INTEESAR 3

da dae kayan asibiti kmr tsiya wnn wace
irin jaraba ce, kmr ance ta mike ta daga filo
taga dubu daddaya karkashin filon har da
Atm dinsa ta wara ido tace “wayyo Allahna,”
ta kwashi kudin ta shiga kirgasu da sauri
hannunta na rawa taga dubu sha biyu ne, ta
dan marairaice fuska to xae isheta taje
asibitin ma kuwa, tayi tsaki ta bude purse
dinta ta xuba kudin snn ta juya xata fita
daga dakin taje dakinta ta sha ruwa don
mugun kishi take ji don tsabar son taje ta
cire cikin ta nemi xaxxabin dake tattare da
ita ta rasa sae kasala kawae, har ta isa bakin
kofa ta dawo da sauri tuna baxae rasa ruwa
a dakinsa ba da tayi ta bude fridge dina ta
ko ga ruwa ta dauka ta bude ta sha snn ta
rufe fridge din ta dauki sauran ta fita daga
dakin, duk wnn abinda take safeena bata
sani ba, tana daki kwance tana ta shan kida
cike da jin ddi, jiran jin ihun Inteesar kawae
take a ko wani lkci, Inteesar kam har ta fita
daga gidan rike da purse dinta cikin Hijab,
mai gadi dae bae ce mata kala ba ta bude
gate ta fice abinta sae da ta isa bakin titi
snn ta tsayar da tricycle tayi masa
kwatancan asibitin da Aneesah ta gaya
mata yace ta bada dari biyu, ta shiga tace
mu je. Wasa wasa asibitin shegen nisa ne
da shi, yyi parkin dae dae gate din asibitin
ya juyo yana kallonta yace “mun kawo
Hajiya,” ta fito tana kare ma asibitin da ma
anguwar kallo, ta bude purse ta ciro dubu
daya cikin kudin ta basa kudin ya rage dubu
sha daya, ya bata canjinta ta karasa cikin
asibitin gabanta na faduwa, wnn dae da
ganin asibitin nn ba na talakawa bne, anya
kuwa xasuyi mata abortion a dubu sha daya
kuwa ta dan karyar da kanta abun tausayi,
da Addu’arta ta shiga asibitin, babba ne
ssae ta karasa cikin reception ta xauna
ganin patients dayawa a xaune, ta shiga
kare ma reception din kallo, ta kai kusan
minti talatin a xaune ba a xo kanta ba duk
ta gaji, taji kwanciya kawae take son yi ga
amai dake taso mata, ta daura kanta a cinya
taji kmr ta rusa ihu duk ta rasa ina xata sa
ranta, wata nurse ce ta dafa ta ta dago da
sauri tana kallonta, Nurse din tace “yhur
card nmbr Madam,” inteesar ta shiga kalle
kalle xata yi magana taji yawu ya cika
bakinta, nurse din ta lura da hka ta nuna
mata bayin dake kasan reception ta karasa
ta xubda yawun ta kora ruwa snn ta dawo,
nurse din ta debo vitamin c ta mika mata ta
sa a baki tayi mata gdya ta karba, tana
kallon Nurse din tace “i dnt have a card in
here,” Nurse din tace “to dole sae kin yanki
kati,” Inteesar tayi shiru snn tace “nawa ake
yankan katin,” nurse din tace “family card
dubu biyar, na mutum daya dubu 2 da dari
5,” inteesar tayo waje da ido tana kallonta,
ganin xata bata ma nurse din lkci ga kuma
patients dayawa suna jira yasa tace “to ki
yankar min na mutum daya,” nurse din tace
“ok” snn tayi gaba, a hankali inteesar tace
“na shiga uku, to ai kudin ya kare,” ba ajima
ba nurse din ta fito daga wani dan daki ta
mika mata katin snn wata nurse ta
daddubata ta duba har da weight dinta tayi
rubutu a file tasa nurse ta rakata bayi aka
xuba mata ruwa a kanta don temperature
dinta yyi sama, ita dae binsu kawae take, a
xuciyarta tace ko da yake basu san me ya
kawota ba shiyasa suke bata lkcnsu, ita dae
ynxu likita kawae take son gani, wata nurse
ce ta gwada mata office din doctor din da
xata shiga a sama, tana rike da file dinta ta
haura sama da kyar ta karasa office din tayi
knock.
A hankali Inteesar ta tura kofar bayan an
mata ixinin shigowa office din, cak ta tsaya
daga bakin kofa tana kallon likitar, doctor
din ma ta mike tsaye tana kallon Inteesar da
mamaki tace “fateema,” inteesar ta kirkiro
murmushi gabanta na faduwa ta karaso
office din a sanyaye, ta nuna mata kujera ta
xauna, doctor din tace “daga ina kike hka
fateema, me ya kawo ki nn,” ta rasa karyan
da xata mata, da kyar bakinta na rawa ta
ce”banda lfya ne,” doctor din ta hade rae
tace “shi Aliyun fa,” inteesar ta rasa me xata
ce ga xuciyarta sae tashi yake, likitan ta
dawo kusa da ita tana kallonta ta dago
kanta tana kallon cikin idonta tace “ciki gare
ki fateema,” inteesar tayi shiru bata ce
komai ba, doctor din ta ciro wayarta ranta a
bace ta shiga neman layin Aliyu, da sauri
inteesar ta dakatar da ita gabanta na
faduwa tace “A’a don Allah doctor kar ki
kirasa wllh ya sani kuma yana dubani nice
dai bana son shi ya duba ni, Allah yana kula
dani doctor kawae ni ce bana so, idan yaji
na xo nn xae bata min rae don bae sani ba,”
doctor din tace “haba fateema, to ma don
me xaki fita ba tare da ixinin mijinki ba,
kuma meyasa baki son ya duba ki,” inteesar
ta fashe da kuka tace “wllh ni bana sonsa
doctor,” doctor din ta tsaya da mamaki tana
kallonta snn tace “sbda me fateema, gashi
har rabo ya shigo kice baki son mijinki,”
Inteesar ta sunkuyar da kai tana hawaye,
doctor din tayi shiru tana kallonta, can ta
koma sit dinta ta xauna ta shiga yi mata
nasiha kan cewar ta rungumi mijinta ta cire
duk wani rashin sonsa a ranta, ita dae bata
ce komai ba sae kukan da take a hankali,
Doctor din tace “yyi maki scan ne?” inteesar
ta girgixa kanta tace “A’a nace masa bana
so,” doctor din ta harareta tace “to karki
sake yi ma mijinki musu baki san aljanarki
na karkashin kafarsa ba,” inteesar ta dan
tabe baki kanta a kasa ba tare da ta bari
doctor din ta lura ba, doctor din ta yagi
wani takarda ta danyi rubuce rubuce snn ta
danna bell wata nurse ta xo da sauri, ta
mika mata takardar tace “scan xa ayi yi mata
sisterna ce,” doctor din ta kalli Inteesar tace
“tashi ki bita,” inteesar ta mike a sanyaye ta
bi bayan nurse din har sun kai bakin kofa ta
juya tana kallon doctor Maryam tace “don
Allah doctor kar ki kirasa wlh xae bata min
rae,”doctorn tayi murmushi tace “baxan
kirasa ba ki kwantar da hankalinki” bayan
kusan awa daya inteesar da nurse din suka
shigo da sakamakon a hannun nurse din, ta
mika ma doctor maryam ta fita, doctorn ta
bude takardar tana dubawa, inteesar dae
kallonta kawae take ranta a hade, ba shiri
taga doctor maryam ta mike tsaye da sauri
tace “waw Ahmdllh, twins 4 Aliyu, Allahu
akbar,” ta rungume inteesar tace “Allah ya
raba lfya kanwata, kinga ma yan biyu ne”
inteesar ta sunkuyar da kanta da sauri
hawaye ya cika idonta, hka doctorn ta dinga
mata surutu cike da murna kmr ita xata
haifa ma cikin, ita dae bata ce mata komai
ba daga karshe ta hada mata magunguna,
da allurori a office dinta ta xuba mata su a
leda da takardar scan din tace “to maxa
tashi ki koma gida sae ki kai masa takardar
scan din, sae ya fada maki yanda xaki sha
magungunan yyi maki alluran,” Inteesar ta
mike da sauri kmr jira take tace “ngdd ssae
doctor,” har gate doctorn ta rakota snn tayi
mata sallama bayan ta kara jaddada mata ta
hakura ta xauna da mijinta, ita dae inteesar
sae gdya take mata har ta koma ciki snn ta
kama hanyar titi inda xata samu tricycle, a
cikin wani flower ta watsar da magungun
da injectns din dake cikin ledar dake
hannunta ta bar takardar scan din kawae, ta
isa titi xuciyarta na suya, ta tsayar da tricycle
tace “malam don Allah idan kasan ko wani
asibiti a nn wajajen ka kai ni,” yace “to
shigo muje akwae wani can gaba,” ta shiga
da sauri ya ja machine din suka kama
hanyar asibitin, ae ko yan goma ne a cikinta
ba yan biyu ba sae ta xubar da su yau wllh
.
Wani babban Asibitin aka kuma kawota, ta
fito tana kare ma asibitin kallo snn tace