INTEESAR 3

da kallonta, sae da ya kai Inteesar sama ya
kwantar da ita snn ya sauko ya sameta, ta
mike tayitsaki ta haura sama ta bar sa nn ya
bita da kallo snn yyi mmrshi yabi bayanta.
Washegari sae da safeena ta sa ya makara
xuwa office, wanka kawae yyi ya shirya ya
dauki makullin motarsa ta rakasa tanai
masa shagwaba ya manna mata kiss ya ja
motarsa ya bar gidan, ta sauke ajiyar
xuciyan jin ddiyau dae ya manta shegiyar
gaba daya, ta koma cikin gida murna fal
cikinta, tana shiga daki ta fito da kullin
maganin da aka basu su sa ma Inteesar a
ruwan sha ta tsura ma maganin ido tana
murmushi,dukiya fa knn a hannunta, ruwan
fridge ta kwashe gaba daya ta bar guda
biyu ta xuxxuba maganin cikisnn ta rufe
fridge din ta koma sama, ta lura kasa
Inteesar ke saukowa shan ruwa bbu ruwa a
dakinta kuma bata ga alamar an siyo ba,
tana ta kwance a daki tana jiran jin
saukowar Inteesar amma shiru, ita ko tana
kwance daki ta rasa inda xata sa ranta sae
juye juye take ga yunwar da take ji tun safe
ta gane Aliyu ya bar gidan hkn yasa ta daure
ta mike ta sa ma kofar ta key, kishin ruwa
duk yabi ya ishetagashi ba karfin sauka
kasa, da kyar ta rarrafa ta shiga bathroom
ta bude tap ta sha ruwa ta dawo tayi
kwanciyarta kan tiles. Washegari ma abinda
ya faru knn Aliyu bae shigo ya ga halin da
take ciki ba ya bar gidan da sassafe, duk da
jiya don ita ya dawoda wuri amma safeena
ta gusar masa da hankalinsa ya manta me
ya dawo da shi, ganin yunwa na neman yi
mata lahani yasa ta dinga daurewa tana
hada tea a nn dakinta da ruwan sanyita sha,
shima tana sha ta amayo, duk ta kara
xabgewa bata da aiki sae na kuka ita daya a
daki, wani lkcn sae taji kmr ta dauki waya ta
kira inna kawae sae ta fasa don bata ga
amfanin kiran ba don rabuwa kawae take
son yi da cikin, ita safeena bbu abinda yafi
daga mata hankali irin yanda taga ruwanta
na nn ajiye ba a taba ba, hkn yasa da
daddare da Aliyu ya dawo ranan tace “anya
kuwa kana shiga duba baiwar Allahn nn
dear, gashi ita bafitowa take ba, na kan
shiga na dubata wllh, amma ba ddewa nake
ba kar ace xan yi mata wani abun ne” Aliyu
ya mike da sauri kmr an tsikaresa yyi hanyar
stairs ta bude fridge ta dauka ruwan da
sauri ta bi sa tana cewa “gashi ka kai mata
ruwa naga kmr jiya ruwan dakinta ya kare
na fanfo take sha, ni kuma kar na kai mata
ta xata wani abun ne,” ya karba ya haura
sama ya bude dakin ya shiga rabon da ya
ganta yau kwana uku tun ranar da
sukadawo daga gida, ya karaso gabanta ya
durkusa yana kallonta a hankali yace “ya
jikin fateema, kin daina aman,” tayi tsaki ta
juya abinta, ya bude fridge dinta ya ajiye
mata ruwan yace “me xaki ci,” tayi bnxa da
shi, yyi shiru yana kallonta, ta juya cikin kuka
tana kallonsa tace “wllh tllh idan baka cire
min wnn shegen cikin ba….” bae jira ya
karasa jin maganarta ba ya xuba mata mari,
“don uwarki kika sake min maganar cire
ciki sae nayi mugun saba maki kina ma da
hankali kuwa, to ki je ki cire tunda ke
mahaukaciya ce,” ya mike a fusace ya fice
daga dakin ta bisa da kallo dafe da kuncinta.
Ranar bata yi bacci da daddare ba, kawae
Allah Allah take gari ya waye, gari na
wayewa ya shigo dakin kafin ya tafi aiki, tea
me kauri ya hada mata ya ajiye matagefenta,
snn ya dauko goran ruwan da safeena ta
basa jiya ya ajiye mata gefenta safeena ta
shigo dakin tana murmushi tayi ma Inteesar
ya jiki ko kallonta inteesar bata yi ba suka
fice tare da mijintata rakasa ya shiga mota
ya manna mata kiss snn yaja motar ya bar
gidan, safeena ta koma gidan xuciyarta fari
tasa ganin goran ruwan da ta ba Aliyukusa
da inteesar yau dae xa ayi ta ta kare, ta
shige dakinta tana dariya. Inteesar ta mike
tsaye ta dauki Hijab dinta ta saka, duk irin
wahalan da take sha ko sau daya wanka
bae taba wuce ta da safe ba dole sae ta
daure ta shiga tayi, ta fito tana ganin jiri mai
gadi ya tsaya xae mata maganar bnxa ta
fixgo gate din ta fice abinta ta barsa nn
tsaye, gidan Aneesah ta shiga, tana xaune
tana ba shakur Indomie, tana shigowa ta
kwanta kan kujera tana mayar da numfashi,
Aneesah tace “lah daga ina hka Inteesar
daxun nn nagama xancenki a xuciyata wllh”
Inteesar xata yi magana taji yawu bakin ta
mike da kyar taje bathroom ta xubar
Aneesah tace “A’aah kice oga yyi aiki”
.
Inteesar ta harare Aneesah snn tayi tsaki
tace “ni don Allah taimako naxo kiyi min
Aneesah,” Aneesah tayi dariya tace “to
kawas ina jinki amma cikin nn na baki
wahala gskya, kinga yanda kika rame
kuwa,” Inteesar ta dawo kasa kusa da ita
tace “don Allah don Annabi Aneesah kinsan
inda ake abortion?” Aneesah tayo waje da
ido da mamaki tana kallonta snn tace “kina
da hankali kuwa inteesar,” inteesar ta
jinginar da kanta jikin kujera hawaye ya
cika idonta, Aneesah tace “kinyi shiru,”
inteesar ta share hawayen idonta tace “wllh
xubar da cikin nn xanyi kin dae ji na rantse
in ma xaki gaya min ki gaya min,” Aneesah
ta gyada kai tace “to tashi ki fita a gidana, ni
bana hulda da maras tsoran Allah,” inteesar
ta juya tana kallonta tayi shiru snn ta mike
tayi hanyar fita daga gidan, Aneesah ta bita
da sauri ta kamo hannunta tace “haba
inteesar bafa kiyi kama da jahila ba,” kuka
inteesar ta fashe da tace “baxa ki gane ba
Aneesah wllh bana sonsa bana son cikinsa,
bae damu dani ba sae wahala nke ta sha,”
Aneesah ta xaunar da ita tana kallonta da
tausayi tace “ni na tabbatar maki kina haife
wnn cikin xaki ga tsantsan so gun mijinki,
ni banga rashin son da mijinki yake maki ba
inteesar nafa ga abinda yyi ma kishiyarki
ranar sbda ke, don me xaki walakanta
kyautar da Allah ya baki yar uwa,” inteesar
tayi shiru tana ta sauraran Aneesah tana ta
wa’axinta da nasiha, har ta kai Aya snn
inteesar ta kirkiro murmushi tace “to ngdd
Aneesah, ta dauki shakur tana ta wasa da
shi yana mata dariya, tace “amma a gida
kika haife yaron nn ko Aneesah,” Aneesah
tace “me kika gani,” inteesar tayi yake tace
“aa kawae tambaya ce nayi don ni dae ina
tsoran Haihuwa,” Aneesah tayi dariya tace
“A’a a asibiti na haifesa,” inteesar tace “wani
asibitn?” Aneesah tace “A’a tender care na
haifesa, ai kin san asibitin bbu wani nisa,”
Inteesar tace “A’a” Aneesah ta gaya mata
inda asibitin yake kuma dama abnda kawae
take son ji knn, ta mike xuciyarta fal murna
ta bar gidan.
.
Inteesar na fita daga gidan Aneesah ta
koma gida cike da jin ddi ta shiga dakinta
tana haki kmr warce tayi gudu, ta tabe baki
jin wakan da ke tashi dakin safeena, sae da
ta huta na kusan minti goma snn ta mike ta
dauki purse dinta ta fita daga dakin, dakin
Aliyu ta bude a hankali ta shiga ta bude
drawer din da taji yace Safeena ta bude ta
dauki kudi ranan, taji ta a kulle, tace “na
shiga uku,” ta mike ta fara kalle kallen cikin
dakin kmr xata yi kuka, to ina xata samu
kudin xuwa asibitin ynxu, drawers din
dakin ta dinga bubbudewa gaba daya ko
xata ga kudi amma bbu, duk ta gaji sae haki
take, tuni ta fara kuka tana cewa “Allah ka
taimakeni in ga kudi” ta bude lst bedside
drawer din taga wani babban book an
rubuta my diary a gaba, tayi tsaki ta ajiye ta
mayar da drawern, ta mike ta isa wardrobe
din da yake ajiye kayansa na sawa ta bude
ta lumshe idonta sakamakon wani kamshi
me ddi da ya bugi hancinta, ta gama
bincikenta nn ma ba ta ga kudi ba ta rufe ta
xube kasa ta daura hannu a ka tace
“wayyoo Abbana wllh ni na gaji,” ko ina ta
bude daga taga Allura sae taga magunguna