INTEESAR Complete Hausa Novel (1).

tabe baki tace “ko ma de sauna nawa ne ni dae
ki rabu dani inna babu inda xani pa” au uwar taki ta hura maki kunne kice min baxaki ba kenan?”
da sauri momy ta fito tace “maxa ki shirya kuje, ni ban hanata ba inna” dolenta ta shirya cikin
atamfa java red colour an mata dinki riga da skirt dama gata fara sosae sae ya amsheta, ta danyi
kwalliya tayi kyau sosai sannan ta dauki hijab dinta har kasa, ta fito palo tace “momy na
tafi” momy tace “ki kama kanki, kuma ku tafi da ihsaan, sannan ki turo min xainab” ae da ita
xamu momy, momy tace “eh nasani,” tana fita tayi sashin su xainab, ta hadu da khadija a
bakin kofa tana dauraye cup, tayi mata wani irin kallon
banxa sannan tace “amma de kinyi batan hanya ne ko?” tayi jim sannan tace momyna ke kiran
xainab. Aliyu ne ya fito yana dubanta yace
“get out” cikin tsawa, xainab ta fito da sauri ita ma ta
shirya cikin wani material ja, tace gani nan xuwa intisaar. Gidan uban wa xaki? Aliyu ya
tambaya yana kallon xainab din, “inna ce xata aike mu gidan kawarta wae,” bae sake cewa komai
ba ya shige ciki kawae, hajiyarsu kuwa tana sashin umma suna tseguminsu da suka saba. A
tare suka je sashin inna da xainab din bayan taje kiran da momy ke mata, ita dinma ta ja mata
kunne ne akan su kula da kansu, ashe faruuq din
ma bae xo ba inna duk tabi ta axalxalesu.
Sha daya da rabi ya shigo gidan, suka gaisa sannan,
inna tace, “amma dei da wuri xaka maido su ko?” yace in’sha Allah inna. Ita dae intisaaar
hade rai ko kallonsa ma bata yi ba. Har bakin kofa ta rakosu sannan ta koma. Sae da suka
hau kan kwalta sannan ya fara hira da xainab, ita dae jinsu kawae takeyi sae wayanta da take ta
daddannawa.
Tafiyar kusan minti talatin sukayi sannan suka iso gidan nasu, yayi horn aka
Bude gate ya shiga yayi park, sannan ya bude masu kofa suka fito, da ganin gidan kasan lallai
mahaifinsa mai kudi ne sosai. Kanwarsa ya kira ta fito,da ganinta baxata wuce su ba, tayi
masu sannu da xuwa tashiga dasu ciki da fara’arta Har palon mahaifiyarsu tayi masu iso,
sannan ta nuna masu kujera su xauna ta cika su da drinks da kayan ciye ciye, ba a dau lokaci ba
mahaifiyar tasu ta shigo palon, suka sauka har kasa suka gaisheta ta amsa da fara’arta
tanai masu sannu da xuwa sannan tace suyi xamansu a kan kujerar, xainab tace nan ma yayi momy,
“a’a don Allah kuyi xamanku nan ba bakon waje bane,” da kyar dai xainab ta xauna kan
Kujerar amma intisaar taki xama, hakan yasa momyn
Ta gano ita ce fateemar. Nan dae ta tambayesu ya mutanan gidan suka amsa mata da duk
Suna lafiya. Ba a jima ba faruuq ya shigo yace xae wuce masallaci tayi masa Allah ya kiyaye hanya
sannan ya wuce yana kallon intisaar amma bata bari sun hada ido ba, sae da suka fara yin
sallah, sannan aka cika su da abinci kusan kala hudu,
Ita dae intisaar ta kasa sakin jikinta ga kunyar momyn da take ji, ganin hakan yasa momyn ta
basu waje tashiga ciki, a tare da kanwarsa ummi suka ci abinci, yarinyar na da kirki sosai,
suka dinga hira kamar da can sun san juna. Karfe biyu faruuq ya shigo gidan ummi ta kai masa
abincinsa dakinsa sannan ta dawo suka ci gaba da hirarsu akan makaranta da sukeyi, sae da
faruuq ya dawo parlon sannan momy ma ta fito, nan dae aka dinga hira amma ban da intisaar da
sae dae tayi murmushi, karfe uku da rabi yace xae maidasu gida saboda traffic, momy tashiga ciki ta
hado masu tsaraba mai yawa tun daga kan atamfa har xuwa sabulai da omo da
jeweries na fashion masu kyau, da after dresses, ummi ma tashiga ta hado masu nata tsarabar na
kayan make-up da turarruka kala-kala, intisaar tace “mun shiga uku xainab, don Allah kice ma
faruuq yace su rage sunyi yawa wllh. Xainab tayi banxa da ita ta dinga godiya kawae, har kusa da
motar suka rakosu sannan ya ja motar suka bar gidan.
Ganin yayi park a wani supermarket ne ya sanya intisaar tace masa “me xamuyi a nan, yace
wannan ba matsalarki bace. Sannan ya shiga ciki, wani tsarabar ya kara hado masu, sannan
ya siya ma inna malt carton daya, da peak milks holland, aka xo aka xuba kayan cikin booth
sannan suka bar wajen. Ana gama sallar la’asar suka iso gida, ya fiffito masu da tsarabar
tasu xainab ta bude baki tana kallonsa tace “me yasa xaka daurawa kanka nauyi haka ya faruuq,”
yace ni dae ku shiga dasu ciki xanje masallaci nayi sallah yanxu, sae na dawo. Kursum ce ta taya su
suka dinga jidar kayan suna sashin inna dasu, shima dan gulma tayi hakan amma ba don
saboda da Allah ba, Aliyu suka tarar xaune a palon, inna ta mike cike da doki tace “kar dae har kun
dawo?” intisaar tayi mata alamar tayi shiru saboda Aliyu dake xaune, haka ma xainab da ta daura
hannunta a baki alamar inna tayi shiru, inna tace “ayyo
haka ne pa.” Aliyu yace “ina suka je da?” da sauri inna tace “gidan hajiya Maimuna na aikesu.” to
wannan kayan meye haka? Cikin in ina inna
tace
“eh eh.. au ita ce ta bada a kawo min mana” nan ya shiga bubbuda ledojin yana kallon kayan baki
bude inna tayi maxa tace “maxa kuje can guriin xainabu gani nan xuwa” da sauri kuwa
suka juya suka bar wajen, sannan inna ta dinga kwasar kayan tana shiga dasu dakinta Aliyu na
binta da kallo “Allahu akbar.. Yanxu har da maltina aka kawo min?? Lah har da madara ni rahma,
amma mutanan nan anyi mutanan kirki.”Aliyu ya bude baki yana kallonta sae kace warce bata taba
shan madara ba ko malt, ita da duk wata abba ke jido mata su dayawa, amma ko sati biyu
ba sayi take shanyewa da yara. “kai Allah ya shima wannan yaron Albarka” Aliyu ya dubeta yace
“wani yaro?” au na manta ne Allah ya shima maimuna Albarka xance, ko da yake ma duk
Daya ne, don dan ta da ya dawo daga waje ne yayo min tsarabar. Aliyu ya tabe baki ya jawo
Abincin gabansa xai fara ci akayi sallama faruuq ya shigo palon bayan inna ta amsa da karfinta,
Mikewa tayi ta rasa inda xata sa shi sae ca take “sannu da xuwa dan Albarka,” ya nemi guri ya
xauna ya gaidata ta masa cike da jin dadi, sannan ya ba
Aliyu hannu sukayi musabaha, da dan fara’arsa Aliyun ya karba don bai san sa ba. Inna ta
Mike ta bude fridge ta jido masa lemo kusan kala hudu da ruwa roba uku, ta dire masa a gabansa
Tana tambayensa ya hanya, sannan ta shige ciki ta fito da cin-cin da alkaki bakin nan nata yaki
rufuwa. Godiya ya dinga yi mata, don yana jin dadin yanda inna ke nan nan dashi, ko xaka ci
abinci ne, bari na kawo maka cokali kuci tare da Aliyu, wannan shine Aliyu jikana da nake baka labari,
dariya ma abin ya ba Aliyun, ta dauko cokalin ta saka masa tace suci tare. Aliyun bai yi musu
ba ya sauko yana cewa ki dae yi a hankali karki fadi da wannan barin jikin da kike yi. Bata ko
tanka masa ba tace “wannan shine faruuq saurayin intisaar ae nasan baka san shi ba, Haisam ne
ya san sa,” dago kai Aliyu yayi yana kallonsa, nan da nan dan fara’ar dake fuskarsa ya bace, inna
tace to kuci abincin mana kar ya huce, ajiye cokalin hannunsa yayi fuskar nan tasa a yatsine yace “ya
dae ci, amma ni wannan ba isar mu xai yi ba,” faruuq ya dago yana kallonsa, ya gane
nufinsa,don hka sae yayi murmushi yace to ni bari naci tunda bako ne ni, da sauri inna tace eh
hakan ma yayi sae ya hakura ayi na dare. Hade rai Aliyu yayi yana kallon inna yace
“kamar ya na jira na dare? Ban gane nufinki ba?”
Inna ta mike ta tabe baki hade dacewa “maida wukar dan nan” sannan ta shige daki sae ga ta ta