawayenta ta

kira uwarta tace “kai ni momy wllh na gaji,

gashi can wajenta yana lallabata yana bata

koko,” uwar tace “yi shiru safeena, daxun

nn na dawo daga wurin mutumin, ca yyi

wae duk abinda xa muyi masa a kantabaxae

taba tasiri ba sbda yana mugun son cikin nn

dake jikinta,” safeena ta dafe kirji tace “ynxu

ciki ne da ita da gske ina xaune momy,”

uwar tace “ki tsaya ki saurareni mana,”

safeena na share hawaye tace “to ina ji

momy,” uwar tace “yauwa, to ynxu ca yyi

dole sae an lalata cikin in har muna son

muga aiki yyi mugun tasiri a kansa, ynxun

ma ba wae bae yi tasiri bane, don xae dinga

lallaba ki kuma sae abinda kika ce masa xe

yi, sae dae fa hankalinsa gaba daya na

gunta sbda wnn shegen cikin, kuma fa baki

isa ki hanasa xuwa gunta ba amma, don

hka kawae ki kwantar da hankalinki jibi ki

xo mu koma kauyen yace yana jiranmu, ciki

kuma kmr ya bare ne,” safeena ta share

hawayenta xuciyarta fal murna tace “to

ngdd momyna,” ta katse kiran tana

murmushin mugunta. Da safe Aliyu ya bae

ma safeena i.v din bikin Zainab, ta tabe baki

tana hararansa tace “to ca nayi maka ban

sani bane,” yyi shiru yana kallonta snn yyi

murmushi yace “to Allah ya baki hkuri

bbyna, amma ni dae ban san me nayi maki

ba kika canxa min kwana biyu,” ya mike ya

karasa kusa da ita ya xauna yana shafa

gashinta yace “haba yan matana,” ta

hararesa tare da buga masa hannu tace “ni

ka rabu dani,” ya rungumeta yace “haba

bbyna,” kmr xata yi kuka tace “to ba kai bne

ba baka ma damu dani da lamarina ba a

gidan ba,” yace “inji wa yace maki hka,”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button