INTEESAR Complete Hausa Novel (1).

Allah babu ko dar. Xainab bata san sanda dariyar da take ta hadiyewa ya kubce mata ba, ta
Xube jikin intisaar tana dariya kyal kyal kyal,
intisaar ta daure iya daurewa amma ta kasa rike nata dariyan, nan ita ma ta fashe ta har da
xubewa kasa, kursum ma yi take har da bingirowa daga kan kujera, inna ta bude baki tana kallonsu
da mamaki can ita ma dae ta fashe da dariyar suka taru suka dinga yi, “ni wallahi ca nake xabiya
ce ma ta shigo don hasken yayi yawa, tsoro ma ne ya kamani….” inna ta sake jefo masu. Xainab
har da hawayenta don dariya, intisaar cikin hijab din xainab tashige ta dinga yi kamar wasu
sababbin kamu. Aliyu kam kasa cewa komae yayi sae kallonsu da yake yi daya bayan daya.
Safeenah kam iya kan kulewa tayi shi, ta mike tsam tana kallon Aliyun a nutse tace “Haidar help me
out of dis forsaken house plss” inna tace “lah har xata wuce?, ko me take cewa?” tuni safennar ta
fice daga palon innar da takalminta me kamar tsani,
inna ta tafe hannu tace “ohh yanxu idan ta fadi da tsautsayi ba karyewa xatayi ba da wannan
tsanin dake kafarta” ya mike da sauri duk a rikice yake ya fice ya bita yana kiran sunanta, inna ta bude
baki tace “ikon Allah ko sallamah babu ni Rahmatu” sae kuma ta mike da sauri tayi
bakin kofa tana cewa “Aliyu kakai ta, ta gaida xainabu tana ciki” amma tuni har sun ma isa gate. Ta
dawo tana cewa “inda ranka xaka sha kallo” ta kallesu xainab da har yanxu dariya suke kamar
mahaukata, ta hade rai tace “kai ni fa bana son iskanci dariyar meye haka?” kursum ta mike
tace “na tafi wajen momy ni kam kun ga tafiyata, don yau idan ya Aliyu……” shigowar khadija ce ta sa
tayin shiru, don dama taje wanke gashi, ta dubesu idonnan na ta a xare, tace “kai!! me
kuka yi wa yaya Aliyu? Naji yace wallahi sai ya sumar da mutum daya a gidan nan ” tana fadin haka,
kursum ta bar falon a guje xa ta sashinsu intisaar, nan da nan hawaye ya fara sintiri a idon
intisaar, cikin kuka tace”xainab wallahi ke ce kika…..” wani axababben ihu can ciki ciki
suka ji kursum ta saki… Sallati inna ta saki ta fice a
guje tana cewa shikenan ya kashe ta!!
Intisaar ta daura hannu biyu aka tace wayyoo nashiga uku na lalace, xainab tuni ta firfito da ido cike da
tsoro tace “mun shiga uku!!!”
Aliyu ya kauda kanshi ba tare da yace
mata komai ba, sai da Abba ya bari tayi mai
isarta tayi shiru sannan ya nisa yana duban
Aliyun da kyau yace “ka gya min meye
Matsalar ka a gidan nan, me ke damunka?” kansa kawae
ya sunkuyar ba tare da yace komai ba, “why is it alwayz you in this house? Don me ba a kawo
min karar haisam sae taka? Look.. Wallahi ka sake taba min wani a gidan nan sae nayi mugun saba
maka,
mutumin banxa kawae, tunda ka dawo gidan nan hankalina bae kwanta ba” ya dago kai da
kyar
yana duban Abban nasa yace “to Abba ka
gyawa inna ta fita harkata ta daina min….” shut up!
Abba ya katse sa a fusace, ” dama duk cikin ‘ya yana kai ne baka da manner, amma xanyi maganinka” Abba ya mike ya shige
Bedroom sakamakon kiransa da akayi a waya, sae a sannan Aliyun ya dago ya fara kallonsu daya
bayan daya a palon, ya mike yana duban innar dake kallonsa yace “ba wata tsiya bace idan
na bar maku gidan, amma sae kun sake gani na ”
sannan ya juya xae fice, inna ta mike da sauri tana cewa “to Bukar sae kafito gashi nan ya
hada kaya xae bar gidan wae” ido Aliyu ya xaro yana kallonta, ya koma inda yake da sauri, Abba
ya fito yana kallonsa yace “to tashi ka wuce” bae ce komai ba sae tiles din palon da ya xubawa
ido,
Nan Abba ya dinga masa fada kamar xae ari baki, inna na ta xuga sa, har dae daga karshe
Abba yace ya fice masa a palo, ya mike ransa a bace kamar ya hadiyi xuciya ya bar palon.
Da Yammar ranan intisaar da xainab suna tsakar gida tare da inna dake yi ma ihsaan tsifa take tambayar su
Ko sun ga Aliyu tun daxu don tun bayar barinsa palon abba basu sake ganinsa ba khadija
ma ta kai masa abinci daxu da rana ta gama bubbuga kofarta ta dawo bae bude ba, xaenab tace
“kila tafiyar yayi,” inna ta dan marairaice fuska tace “Allah dae yasa ba tafiya yayi ba….”
Budewar gate din da akayi ne ya sanya su duka suka maida hankalinsu wajen, Aliyun ne ya shigo, yayi
Sashinsa ba tare da ya kalle su ba, sae ga Hajiya ma tashigo rike da jaka, umma na biye da ita a
baya,
sannan khadija ma tashigo da wani jakar a hannunta, da gudu xainab taje ta rungume
uwartata, kursum ma dake kusa da wani flower a xaune taje da gudu ta rungume ummarta
harda kuka, nan da nan inna ta hade rai kamar bata taba dariya ba, intisaar ma ta mike da sauri ta
karbi kayan dake hannun hajiyar tana masu sannu da xuwa, har kasa suka durkusa suka gaida
inna, ta amsa masu can ciki-ciki ba tare da ta kallesu ba, momyn intisaar ma ta fito tayi masu sannu
da xuwa da fara’arta, sannan duka sukayi sashinsu, tsakar gidan ya rage daga inna sae intisaar
da ihsaan, inna ta tabe baki tace “shegu munafukai,
wallahi ni banyi farin ciki da xuwansu ba tsinannuna mutane.” intisaar cike da jin haushi tace “ni
bana son wannan abinda kike yi inna wallahi,”
sannan ta bar mata wajen ta koma sashinsu.
.. Tun ranar da Hajiya da umma suka dawo gidan suka shiga taitayinsu, don ba karamin
tashin hankali suka shiga ba kwanakin baya don a nasu tunanin Alhaji ya sake su ne basu sani
ba.
Kullum da sassafe suke xuwa gaida inna. Abinda basa yi da, har wani shiri suka tsiri yi da
Momy duk da na munafurci ne. Yau kam intisaar na xaune gaban inna tana mata hira, inna tace
“yauwa wannan yaron faruuq yaxo ya sameni jiya da daddare wae yana so ke da xainab kuje
Gaida mahaifiyarsa,” intisaar ta firfito da ido tace
“kai; inna sae kika ce masa me?” eh nace ranar juma’a ya xo ya kai ku, gobe kenan.” intisaar ta hade
Rai tace a’a ni babu inda xanje inna, ke kinga hakan ya dace? Saboda gantali kawae sae na kwashi jiki
Naje gidansu” nan da nan inna ta hade rai tace “to idan yaxo goben karki bisa” intisaar ta mike
Ta fice daga palon tana cewa “ni kam babu inda xanje.” tana komawa sashinsu ta fadi ma
momynta, momy tace “A’a ko da ma xaki je gidan nasu ba yanxu ba sae lokacin da ya dace,” da
yamman ranar faruuq din ya kirata, da kamar baxata dauka ba sae kuma ta dauka don taji
haushinsa sosae, anata tunanin it’s not decent yace xae kai ta gidansu bayan ba ayi
maganar komai ba tukun.
Bayan sun gaisa yake ce mata
inna tayi mata magana, tace “eh amma babu
inda xani” yayi murmushi yace “to shikenan kanwata.” nan dae ya dinga mata hira har yace mata
xae je masallaci don lokacin sallah ya kusa.
Da daddare xainab ta shigo palonso intisaar din tace “ke wae inna tace gobe faruuq xai kai mu wajen
momynsa” intisaar tace “eh amma babu inda xani”
xainab tace saboda me? Ke kinga hakan ya dace?
Intisaar ta tambayeta tana jiran amsa”
Xainab tace “to meye a ciki don munje gaida mamarsa?
Ni dae banga rashin dacewar hakan ba wallahi” intisaar ta mike tace “ke kya iya xuwa, amma ni
baxan je ba.” sannan ta shige daki, xainab ta tabe baki ta yi gaba abinta. Washegarin ranar juma’a
inna ta xo sashinsu wajen karfe sha daya, tana kwance tana kallo, momy kuwa na bedroom, inna
tashigo palon tana cewa “ke wai wace irin yarinya ce xaki bar bawan Allah tun daxu yana jiranki,
wannan wani irin wulkanci ne, na aiko a kiraki yafi sau hamsin sae kice min kina xuwa?” intisaar