INTEESAR 3

tace “ae ba dan jiya dare yyi ba da baxa ku
tashi ku tarar dani gidan nn ba, inteesar
bata tanka ta ba ta dauki Hijab ta sa ta tada
slh, ko da ta idar ta gaida inna maimakon ta
amsa sae ca tayi “ni tashi ki hada min kayan
karyawa nayi na bar gidan nn tun kan na
fara ganin abinda yafi karfina,” inteesar xata
yi magana Aliyu ya bude kofa ya shigo dakin
yana kallon inna, daga tsayen yace “an tashi
lfya,” inna ta galla masa harara tace “ban
tashi ba, hka kke gaida uwarka,” Aliyu yace
“har gida xan xo na rama abinda kika min
daxu wllh,” Inteesar ta mike ta fita daga
dakin ya bi ta da kallo ya tabe baki yana
kallon inna yace “yar nn bakuyi mata trainin
me kyau ba a gida, bata san ta tashi ta gaida
mutum ba da safe,” inna tace “ae gun
uwarka ta gaji hka, wae ni Aliyu ya naji
shiru har ynxu ban ganta da ciki ba,” Aliyu
yace “ita ce tace bata son Haihuwa,shine ma
yasa xan auro warce ke son Haihuwan”
inna tayo waje da ido tace “kmr yaya,” xae yi
magana wayar inna ta cika daki da ruri ta
daga da sauri tare da cewa “salama
alekum,” ya mike ya fice daga dakin, kitchen
ya sameta tana hada ma inna break, ya
karaso kusa da ita yana kallonta yace “ke
gidanku ba a koya maki idan kin tashi da
safe kiyi gaisuwa ba ko,” ta tabe baki bata
ko kallesa ba bare ta basa amsa, kmr xae yi
magana sae kuma ya fasa ya matsa dab da
ita yace “gobe xa a xo ayi ma amaryata
danki, kuma tace dakin da kike ciki take so
don hka nake so kije ki fara fiffito da
kayayyakin dakin ki xaba wani dakin ki
xuba su ciki,” tayi yar dariya bata ce komai
ba, yace “hope dats clear,” tayi masa wani
mugun kallo ta juya xata fita daga kitchen
din ya kamo hannunta.
Inna na xaune a daki tana kallo bayan ta ci
tayi kat, inteesar kuwa na wanke Bathroom
Aliyu ya shigo yana kallon inna yace “inna xo
mu je indan xaga dake gari mana tunda ina
gida yau,” inna na kallonsa da mamaki don
daxun nn suka gama fada tace “kai da
gske? Amma fa ba tukin nan taka ta
ganganci xaka yi dani ba fa,” yace “wllh a
nutse xan tuka ki,” ta mike da sauri tana
gyara daurin dankwalinta tace “to ita
Inteesar ita kadae xa mu bari gida, wae ma
to wa xae je ya kwaso min kayana ne,” yace
“ehh xan kira Zainab ta kwaso maki, inna
tace “Inteesar ke baxa ki je bane, Aliyu yace
“ki dae gaya mata me xata girka maki kafin
mu dawo,” inna tace “to kiyi min tuwan
semo da miyar kubewa,” inteesar ta fito
tana kallonsu, ko kallonta inna bata yi ba
tace “sae mun dawo,” ta fice Aliyu ya juya ya
galla mata harara snn ya fice shima, mai
gadi na bude masu gate tace “yauwa Aliyu
wnn ba mutumin arxiki bne jiya kokuwa ya
dinga yi dani ka koresa,” yace “to inna,”
suna ta tafiya suna hira inna sae kyalkyale
dariya take duk da Aliyu bae ga abun dariya
ba don hiran ma ba ganewa yake ba, tafiyar
kusan minti talatin suka yi snn yyi parkin
yana kallon inna yace “to fito in siya maki
nama,” inna ta fito da sauri tace “yauwa dan
albarka” tana kare ma inda suke kallo
bakinta a wangale, can sae fara’ar dake
fuskarta ya bace tace “nn ae anguwansu
farida ne Aliyu,” yace “yauwa ashe kin gane,
kuma nasan xaki iya gane gida daga nn
kina shan kwana xa ki ga gate, in kin koma
sae kice da Haisam ya siya maki naman don
ban fito da kudi ba” yana kai wa nn ya shige
motarsa yyi gaba inna ta fasa ihu tana salati,
mutanen dake gun suka taho da sauri suna
tambayar lfya. Inteesar na kwance da
daddare ya shigo gidan ita dae tasan bbu
maganar dawowan inna gidan, tana ji ya
bude dakinsa ya shiga, ta mike xaune ta
rafka tagumi tana naxarin abinda yace mata
daxu da safe ita har lkcn ta kasa gaskata
wae Aliyu aure xae yi nn da kwana hudu,
tunanin hkn yasa hawaye ya cika idonta,
tana nn xaune har kusan karfe daya ganin
bacci ya kaurace mata yasa ta mike a
sanyaye ta shiga bathroom ta dauro alwala
ta fito ta fara sllhn dare. Da safe tana gaban
madubi tana gyara fuskarta ya shigo dakin,
1st tym in history Aliyu ya shigo mata daki
da sallama ta amsa ba tare da ta kallesa ba
yana kallonta bbu yabo bbu fallasa yace
“kina jina, ki kama kanki safeenah xa su xo
gidan nn anjima don nasan baki da kunya,
infact bance ki fita ba ma,” tace “akan me
baxan fita ba? Wllh bbu abinda xae hanani
fita,” yace “shknn, ni kuma xan ce mata duk
abinda kika yi mata tayi min maganinki” ya
juya ya fice daga dakin bayan kmr minti
goma ya dawo yana kallonta yace “kinga
dakina yyi kama da dakin kaya, c’mon kin
wuce kin dauke min kayanki da kika ajiye
min a ciki ko sae na bata maki rae,” xata ce
wani kaya sae ta tuna kayan baccinta dake
dakinsa ta mike fuskarta daure ta fita tayi
hanyar dakin ya bita a baya tana shiga
dakinsa ya jawo kofan yasa key, ta juya da
sauri tana kallon kofar ta shiga bugawa
tana cewa “meye hka,” yace “hka xaki tsaya
har sae na dawo,” ya rufe nata dakin ma da
key snn ya fice ya bar gidan, kuka ta fashe
da ta durkushe tana kare ma dakin kallo,
sae a snn ta lura da kayan tea da cakes din
da ya ajiye mata kan fridge sae plantain
chips, karfe sha biyu taji ana shigowa gidan
da motoci ta mike da sauri don bayan ta
gama cin kukanta ta gaji kwanciya tayi, ta
karasa jikin window taga manyan motoci
shake da kaya har kusan guda uku, wasu
lafiyayyun motoci suka shigo gidan, manyan
mata kusan su goma suka fito suna
daddaga hanci, sae ga wata motar ma ta
shigo safeena da kawayenta suka fito daga
cikin motar tana gwada masu ta inda xa su
bi su shiga gidan, tuni aka fara sassauke
lafiyayyun funitures din da aka shigo da,
Inteesar ta sake labulan a sanyaye ta koma
kan gado tayi kwanciyarta tare da lumshe
idonta da taji na neman kawo kwalla, duk
suka cika gidan da hayaniya wasu na sakin
magana, ana ta shigo da kaya. Ko minti sha
biyar ba ayi da shigowarsu ba Anty Nafeesa
da Zainab suka shigo gidan, suna shiga falo
duk aka juya ana kallonsu, batare da Anty
Nafeesa ta kallesu ba tace Sannunku fa,
Zainab kuwa dama ko kallonsu bata yi ba,
Safeena dake kwance kan kujera da
kawayenta suna ta hira da shewa ta bi su
da wani irin kallon raini hka ma iyayen nata,
cikin daga murya Anty Nafeesa tace “to ina
uwar gida sarautan mata kuma ran gida
take ne,” Zainab tace “ina xata iya da wnn
hayaniyar Anty, kila tana can cikin daki,”
.
Safeenah da ‘yan uwanta suka bi su da kallo
har suka haura sama Anty Nafeesah na
cewa “gskya kam ina xata iya da wnn
hayaniyar,” wayar Zainab yyi ring ta duba ta
ga ya Aliyu, tace “ashe dae ya Aliyu na da
nmbrna,” ta daga yace “ki fito waje ki
karbar maku makulli,” tace “na me,” yace
“ban sani ba snn ya katse kiran” ta kalli Anty
Nafeesa dake buga kofar inteesar tana
kiranta tace “wae yaya naje na karba makulli
a waje,” Anty Nafeesa tace “na me, ko tare
suka fita da Inteesar din ne,” Zainab tace
“kila, ina xuwa na karbo keyn,” ta fice da
sauri, yana cikin mota yana jiranta ta karasa
ya mika mata keyn dakinsa da na Inteesar,
tace “to ina inteesar din,” yace “in kun bude
xa ku gani,” ya ja motarsa yyi gaba, ta tabe
baki ta koma cikin gidan, dakin Inteesar
suka fara budewa bbu kowa ciki, snn suka
bude nasa, tana xaune ta hade kai da
gwiwa, suka karaso cikin dakin Anty
Nafeesah tace “amma Aliyu dan rainin wayo
ne kulle ki yyi a daki don ya isa,” Zainab ta
dago kanta tana kallonta, kuka take, Anty
Nafeesa ta galla mata harara tace “ban san
shashanci kukan lfya” ita dae bata ce komai
ba ta gaida Anty Nafeesa, Zainab tace “meye