INTEESAR Complete Hausa Novel (1).

Fito da garin rogo da suga ta xube masa a gabansa tace “ka debo ruwa a pampo ka jika kasha don
ruwan kenan na kwaso wa faruuq.
Takaici ya hana Aliyu cewa komai sae bin inna da yake yi da kallo har ta koma ta xauna tana ci gaba da
hirarta da faruuq, shi kanshi faruuq din abin ya basa dariya sosae don har sae da ya dan
dara,
can sae Aliyu ya turawa faruuq din garin yace “shi da ya kwaso yunwa har haka ya shigo sae ya hada ya sha, ni kam am okay” ya fadi a walakance yana duban faruuq din da har
yanxu murmushi na fuskarsa, sallamar Haisam ne ya sanya inna bata tanka masa ba, inna ta
amsa da murnarta tana cewa “yawwa yaron kirki sannu da xuwa shigo ka taya ni godewa faruuq abin
arxikin da yayi min” haisam ya shigo suka gaisa da faruuq da fara’a sannan ya gaida inna da
bakinta yaki rufuwa, yace kinga inna bari naci abinci tukun yunwa nake ji, idan yaso in nagama
sae na taya ki murnar, faruuq ya dubi haisam yace “bismillah kaxo muci wannan don ni ba
wani yunwa nake ji ba,” nan da Haisam ya xauna suka fara cin abinci da faruuq din suna hira inna
na tsoma masu baki, haisam ya dubi Aliyu da ya kura wa TV ido yace “ya dae bross lafiyanka?,
kardai yau ma baka je clinic din ba” Aliyu ya watsa masa harara yace a fusace “spare me malam bana
son sa ido plss” daga haisam din har faruuq suka kwashe da dariya inna na tayasu har da
kwanciyarta, Aliyun ya kulu matuka amma bai sake cewa komai ba illa gnash din hakora
da yayi fuskar nan tasa a tamke. Har dae suka gama cin abinsu sannan inna tace idan basu koshi ba
ga gari su jika, faruuq yace a’a ya koshi haka ma, Haisam Nan inna ta fara jawabinta tana
washale hakora ” kaga haisam daxu su intisaar suka je gaida mamar faruuq suka yi masu sha tara
ta arxiki, bari na kwaso maka ka gani, gaskiya gidan mutunci ne wannan gida” nan inna ta dinga
jido ma haisam kaya yana ta yabawa da kara taya innar tasa godiya. Ido Aliyu ya xuba mata yana
kallonta cike da mamaki, daxunan tace masa kawarta ta bada a kawo mata yanxu kuma
tace daga gidansu faruuq, dama gidansu faruuq din sukaje? “kaga har kwalin maltina fa haisam,
kai ni dae banda bakin gode maka faruuq, Allah dae yayi maka albarka ya dada budi,” ta fadi tana
kallon Aliyu baki har kunne, taga yana mata wani kallon rainin wayo yana girgixa kafa, ta juyo
tana kallonsa da kyau tace “meye kake kallona haka,?
Ka taba kawo koda gwangwanin madara daya ka kawo min gidan nan ne bare maltina? Kuma
Don yanxu na samu me min sae ka dinga min bakin ciki? To ahir dinka, Allah ya fika, har gwanda
haisam duk sati yana yo min tsaraba amma ban da kai don bakin rowa irin taka,” ta juyo
tana murmushi taci gaba da shi ma Faruuq da haisam albarka. Ya mike tsam yana kallonta bacin
rai karara a fuskarsa yace “ai ke ba uwata bace da xan dauka gwangwanin madara na kawo
maki,
Idan ma kyautar nake son yi ae uwata na nan da ranta, don haka baki isa nayi maki kyauta ba
Hajiya, wa inda suka ga xasu iya sae su maki.
Aikin banxa kawae aikin hofi, mutum ya tsufa bae san ya tsufa ba” yana kaiwa nan ya fice
Ba tare da ya jira cewarta ba, sashin hajiyarsu ya
nufa, yana shiga ciki rae bace ya fara
Magana “mumy kina gidan nan xaki bar ‘yar ki ta fita
raka wata banxa can gidan saurayi? Hajiya ta mike da sauri tana cewa wa kenan? Kursum
daka palon tace “xainab mana daxu ta raka intisaar gidan saurayinta suka dawo da kaya niki-
niki wallahi,” hajiya ta xabga salati tana tafe hannu tace “wallahi ca tayi min inna rahmatu ce xata
aiketa gidan kawarta….” bae kara sauraran mahaifiyar tasa ba ya dubi kursum cikin tsawa yace
“ina xainab din?” a dan tsorace tace “tana can Palonsu intissaar can inna tace suje ae” maxa jeki ki
kiramin ita, ta dan marairaice fuska don ita mugun tsoransa takeyi tace “yaya ko naje
ba xuwa xatayi ba da dae kaje da kanka” bae kara bin ta kanta ba yayi sashinsu intisaar din rai
bace yana kwadawa kanwartasa kira, yana isowa wajen sae ya daina kiran nata don yasan
xata iya gudu idan taji muryarsa, daga dan nisa ya hango ihsaan bakin tap tana dauraye cup
din da tasha corn-flakes, tana ganin sa ko ta ruga ciki a guje tace “momy kinga ga uncle nan xuwa,”
intisaar ta xaro ido tace ya Aliyu? Ihsaan ta gyada kanta, nan suka shige bedroom din
momy a guje don tsiyace kadae ke kawo Aliyu
sashinsu, yana isa bakin kofar ya bude yana karewa palon kallo, momy na xaune dama ita ma a palon,
ya kalle ihsaan yace “xo nan,” ta isa gareshi tana kallonsa, yace “me kika gudo kika cewa,
kuma idan baki gaya min gaskiya ba xan xaneki yanxu a nan” nan ta marairaice fuska xatayi kuka
tace “nace ma Anty xainab da Antyna kana xuwa”
shine sae sukayi me? Ya tambayeta yana kallonta, “shine sae suka gudu suka shiga
daki,” rankwashi ya kai mata har sau uku yace “ki
ka sake gani na kika je announcement sae na cire maki wannan katon idon naki, wawiya
kawai fice min a gaba. Ta ruga da gudu ta fada jikin momynta da ta tsurawa TV ido tun daxu,
tana kuku Ya juya xae bar wajen kenan don yasan ba fitowa xasu yi ba ya ci karo da hajiyarsu
itama ta karaso wajen a fusace, Aliyun yace “me kuma kika xo yi nan Hajiya?” bata bi ta kansa ba ta
dinga kwada ma xainab kira tana cewa
“wallahi ki fito daga gidan nan kar na ci ubanki
Munafukar yarinya,” ganin momyn intisaar din a xaune
A palo ne yasa ta ja ta tsaya, Aliyu yayi dan tsaki yayi gaba abinsa, don baya son uwarsa tana
masifa ko neman magana a gidan, ita kuma aikinta kenan. “Zainabu! Ki gya min dalilin sa ‘yata
bin watsatsiyar yarki gidan saurayi don a bata ta?”
hajiya ta fadi fuskarta a tamke, ko kallo bata ishe momy ba da ke ta aikin kallonta tana
rungume da ‘yar ta, hakan ya kara hassala hajiya don tana matukar bakin cikin sharesu da
momyn ke yi a gidan, kenan ma mahaukata kawae ta maidasu don ba dai amata abu ta tanka a
gidan ba, cikin daga murya hajiya tace “wae ba da ke nake ba ko kurama ce ke?” nan ma de
momy ko kallonta bata yi ba, hava nan hajiya ta dinga
gaya mata maganganu marasa dadi masu kuntata xuciya duk don momy ta kulata amma bata
ci nassara ba don momy murmushi ma kawae take yi. Hayaniyar hajiyar ne ya fargar da umma
ta karaso sashin da saurinta tana cewa “lafiya hajiya me ya faru, rashin kunya ta maki ko me?”
ina fa,, yawon iskancin da da ta sa ‘yar ta take yi, shi xasu koyawa xainab dita, tunda gashi yau
har shiryata tayi suje gidan saurayin ‘yar tata. Umma
ta xabga salati tana jujjuya kai tace “wallahi kursum taxo ta sameni wae xainab ta bi intisaar
gidan saurayi ya cika su da kaya duk na tsamman shirmanta ne shiyasa ban tanka mata ba”
hajiya tace “Allah ya isa tsakanina dasu,” umma tace “to yanxu ina shegiyar xainab din take” bata jira
amsa ba ta afka palonsu intisaar din ta tsaya
gaban momy tana cewa “ki fito mana da ‘yar mu kar mu aki abinda baki xata ba gidan nan yau,”
tana magana ne tana nuna momy da dan yatsa, momy tayi murmushi mai sauti, ta kama hannun ihsaan
suka shige bedroom ta kulla kofar. Galala umma ta bita da kallo, hajiya ma ta shigo palon
tace “idan ba tsoro ba dan uban mutum meyasa bae tsaya ba” nan suka dinga xaxxaga mata
rashin mutumci kwando-kwando suna xage-xage, gori kam ta sha shi kala-kala, abinda ya fi bata
masu rai bae wuce yanda ta barsu su kadae suna ta haukansu ba, don a da can idan suna mata