INTEESAR 3

magungunanta ta gani kan gadon kusa da
shi, ta yo waje da ido a tsorace da ganinta
kasan bata da gskya, ya tsaya kallonta yace
“me ya faru,” sanin cewa xae juya ya kalli
inda take kallo ne yasa ta tofar da yawun
bakinta nn bakin kofa da sauri ta fasa wani
raxanannen ihu tana tsalle, har ya juya ya
kalli ledan kan gadon kuwa ya mike da sauri
ya karasa kusa da ita a rude ya riketa yana
tambayarta lfya, jikinta ya dau rawa ta fashe
masa da kuka tace “wayyoo cikina ke min
ciwo har da kaina,” da mugun damuwa
yace “cikinki kuma” ta gyada masa kai
jikinta na ci gaba da rawa, ya daga ta xae
kwantar da ita kan gadonta ta fasa masa
ihu a gigice tace “wayyoo ni ka kai ni
dakinka, xafi nake ji,” duk ta rikitasa ya
dauketa da sauri ya bude dakin ya fita, sae
kuka kuwa take jikinta na rawa, safeena
dake fitowa daga dakinta knn ta bisuda
kallo xuciyarta na bugawa “kai wayyoo ddi,
ta sha ruwan,” ko kallonta Aliyu bae yi ba, ita
ko inteesar sae kuka take kmrgske, ya
kwantar da ita kan gado bayan ya kunna AC
yana kallonta yace “ina kika ce ke maki
ciwo,” a hankali tace “ya daina, wanka
kawae xanyi da ruwan xafi,” ya shiga
bayinsa da sauri ya hada mata ruwan, yana
shiga ta mike har tana tuntube ta fice daga
dakin da sauri suka kusan cikin karo da
safeena dake labe bakin kofa, safeena ta
koma baya a tsorace tayi xaton Aliyu ne,
inteesar ta watsa mata harara tace “an dae
ji kunya,” tayi tsaki ta bude kofar dakinta da
sauri ta kwashe magungunan kan gadon ta
xuba su cikin handbag dinta jikinta na
rawa, tana xuba su ta fice da sauri taga
safeena tsaye har lkcn kwakwalwarta a
jagule to ko bashi tasha bane, inteesar ta
wuce ta ta shige dakin Aliyu, dae dae nn ya
fito ya tsaya kallonta da mamaki, xae yi
magana ta rigasa “ruwa, amm ruwa naje
sha,” yana mata mugun kallo yace “get out,”
ta yi kmr xata yi kuka ya daka mata tsawa
“ni kike raina ma hankali ko, fitar min a daki
munafuka,” tayi tsaki ta juya ta fice daga
dakin tare da sauke ajiyar xuciya. Bata samu
shan maganin ba ranar da daddare har tayi
bacci don ido Aliyu ya sa mata, washegari
sunday yana gida yana xaune dakinsa
na’ura gabansa, safeena ko na daki kwance
abun duniya ya isheta, inteesar ta gama duk
abinda xata yi da kyar don xaxxabi ne ssae
tare da ita, ta rufe dakinta da makulli ta ciro
maganin da likitan ya bata jiya ta debo ruwa
a bathroom don har lkcn ba ruwa a dakinta,
ta xauna kusa da gado, ta fiffito da
magungunan daga kwalayensu ta daddauki
yanda yace mata, ta tsura ma kwayoyi
shiddan dake hannunta ido, ita bata ma
taba ganin irinsu ba, ta rumtse idonta ta
xuba su a bakinta ta kora da ruwa da sauri
ta hadiye su.
TAMMAT ALHAMDULILLAHI.
[ad_2]