INTEESAR Complete Hausa Novel (1).

Na fara gaida momyn mana,” da sauri tace “a’a kadai je gun inna idan xaka tafi sae ku gaisa,”
yace ok
sannan yayi sashin inna.
Tana isa kofan parlonsu sae da tayi kusan minti biyar sannan ta shiga,
momy da ihsaan na cin abinci, ta nemi gefe ta rakube, momy ta harareta bata ce komai ba.
A haka suka gama cin abinsu. momy taje tama ihsaan wanka, ita dae tana nan a bakin kofa
A xaune. Xainab ta shigo da sallama tace “ke yar walakanci ce pa yarinyar nan, shine xaki bar
bawan Allah tun daxu yana jiranki,” ta mike da sauri tace “bari nayi wanka na manta ne,”
sannan ta shige bathroom tana satan kallon momy dake shafawa kanwar tata powder. Ta saka
kayan barcinta sannan ta dora dogon hijab har kasa ta fito, ta dubi momy tace “ina xuwa momy,”
ko kallonta ma bata yi ba ta fice a sanyaye, ko me inna ta tsara mata oho. Tana isa sashin inna
ta nemi gefe ta tsaya sannan ta fara kiransa, bugu daya ya dauka tace “ka fito ya faruuq ina
nan waje,” yace “baxaki shigo…..” da sauri ta katse sa ta hanyar cewa “aa ka dai fito ina jiranka
sannan ta kashe wayan” ya dubi inna yace “inna ni xan tafi sai wni lkcn,” aa to ina intisaar
dinm baxa ta xo bane, yace “aa tana nan waje tana jirana.
Yana fitowa ya kalleta yayi murmushi yace “sae yanxu?” bata ce komai ba sae gyada
Masa kai da tayi, sae da ya fara shiga suka gaisa da momy sannan ta rakosa gate, ya dubeta yayi
Yar dariya yace “me ya hadaki da innar taki baki San shiga wajenta?” tayi yake tace “aiki xata
sani ne shi yasa” yyi dariya yana kallonta yace “ke dae fadi gaskiya kanwata,” ta kauda kai bata ce
komai ba sae hmm. To bara na wuce kar Abbanki yaxo ya same mu a nan ko?” da sauri tace
“wa?”
ya kashe mata ido yace “Aliyu mana” tace
“uhum kaga sai da safe ya faruuq yau ba hira kake san min ba” yayi dariya yace “dama ae wuce wa
Xanyi bayan kinsan kin wa inna laifi xaki turani can” bata ce komai ba sai murmushin da tayi, ya
Ciro kudi mai yawa yace taba ihsaan, don yasan ita ba karba xata yi ba, shima din da kyar ta
Karba, suka yi sallamah ya wuce, sannan tayi
sashinsu.
Tun faruwar abin suke wasar ‘yar buya da inna, yau dae kam har dakinsu inna taxo ta
sameta, tayi mata tatas, ita dariya ma abun ya bata, can dae ganin ba kyaleta inna xatayi ba tace “to
naga dae inna ba sharri nayi……” dundun da inna ta kai mata ne yasa ta fashe da dariya, tace
“kai ni inna ki kyaleni, haka kawae ban ji ba ban gani ba ya Aliyu ya min duka,” da kyar inna ta kalleta
Ta bar sashin nasu, momy dae bata ce masu komai ba, sai gashi da daddare wae xata wajen
inna, momy tace “amma baki da kunya wallahi” tayi dariya tace “to momy ae dae inna ta ce.”
A hanya suka hadu da xainab, ta bude baki tace yau kuma wajen inna xa a? Har an manta… Duka ta kai
mata ta bar wajen da sauri, xainab ta bita ita ma tana cewa “tab ae wllh sae na rama” da
sauri ta bude kofar palon ta afka ciki tana dariya,
Inna tace “lafiya ke da wa?” ta juya da sauri xatayi magana sae kuma tayi shiru ganin Aliyu
xaune a parlon yana cin abinci… Xainab ta shigo ta da’da mata duka ita ma sannan tace “na rama”
intisaar dae bata ko kalleta ba sae kame-kamen da ta fara yi, inna tace “ku dae ban san randa
xaku girma ba,” Aliyu ya mike yayi tsaki ya dube
xainab yace “get out kar na fasa maki kai,” ta harare sa
tace “saboda kan nawa……” da gudu ta fice ganin ya yo kanta, ae intisaar na ganin haka ita ma
ta fice a guje, inna tace “kai wallahi mugu ne yaro nan” kofar ya rufe ya dawo yaci gaba da cin
abincinsa yana kallo. Suna xaune a palon inna,
xainab na daddanna mata kafa, intisaar kuwa kallo takeyi sae kursum dake kwance ita ma
tana kallon, inna tace “wannan yaron yace xae xo da bakuwa yau ko me xamu girka mata?”
xainab ta yatsine fuska tace wai Aliyu? Inna tace “eh,” ta tabe baki tace abinda muka dafa a gidan
xamu bata mana. Khadija dake dakin inna tace “kamar ya abinda muka dafa xamu bata? Ita bakuwar
xa a ba wa dafa duka?” xainab tace “shi kuma dafa dukan ba abinci bane ba koh?” khadija tayi
tsaki tace oho. Kar ki min rashin kunya wallahi don xan fasa maki baki, xainab ta fadi tana kokarin
mikewa, inna ta fixgota tace rabu da ita.
kursum je ki ki kira min Zainabu, da gunguninta ta fice wae ita ta gaji. Ba a jima ba momy ta
iso, inna tace “zainabu shinkafa da miya xaki girka min, wae Aliyu xai xo da bakuwa, wannan
gantalallun ‘ya yan sai yawo suke da hankalina.
Ta ce “to inna sannan ta fita.” xainab tace “inna budurwarshi ce?” inna tace kya barni
budurwa,”
kursum tace yau akwae buduri kenan. Nan inna aka tashi aka fara gyare gyare su xainab na
tayi mata dariya kuma suka ki taya ta, intisaar kadai ce ta kama mata aikin don wae bayan
la’asar xasu iso. Momy ta gama girki ta kira xainab taxo ta dauka ta kawo sashin inna. Karfe hudu
da rabi ya shigo parlon da sallama, yana sanye da kananan kaya yayi kyau sosai, inna ta amsa
da fara’arta tana cewa “ina yarinya,” yace tare muke, sannan ya dubi su xainab yace “ku kuma
uban me kuke yi a nan, da sauri intisaar ta shige dakin inna, xainab ma ta bita kursum kadae ce
taki tashi, har yarinyar tayi sallama da siriyar murya, inna ta amsa da karfinta tana wangale baki,
yarinyar ta shigo palon.
… Tana shigowa palon ya nuna mata kujera ta xauna, kursum dake kwance dama tuni ta
mike tana karewa yarinyar kallo, doguwa ce kyakkyawa fara amma da ganinta kasan ta
hada da mai, tana sanye da atamfar Holland an mata shegen riga da skirt dinkin ya dameta sosae,
sannan ta sakale wani dan guntun mayafi kalar atamfar tata yellow a wuya, make up kuwa
har da na hauka don har da su blusher, sae
wani yatsine fuska take, inna dama tuni bakinta a bude yake… Kursum ta dan sa kafa ta bugi
inna alamar ta rufe bakin, ba shiri kuwa ta rufe hade da cewa “ikon Allah! Ina yini? Yarinyar ta
kalle innar tace “sannu baba” tana taunar cingam hade
da karewa parlon kallo, inna tace “yauwa pa” Aliyun kuwa tuni yayi hanyar fridge xae
dauko mata lemo da ruwa. Inna dae ta dage sae kallonta take daga sama xuwa kasa, can sae
ta fashe da dariya, kursum ta rufe fuskarta cikin kujera dan ita ma kar tayi, don shi ke cinta,
daga yarinyar har Aliyu juyawa sukayi suna kallon inna, inna dae ta kasa daena dariya, Aliyu yace “wae
meye haka ne Hajiya?” tayi kokarin shanye dariyar tace “wallahi wani abu na tuna ne” sae kuma
ta kwalo wa xainab kira, “xainab ku xo gu gaisa da Antyn taku mana” xainab dama kamar jira
take tafito da sauri don tuntuni take son lekowa amma tana tsoran kar Aliyu ya ganta, intisaar ma ta
fito don tana san ganin budurwar tashi, gefe suka nema suka xauna, xainab ta kalle yarinyar
sannan ta kalle intisaar da ta sunkuyar da kai
saboda dariyar dake cinta, ita kanta xainab daurewa take amma da tuni ta fashe da ita.
Inna ta sake kwashewa da dariya tana kallonsu xainab din, tace “ku kawo ma antyn taku abinci
“No”a barshi kawae naci a gidanmu kafin na fito,” Aliyu sae kallon inna yake cike da takaici.
Inna ta kara dacewa “to ai bamu ma san sunanki ba” sunanta safeeyna, Aliyu ya taya ta fadi. “ayya
amma wannan telan naki bai maki adalci ba, atamfa har atamfa amma ya tashi yayi maki
dinki kamar ‘yar babyn roba, ae wannan riga taki ko ihsaan jikin ta baxae shigeta ba, amma
wannan anyi dan banxan tela,” inna ta fadi tsakaninta da