INTEESAR 3

maka ba wlh mugu kawae,” juyawa yyi ya
fice daga dakin da sauri ta mike jikinta na
rawa ta shige bathroom ta rufe da key.
Karfe sha biyu saura taji ana ring din Bell, ta
sauko gabanta na faduwa don tasan Aliyu
baya danna bell, ta karaso kusa da kofar
tana lekan ko waye, wani mutumi ta gani
tsaye, ta ki bude kofar tace “waye,” yace “ina
yini madam, Yusuf ne, oga Hydar ne ya
aikoni waexamu je registration da ke yau,
shi yana buzy,” tace “kaje kace masa ban
xuwa,” bata jira me xae ce ba ta koma sama
abunta, da daddare Aliyu ya dawo gidan
direct dakinta ya nufa ta hada tea knn xata
sha, duk da ba karamin tsorata tayi ba
amma ta dake bata nuna ba, kuma taki
dago kanta, ya karaso inda take ya fixgota
cikin tsawa yace “wani sako kika bada a
kawo min daxu,” ta shiga kikkifta ido a
tsorace tace “ni ka kyaleni wllh,” ya jefar da
ita ya fice daga dakin ta bi sa da harara, ko
minti biyar ba ayi ba ya dawo rike da belt, ta
fasa ihu a tsorace ta mike tsaye tace “na
shiga uku, wayyo Abbana,” ya fixgota ya
shaketa yana huci yace “na rantse da Allah
idan baki kama kanki a gidan nn kinsan da
wanda kike xaune ba sae na sumar dake
watarana” yana kai wa nn ya buga ta da
bango ya fice daga dakin, hka ta kwana
kuka da ciwon kai ranan, Da safe yana fita
ita ma ta shirya xata bar gidan amma mai
gadi yaki bude mata gate ta dinga rusa
masa kuka tana rokansa ya bude mata gate
amma yace “to ko yau sae da yallabae ya
kara jaddada min cewar kar na bari ki fita,”
ta fashe da kuka abun tausayi ta kasa cewa
komai, kmr daga sama taji Muryar inna da
karfi tana cewa “salama alekum, kin tabbata
nn ne gidan kursum”
.
Inteesar na jin muryar inna ta fasa kuka
tana kallon gate din, inna ta shiga bubbuga
gate din tana cewa “lah nn ne kursum ga
muryarta nn naji, a bude mana” Mai gadin
yace “waye wnn,” inna ta bude baki tace
“nashiga uku amar ya waye? Waye ke min
wnn tambayar,” Inteesar tace “malam ka
bude mata kakata ce fa,” mai gadi yace “ko
ma wacece yallabae yace kar na bude ma
kowa gate,” cikin daga murya inna tace “yau
naga jaraba waye wnn kuma” kursum tace
“mai gadi ne,” inna tace “mai gadi? To ya ci
ubansa ba a gaya masa ko ni wacece bane
ni da gidan jikokina xae hana ni shiga,”
kursum ta fashe da dariya inna tace “ke ban
san shashanci fa,” sae kuma ta shiga kiran
Inteesar,” cikin kuka inteesar tace “Na’am
inna yaki bude gate din,” a fusace inna tace
“yau ni naga jarababben dan iska gate din
ta ubanka ce ko ko, kaji min mutum,” dariya
ma abun yaba mai gadin inna tace “shi
Aliyun yana ina,” Inteesar tace “oho nima
ban sani ba,” inna ta shiga buga gatedin da
karfi tana duddura ma mai gadi xagi,shi dae
yana xaune sae shan rakensa yake inteesar
tace “wae kai wani irin mutum ne baka jin
ka bude mata gate ne ka maida mutane
mahaukata,” inna tace “ki rabu da shege,
kursum maxa kira min Bukar,” kursum ta
karbi wayar ta kira Abba ta mika mata tace
“Bukar Bukar gani gidan Aliyu wani kato
yahanani shiga, na kai awa biyu tsaye cikin
rana Bukar,” Abba yyi murmushi yace “to ae
umarnin da aka basa knn baaba ku koma
gida kawae,” cikin kuka inna tace “kambu,
Al’quran bbu inda xani sae ya bude min
gate don uwarsa,” nn ta shiga jijjiga gate
din kmr xata cire tana tsine ma mai gadi,
maigadi yyi tsaki ya ciro dan wayansa ya
kira Aliyu “oga ga wata tsohuwa nn ta xo ta
cika anguwa wae sae an bude mata gate,”
Aliyu yyi dariya yace “karka kuskura,” snn ya
katse kiran mai gadi ya mike yana fito ya
shige dakinsa. Inteesar taji kmr ta shakesa
ta karasa kusa da gate din tace “inna Aliyun
ne fa yace kar ya bude maku wlh, ku tafi
gida kawae ba budewa ae yi ba,” inna ta yo
waje da ido tace “me? To wllh bbu inda xani
ina nn har sae an bude min gate din,” cikin
kuka take maganar, kursum kuwa sae
dariya take har da faduwa,inna ta nemi
dakali ta xauna tana sharbe majina, tace “ae
yau bbu abinda xae hanani shiga gidan nn
wllh sae na shiga” Inteesar ta gaji da
tsayuwa ta shiga, ciki lkci lkci ta kan fito ta
tarar suna nn, sae tausayin innan ya cika ta
taji kmr ta dinga ihu don takaici lallai Aliyu
ya cika mara mutunci, duk irin yanda ta
lallaba inna ta tafi kin wucewa inna tayi, har
aka kira azahar inna na nn xaune kursum ta
gaji ta kama hanyar gida inna ta rakata da
xagi, shegiya kawae ni ba mutum bace
kuma ban san ciwon jikina ba sae ke ko,
ganin har kusan karfe hudu inna na nn a
xaune yasa inteesar ta fito da ruwa tana
kallon mai gadi tace “don Allah don annabi
malam ka dan bude gate din sae ka mika
mata ruwan nn wllh tsohuwace,” da kamr
baxae tashi ba sae kuma ya mike ya karbi
ruwan da take mika masa ya dan bude gate
din yana lekota yace “ga ruwa kaka,” ta
mike tsaye tana kallonsa da shirin masifa ko
me ta tuna sae kuma tafasa, ta karaso kusa
da gate din kmr xata karbi ruwan ta
bangajesa da karfi ta shige gidan da gudu.
Me inteesar xata yi idan ba dariya ba, ta
durkushe kasa ta dinga dariya kmr cikinta
xae kulle, mai gadin ya bude baki yana
kallon inna dake huci tace “don buhun
ubanka ni xaka hana shiga gidan jikokina,
mugu katon bnxa kawae, wllh baka sameni
lkcn ina Rahmatu ba da yau bbu ubanda xae
hanani faffala maka mari dan iska,”
Inna na kai wa Aya ta yi hanyar garden kmr
xata tashi sama tana huci Inteesar ta bi ta
da sauri tana ci gaba da dariya tace “ba nn
bane hanyar shiga inna,” Mai gadin ya sauke
ajiyar xuciya yana bin inna da kallo, bae taba
ganin tsohuwa da karfi hka ba, har suka
shiga falo Inteesar bata daina dariyar da
take ba inna ta hade rae tace “ke ni fa ban
san tsiya meye abun dariya a nn, wlkncin da
katon can yyi min ko me” kan Inteesar tace
komai inna ta rike haba baki bude
tace”A’aah bene kuma cikin gida ni
Rahmatu naga abinda ya ishe ni,” Inteesar
tace “kuma shi xaki hau muje daki ba,” inna
tace “ni ina xan iya,” inteesar na dariya ta ja
ta suka haura sama tana mitan kafafunta na
ciwo, sae da inna ta fara sllh snn Inteesar ta
kawo mata abincin da ta dafa kmr dae
tasan inna xata shigo gidan daga karshe,
inna aka xauna aka bubbude kafa tana ci
tana xagin mai gadi da Aliyu, sae da inna ta
gama cika cikinta snn Inteesar ta xaga da
ita ko ina na gidan har dakin Aliyu sae da
suka shiga, inna sae washe hakora take
tace “ashe dae xan ga wnn rana da xan
taho gidan jikokina ni rahmatu, ae Bukar
bae yi ba, ni ban san meyasa yake min hka
ba gidan jikokina ma ya hanani xuwa sae
da ixininsa sae kace ubana, daba dan hka
ba ae sae na dawo nn ma gaba daya gani
ga ku, ni dae ynxu ‘ya yana nake son gani
duk da bamu san gawan fari ba, xan so
naga yayanku da Aliyu,” Inteesar dae bata ce
komai ba a xuciyarta tace Allah shi kyauta
na Haihu da Aliyu, inna ta juya tana kare
mata kallo tace “wae ni ya naji shiru ne har
ynxu Inteesar ga fadila can da ciki, anya
kuwa bakwa shan abu yaran nn, barin ke,
nafi tausaya maki don shegen yaron nn kai
ki xae yi ya baro ki” Inteesar ta hade rae tayi
gaba ta barta nn tsaye, inna ta bita a baya
tana cewa “to ni dae banga abun bata rae
ba a nn daga fadan gskya” suna komawa
daki inna ta xauna ta hade rae tana kallon
Inteesar tace “ki maxa ki hada kayanki tafiya
na xo yi dake dama, wae ashe gantalallen
yaron nn aure xae yi ban sani ba,” sae kuma
ta fashe da kuka tace “sakayyar da xae
mana kenn, wllh sae ya baki takardar ki ba
rasa masoya kika yi ba,” Inteesar tayi shiru
da mamaki tana kallon inna kmr ba ita ba