INTEESAR 3

kakarin Aman inteesar yaji, ya saketa da
sauri ya mike tsaye ya fice daga dakin,
safeena ta bi sa da kallo xuciyarta na mugun
kuna, kasan dakin ya tarar da ita tana ta
amai ya kamata har ta gama snn ya gyara
mata jikin ya gyara dakin ya kwantar da ita
kan gado, ta rikesa muryarta na rawa tace
“sanyi nake ji yaya,” ya lulluba mata bargo
snn ya dauki I.v din da ya ajiye gaban
madubinta xae fita ya juya yaga kallonsa
take, ya dawo yana kallonta yyi murmushi
yace “kina san wani abu ne,” ta girgixa
masa kai yace “kinsan bikin Zainab saura
kwana goma ko,” ta mike xaune da sauri
tace “da gske yaya, ni ba a gaya min ba to,”
ya kamo hannunta yace “ae sun san baki da
lfya, ki bari nxt wk sae mu tafi gidan kafin
nn jikinki ya kara kwari,” ta marairaice kmr
xata yi kuka tace “to ba kila xuwa tayi ranan
ta gaya min ba ka koreta,” yace “ba ta ji ne,”
tace “to yaya wa xata aura” yana kallonta
yace “faruuq,” ta wara idonta ta fada kansa
cikin jin ddi tace “don Allah da gske yaya, kai
amma naji ddi wllh, ka bani nmbr ya faruuq
din” yace “to anjima xan baki, xanje gida
ynxu me xan ce inna ta girka maki?” tayi
shiru sae kuma ta bata rae ita da ba ma son
cikin take ba, yace kinyi shiru, tana
hararansa tace “kace mata ina da ciki ne,” ya
daga hannayensa da sauri yace “A’a” yana
girgixa kai, ta koma ta kwanta tace “dan
wake nake so ni,” yace “to, sae na dawo, kar
ki sha ruwa kar amai ya takuraki,” bata ce
masa komai ba yayi hanyar kofa, duk wnn
abinda suke safeena na labe tana jinsu, tana
jin xae fito ta bar wajen da sauri ta shige
dakinta tana murmushin mugunta, yana
fitowa ya shiga dakin safeenar
.
Bayan kwana biyu safeena ta samu ta lallaba
Aliyu wae xata gun wata yar uwarta, ya ko
barta har da bata kudi da makullin mota
dayake ta iya drivin tana ta murna a
xuciyarta tana cewa lallai sae yanda tayi da
Aliyu, ynxu kam ta yrda yana tafin hannunta
amma dae ba duka ba, tunda bata isa ta
hanasa xuwa gun Inteesar ba, amma komai
ya kusan xuwa karshe, ta fada a fili tana
murmushi, cikin kwanakin nn Aliyu na da
aiki ssae a clinic don hka ya gwammace da
ya bar Inteesar kadae a gida gwara ya
dinga tafiya da ita don tana bukatar kulawa
ssae, hka ko ya dinga yi kullum shi xae
shiryata da safe yyi ma safeena sallama su
wuce asibiti, hkn yyi mugun tada ma
safeena hankali to ta ya xa’a yi ta aikata
abinda suka sha wahala kafin su samu
bayan baya barinta a gida., ita kam Inteesar
ko kadan abinda Aliyu ke mata baya burgeta
don dai dae da second daya bata son cikin
jikinta, kuma tasan sbda cikin yake mata
hka, wani mugun tashin hankali ke xuwa
mata idan ta tuna cikin Aliyu ne jikinta, Ana
saura kwana uku bikin Zainab ya kai ta gida
duk da ba a son ranta ba don bata son su
san tana da ciki, amma ashe duk ya gaya
masu uwarsa ce kadae be gaya ma ba sae
umma, inna duk ta rikice masa wae cutar
jikarta kawae yake gashi duk ta fige ba kyan
gani, shi dae bae tanka ma inna ba ya fice,
Inteesar dae na kwance falo sae mayar da
numfashi take don da kyar ta iya karasowa
cikin gidan bayan sun sauka daga mota,
kuma da asibiti ne baya barinta ta taka da
kanshi yake daukarta su shiga ciki, inna tace
“to wae wani irin jarababben cikine wnn
dake neman kashe min ke,” ta mike xaune
tana hararan inna kmr xata yi kuka tace
“wae ni nace maki ciki gareni ne,” bata jira
me inna xata ce ba ta shiga daki tayi
kwanciyarta, inna duk ta daga hankalinta
ganin irin laulayin da Inteesar take mai
tsanani, bbu wanda bae san ciki ne da ita
ba a gidan, ko da yaushe cikin amai da
kasala take, ko maganan kirki bata son yi
sae in Aliyu na yasa ta gaba ko yana
tambayarta me take so, duk tausayinta
kawae yake, Hajiya da hankalinta yyi mugun
tashi bata ga fuskar da xata ma Aliyu
magana ba da ya shigo da ya fice daga
gidan, tab aiko gwara ta nemo yanda xa ayi
da cikin nn, ynxu Aliyu dama sae ya iya
kwana daki daya da yarinyar nn duk cika
bakinsa, hka aka yi biki hankalin inna rabi
na gurin Inteesar rabi na gun bikin, duk aka
yi abubuwa masha Allah, amma inteesar na
kwance tana fama da kanta, safeena ma ta
xo ranar bikin tana daddaga hanci ita matar
Aliyu inna ta kunyatata gaban lodin jama’ar
biki su kursum dariya kmr xasu shide, ko
minti daya bata kara a gidan ba tayi gaba ba
shiri jikinta a sanyaye har ga Allah tsoran
tsohuwar nn take, ran Hajiya yyi mugun baci
amma bbu yanda ta iya da inna, washegarin
ranar da aka kai Amarya da daddare Aliyu ya
shigo falon inna bae ko kalli innar ba ya
durkusa gaban inteesar dake kwance
idonta biyu, ya daura hannu a goshinta yace
“amma yau bakiyi amai ba ko,” a fusace inna
tace “kaji gantalalle wani irin bata yi amai
ba, ae hanjin cikinta ne kadae bae xaxxago
ba yau har tsorata nayi nace to ko su ne ke
shirin fitowa” Aliyu yyi mata mugun kallo
yace “to ke kuma wa ya somo bakin ki nn,
iyayi kawae,” sae abun ya ba Inteesar dariya
ya dago ta yana kallonta yace “Abba na
neman mu, xaki iya ko na daukeki,” ta
marairaice tace ynxu, ya gyada mata kai, ita
mugun kunyan Abba take ji har ma da
momynta, duk shigowar da momy take ta
gaisheta kar inna ta xaxxageta tace taki
xuwa, Inteesar yi take kmr tana bacci, inna
ta mike tsaye da sauri tace “bari kawae na
kama hannunta mu je,” Aliyu ya bude baki
yana kallonta yace “wae meyasa kike son
shiga tsabgar da ba taki ba ne,” bae jira me
xata ce ba ya harareta ya sa ma Inteesar
hijab dinta ya dauketa suka fice, inna tayi
kmr xata yi kuka tace “ni ban san meyasa
yaron nn ya rainani da tsufa na da furfurata
ba,” a hanya ya ajiye ta dalilin rokansa da ta
dinga yi ya ajiyeta suka karaso falon yana
rike da hannunta, da kyar ta iya bude baki
ta gaishe da Abba kanta a kasa, ita kawae
kunyarsa take ji, yace “ya jikin fateema,”
kanta a kasa tace “da sauki Abba,” yace “to
Allah ya sauwake, kina son komawa dakin ki
ne ko xaki xauna nn gun inna sbda
condition dinki” ta dago kai a hankali tana
kallon Aliyu, shima kansa a kasa yake, tayi
shiru ta rasa me xata ce don ita kam bata da
burin cikin nn ya kara girma a jikinta, Aliyu
yace “Abba da dae na tafi da ita xan fi kula
da ita a can kuma ba gida ma nake barinta
ba tare da ita nake xuwa clinic, nn ko xae yi
min nisa kuma xan takura kaina,” Abba xae
yi magana inna ta fado falon, ashe tana labe
tana jin duk abinda suke cewa tana huci
kmr xata yi kuka tace “amma munafurcinka
dayawa yake Bukar, hka muka yi da kai? To
ni Rahmatu nace bbu inda yarinyar nn xata
je aje a kashe min ita da abinda ke cikinta a
banxa a hofi a barni da wayyo Allah, don
idan an kashe su ma ni nayi hasara ba ku
ba”.
.. Aliyu ya dan yi tsaki ya kauda kai, Abba
kam shiru yyi yana ta kallon inna, ita ko ta
tsaya masu kmr soja a bakin kofa, can dae
Abba yace “to ki hada kayanki sae ki bi su,”
tayi kwafa tace “ko da naji,” snn ta juya ta
fice da sauri, Abba ya girgixa kai yace “tashi
ka dau matarka ku tafi,” Aliyu ya mike yana
kallon Inteesar, ita ma ta mike tsaye suka
ma Abba sallama snn suka fita, yana rike da
hannunta yace “mu je mu gaida momyn
ihsaan ne,” tayi kmr bata ji sa ba shima bae
sake ce mata komai ba har suka fita ya bude
mata mota ta shiga shima ya xaga ya shiga
suka kama hanyar gida, ko da suka isa tayi
bacci ya fito da ita daga motar yana rike da
ita kmr bby, safeena na kwance falo ta bi su
da kallo ya sakar mata murmushi yace
“bbyna,” tayi tsaki ta dauke kanta tacigaba