INTEESAR 3

na kuka Inteesar” Anty Nafeesah tace maxa
tashi kije ki gyara fuskarki kiyi kwalliya kar
na bata maki rae ke dae baki gajiya da wnn
shegen kukan naki komai kuka komai kuka,
ita dai bata ce komai ba suka bar dakin
Aliyu Zainab ta kulle suka koma nata dakin,
sae da ta sake wanka snn Anty Nafeesa ta
sa ta gaba ta tsantsara kwalliyanta snn ta
fito mata da wata shaddarta dogon riga
maroon colour ta saka Nafeesa tayi mata
dauri mai kyau, Zainab tace”waw yan matan
yayanmu kin ga yanda kika xama kmr wata
balarabiya,” inteesar ta galla mata hara, ba
karamin kyau tayi ba duk da ta rame ssae,
Anty Nafeesa tace “to akwae abinci ne a
gidan? Don ni yunwa nake ji,” Inteesar tace
“sae da na girka maku,” Anty Nafeesah tace
“to da dae yafi,” ta ce “toAnty suna falo
kuma,” Anty nafeesa tace “to ina ruwanki da
su ae don su ganki da kyau nake son kije
kiyi mana girkin,” ta mike ta dauko mata
takalmikalan shaddar ta ajiye mata snn ta
feshe ta da turare tace “maxa sa ki tafi
indomie kawae xaki girka mana,” Zainab
tayi dariya tana kallon Anty Nafeesa,
Inteesar kam murmushi tayi ta sa takalmin
gabanta na faduwa ta fita xuwa kitchen,
duk suna xaune falon har da safeena kusan
su goma banda wa inda ke ta jere a daki,
Inteesar bata ko kalle inda suke ba a nutse
cikin takunta mai jan hankali ta nufi kitchen
ta bude kofar kitchen din tana yatsine fuska
don duk sun dauki cups sun sha lemo da
shi, ta dan tabe baki ta shiga kitchen din,
duk kawayen safeena suka juya suna kallon
safeena da yanayinta ya sauya lkci daya
xuwa bacin rai tana kallon kofar kitchen din,
inteesar ta kunna gas ta daura ruwa snn ta
fito falon ta shiga kwala ma Zainab kira
cikin wani irin tsiga, da sauri Zainab ta
sauko tana cewa “na’am yan matan
yayanmu wnn kira hka,” inteesar ta galla
mata harara da wasa tace “ban fa son
iskanci indomie nawa kike ga xae isheku,”
Zainab tace ” wani irin tonan asiri ne wnn,
ko ma dae duka nace ae gidan yayana ne nn
bbu uban da ya isa ya hana,” Inteesar tayi
dariya ssae tace “ikon Allah to shigo ki girka
maku kinsan dae ni ba daga nn ba ban gaji
rowa ba kuma duk yanda nace hka xa ayi a
gidan nn bare kice kina tsoran wataran ki
xo…,” a fusace safeena ta mike tana nuna
Inteesar da yatsa tace “ke ki kama kanki kar
ki kaini bango don dukan tsiya xan maki
wllh wllh kuma sae dae mijikinki ya gode
min idan ya dawo,” Zainab ta yo waje da ido
tace “wa xa a duka ni Zainb” Inteesar tayi
dariya tace”tambayan min ita don ni kaina
ban gane inda ta dosa ba,” Safeena ta ciro
wayarta da sauri ta shiga kiran Aliyu, “Aliyu
Aliyu ka ja ma ballagaxar da ka ajiye a gida
kunni wllh ta fita harkata idan ba hka
bakafin na bar gidan nn yau sae na yi mata
kaca kaca, kuma wnn shegiyar kanwartaka
ita ma kaja mata kunne,” Zainab tace “wllh
ni ba shegiya bace sae dae kece shegiya,”
Inteesar ta ja ta suka shiga kitchen suna
dariya, safeena tayi shiru tana sauraran
abinda Aliyu ke ce mata tana bubbuga kafa,
sun gama dafa indomien knn xasu wuce
samaAliyu ya shigo gidan, ba karamin
tsorata inteesar tayi ba tayi hanyar stairs ba
tare da ta kallesa ba, Zainab tace “ke kar ki
bada kanki mana ki tsaya ae Anty nafeesa
na nn,” Aliyu na kallonta yace “ke xo nn,” ta
galla masa harara tace “nayi maka me,”
karasowa kusa da ita yyi ta dake xuciyarta
na bugawa, duk yan falon suka xuba masu
na mujiya, ita kanta Zainab karfin hali tayi ta
tsaya, Safeena kosae taunar cingam take
tana jujjuya ido xuciyarta fal murna ita nn
kawayenta suka yanda ta isa da Aliyu, yana
isa kusa da inteesar ya kama hannunta ta
fixge tace “da’alla malam kyaleni,” ya tsaya
kallonta da mamaki bae ce komai ba,ya juya
yana kallon Zainab yace “je dauko mata
mayafinta ko ki bata naki,” Zanab ta cire
mayafinta ta mika ma Inteesar taki karba,
shi ya karba snn ya sureta kmr wata bby
suka fita daga gida
.
Inteesar ta tsorata ssae murya can kasa tace
“don Allah kayi hakuri ka saukeni wllh ita ce
ta fara,”Safeena kam binsu tayi da kallo da
mugun mamaki don tsabar mamaki kasa
rufe bakinta dake bude tayi, ita nn jira take
taga ya rufe ta da duka, Zainab kuwa dariya
tayi tace “kai irin wnn soyayya hka, ko me
Inteesar ke ma yayana hka oho,” ta haura
sama tana ci gaba da dariya, bayan mota ya
jefata snn ya xaga ya shiga motar ya ja ta,
ita ko kallonsa kawae take gabanta na
faduwa ko ina xae kai ta, sun yitafiya ssae
snn taga yyi horn aka bude gate ya shiga yyi
parkin, ya bude mata kofa yace “fito kar na
mareki,” ta fito tana kare ma wajen kalloduk
da tasan inda ya kawota don ta taba xuwa,
lallai ma Aliyu asibiti ya kawota, yyi gaba
tana biye da shi a baya kmr xata yi kuka,
nurses duksuka kama kansu ganinsa, suka
bi inteesar da kallo suna masu sannu da
xuwa, bae ko kallesuba sae ita ce ta
gaishesu ganin yanda suke kallonta, can last
flour office dinsa yake kusa dana aminin
dad dinsa don shine mai asibitin wato
dad din Sadeeq, ya bude office dinsa ya
shiga, ganin taki shigowa yasa ya fixgota, ta
shiga karema office din nasa kallo, ba
karamin haduwa yyi ba kmr ba office ba ita
fa bata taba gskata Aliyuna aiki ba duk da
tasan da sassafe yake barin gida ya dawo
late, ya shiga dakin da ke cikin office din ita
dae tana nn tsaye har ya fito bayan kmr
minti goma sanye da kayan surgery, green
colour yana kkrin sa hand gloves alamar
theatre xae shiga, ya galla mata harara yace
“kada Allah yasa ki xauna kuma idan lkcn
sllh yyi kar kiyi,” snn ya fice, tayi tsaki kmr
xata yi kuka ta xauna kan kujera tana kare
ma office din kallo, ko minti goma ba ayi ba
da fitarsa wata nurse ta shigo rike da abinci
a rufe da lemo ta ajiye mata tace “sannu
madam,” snn ta fita. Hka inteesar ta yi ta
xama kamar gantalalliya a office kmr tayi
kuka, abincin da aka kawo mata ma kin ci
tayi, ta gaji da xama ta kwanta kan gadon
da ake duba pregnant women tayi
kwanciyarta sae bacci, ko da ta farka taga
biyar ya kusa ita da ta kwanta tun kusan
daya da rabi, bata damu ba don dama bata
sllh, ta bude abinci daxu ta yatsine fuska ta
rufe, aka bude kofa wasu nurse biyu suka
shigo da jarirae har biyu suka yi ma inteesar
sannu, snn suka daura su kan gadon yara
dake office din daya ta kunna wani wuta
mai haske dae dae fuskarsu snn suka fita,
inteesar ta wara ido tana kallon yaran
kyawawa dasu, ta karasa kusa dasu da
mamaki tana kallonsu tace “yan biyu,” a
hankali dayan ya shiga kuka yana tsotsan
hannunsa dayan ma ya karbe taji kmr ta
daukesu don tana bala’in son yara, ta rasa
yanda xata yi dukta rude ganinsu tayi can
tayi nn, aka bude kofar dakin Aliyu ya shigo
ta juya da sauri tace “ya Aliyu yan biyu ne?”
ya cire abun bakinsa yace “ehh” ba tare da
tasani ba tace “waw a ina kukasamo su” ya
karaso kusa da gadon yana kallonsu yace
“daxun aka cirosu daga cikin mamansu,
bata farfado ba har ynxu ma” inteesar ta
juya da sauri tana kallonsa kmr xata yi kuka
tace “theatre aka mata,” xae yi magana daya
yaron ya tsala ihu tace “wayyo ya Aliyu in
daukeshi,” ya harareta yace “basu da
lafiyasuma,” tayi shiru tana kallonsu kmr
xata yi kuka.Ya dauki dayan a hankali ya
mika mata yana kallonta.
.
A hankali Inteesar ta sa hannu ta karbi bbyn
da yake mika mata tana murmushi, tace “ya
Aliyu ni ina son twins ssae” yana kallonta
yace “kina sonki haifi twins knn,” da sauri
tana kallonsa tace “eh mana ina so,” ganin
irin kallon da yake mata yana murmushi