INTEESAR Complete Hausa Novel (1).

bude
baki tana kallon inna. Sallamar haisam ya
sanyata rufe bakinta, inna ta amsa mashi ba
tare
da ta lura da halin da intisaar ta shiga ba ya
shigo, suka gaisa yace “kina sha’aninki inna,
ina
kika samo kudi hka?” ya tambayeta yana
karewa
palon kallo, a xuciyarshi yana cewa kar dae
wani
abun inna ta kuma saidawa, don saranta
knan, in
dae bata da kudi to bata ki koh plaxman
palonta
ta saida ba, hkn kuma na bata wa abba rai
sosai
ba kadan ba, don duk abinda yke mata bata
gani
sae ta saida wani abun palonta ko daki,
“wllh fili
na na saida haisam” haisam yace “mene?”
Ba tare da inna ta kallesa ba tace “nace
mka fili na na saida. Ko bka ji ne” ya nemi
kujera
ya xauna yana kallonta cike da mamaki yace
“wani filin inna?” don dai shi yasan a ynxu
hka
inna bata da fili, idan ba dae wanda ake
mata
gini taje ta saida ba, “wannan din da
babanku ya
siya min” ta fadi tana mikawa intisaar
kudaden
ta kai mata daki. Haisam ya yo waje da ido
“yace wani filin abba ya baki?” inna ta hade
rai
tace “na jan bulo mana” haisam ya saki
salati
yana kallon innar, inna tace “kai ni don Allah
ku
rabu dani, ina da bukatar kudi kuma baxan
saida
kaddarana ba?” haisam yace “ya salam!
Ynxu
inna abba ca yyi maki filin naki ne? Daga ya
baki
takardu ki ajiye masa sae ki je ki saida fili?
Wai
ma nawa kika saida filin?” “ni dubu dari
biyu da
hamsin aka siya,” inna ta fadi a marairaice.
Haisam ya mike da sauri yana kallonta ya ma
kasa cewa komai,” filin abban kika saida
masa
dubu dari biyu da hamsin? Kin san nawa ya
sayi
filin inna, haisam ya girgixa kai yana kallon
innar
cike da takaici, ita kam sai wuri-wuri take
da ido.
Aliyu yyi sallama ya shigo yana cewa “har
kin
dawo daga yawon inna?” ya kalli haisam da
yanayinsa ya sauya xuwa bacin rai yace “me
ya
faru guy?” Aliyu filin abba taje ta saida dubu
dari
biyu da hamsin wae” haisam ya fadi cike da
jin
haushi, Aliyu ya xaro ido yace “wat?” filin da
yke
cewa xai fara gini cikinsa nxt yr?” dariya
Aliyu ya
dinga yi har da dafa bango, intisaar kam ido
ta
xuba masu tana kallonsu ita ma tasan inna
bata
kyauta ba, tuni inna aka fara hawaye, irin
dariyar
da Aliyu yake yi ne ya kara kullar da haisam,
to
meye abun dariya a nan, ta rangada wa
abbansu
asara, don ko shi bai sayi filin hka ba, cikin
karkarwar murya inna tace “to ni ina nasan
filinsa
ne, da naga bai sake min mgna ba ai nayi
xaton
ya bani ne, kuma Aliyu ba kai ka bani
shawarar
ba to?” Aliyu ya xaro ido yace “wa? Aa karki
sake
saka ni cikin wannan case din Hajiya” inna
tace
wllh kai ka sani, kana ji ko haisam, jiya ya
shigo
da daddare nake ce mashi bnda kudi kuma
ga
bikin jikar aminiyata ya taso bari bukar ya
dawo
na tambayeshi kudi, sae Aliyu yace min ae
Bukar
bai da kudi ynxu hka sae dae idan xan saida
kujeruna ne na biya bukatata, to naga dae
taya
xa ayi na saida kujerun palona, palo ya
xamo
wayam, kuma kwanakin baya ma da na
saida
fridge dina ma ae sae da bukar yyi min
masifa,
to yana fita a jiyan sae na tuna ai akwae
takardun filin da bukar ya bani……” Aliyu ya
daka
mata tsawa yana cewa “ke inna rahmatu
wllh kar
ki saka ni cikin wannan case din na gya
maki,
idan dae mutum ba hauka ya fara ba ta ya
xai
kin kima kujerunsa ya saida don an bashi
shawarar, ni dama wasa nke maki, kuma
magana
ce na gya maki.” tuni inna aka fara kuka
wiwi,
Aliyu ya fice yana dariya, Haisam kam kasa
cewa
komai yyi, tun ba yau ba yasan Aliyu mugu
ne,
idan ba hka ba taya xa a saida kaddarar
mahaifinsa mai muhimmanci yayi ta dariya.
Ya
juya ya fice kawae ba tare da yace da inna
komai
ba, to waye ma yyi mata jagora taje tayi
wannan
aika aikan, Aliyu na fita yaje ya sami
hajiyarsa
yana ta dariya ya bata lbrin abinda inna tayi,
ta
hade rai tace “to meye abun dariya a nan
Aliyu,
gadonku fa ta walakanta kke dariya hka?”
ya
mike yana kallon umman tashi yace “ni
banyi
depend a gado ba mum, Allah ya hore min
don
hka, 4 ol i care,” ya fice yana ci gaba da
dariyarsa don yasan drama xa ayi a gidan
yau
idan abba ya dawo. Abba ne tsaye kan inna
yana
faman bambamin fada kmr xae maketa,
inna ba
baki sae idanuwa, “kinsan nawa na sayi filin
ne
xakiyi min hka inna, daga baki ajiya sae ya
xama
naki, ina aka taba yin hka? Bbu shawara
bbu
komai xaki je ki walakanta min abun da
akalla
xan iya saida shi miliyan daya da rabi.”
hajiya da
umma dake palon ji sukayi kmr su shide
don
murna, Aliyu ya kasa hadiye dariyar dake
cinsa
ya fasheta, abba ya juyo kansa ya dinga
masifa
kmr xai maresa, ba shiri ya kame kansa, don
ran
abba yyi mugun baci ranar. Ganin ba sarki
sae
Allah yasa inna ta fashe masu da kuka tana
cewa “tunda yusufa ya rasu dama nake
shan
wahala a duniyar nan, daga kai har ‘ya
yanka
bakwa tsinanani da komai, ni ke yi ma kaina
duk
bukata, Abba ya bude baki yana kallonta ya
ma
kasa cewa komai, shi din ne baya mata
komai?
Gnin ta dage sae rera msu kuka take ne
yasa ya
shiga bata hkri, tce “hka kawae baxan
kyautatawa
aminiyata ba jikarta xatayi aure, kuma
nasan idan
na tambayeka ba bani xakayi ba,” Abba ya
girgixa kai yana mamakin uwartashi, duk
juma’ah
sae ya bata dubu goma bayan abubuwan
da yake
siyo mata duk karshen wata sannan ya
damka
mata dubu ashirin ko tana da bukatar kudi,
amma yanxu kiri-kiri tace bbu mai taimaka
mata
a duniyar nan sae Allahnta, komai ita take
ma
kanta. Abba yace “to shknan inna, Allah yasa
hkn
shine mafi alkhairi, kudaden sun isheki de
ko? Ta
dan fara kame kame tana goge kwalla tace
“ni
idan san samune akara min dubu hamsin,
ko
kuma dari ma.” takaici yasa abba gyada kae
kawae, ya dubi Aliyu yace anjima ka ciro
mata
dubu hamsin Ali, xan bka, “tab! Ai ni abba
accnt
dina ko dubu goma bai kai ba ina ga ma.”
… Inna ta galla masa harara tace “Allah ya
dauwamar dasu a hka,” Haisam yace
“anjima xan
ciro na kawa maki inna.” nan ta dinga sa
masa
albarka, abba yyi mata sallama ya fice daga
palon nata cike da jin haushin hali irin nata,
Aliyu
ya bi bayansa yana cewa “wannan ai sata
kiri-kiri
ne kawae, daga an baki ajiye sae ki
maidashi
naki” bai jira me xata ce ba ya fice da sauri
yana
dariya. Haisam na fitowa daga palon innar
umma
ta aika a kira mata shi yaje, nan kuwa ta
balbalesa da masifa tana cewa” kai dinnan
soko
ne wllh, Aliyu ya fika wayo nesa ba kusa ba,
kana tunanin idan ka dauki kudin naka har
dubu
hamsin ka bata Alhaji bka xai yi ne? Kai dae
bn
san wani irin yaro bne Allah ya bani, don
meyasa
baxakayi koyi da Aliyu ba, duk ka bi ka tare
gurinta sae kce ta asirce, wllh idan baka yi
gaggawan sauya wannan mugun halin
naka ba
sae na saba mka” haisam ya girgixa kai cike
da
takaicin hali irin na uwartasa yace “Allah ya
kyauta! Sannan yafice a fusace. Shi kam
Aliyu
hajiya yaba masa ta dinga yi tana sa masa
albrka, shi dae bai tanka mata ba. Da
yammacin
ranar Haisam ya kaita gidan aminiyartata
bayan
ta shiga kasuwa tayi kaca-kaca da kudin, a
dole
ita wae sae ta kyautatawa kawartata tunda
bikin
jikarta ce. Su hajiya kam sun ji ddin xuwan
inna
gidan bikin don kwana biyar tace xata yi, ko
ba
komai xasu dan samu sarari a gidan su
sheka
tsiyarsu yanda suke so. Intisaar na daki
wajajen
karfe goma na safe tana duba wani Novel
na
turawa taji hayaniyarsu hajiya a tsakar
gidan, ba
shiri ta fito ta tarda su hajiya sun saka
momynta
a gaba sae maganganu suke gya mata fadila
na
taya su, “idan banda rainin wayo tun asubar
fari
take ta facakala da ruwa sae kace ita daya
ce a
gidan, ynxu idan ruwan ya dauke mu da
wanne
xamuyi ayyukan mu, mun xo muna mata