NJEEB 40

Ibtisam kallonshi tayi da sauri wanda akai Sa’a shima ita yake kallo, matsawa yayi kusa da ita tare da fad’in you always ask me to send you free right??
Ibtisam kasa bashi amsa tayi……
Najeeb yace OK I will send you free, coz even I ban San kallon Fuskanki because whenever I see your face zan tuna da abunda
kika aikata which……. Shuru yayi yana kallonta yanda take kuka
JIbtisam wani kuka ne ya kubce mata wanda bata san tanayi ba, kuma bata san zai fito ba……
Granny ce tace wai miye haka kukeyi ne? Kai ku fad’amin Mai kuke cewa Kun barni cikin duhu fah
Matsawa tayi kusa da najeeb wanda yake gaban ibtisam yana kallonta, tace Mai yake faruwa ne?? Tare da kallon ibtisam
Dad ne yayi magana tare da fad’in najeeb karka sake ka aikata abunda kake k’okarin aikatawa domin ibtisam nada laifi kaima kana dashi, just forgive and forget, kuyi hakuri ku d’auki kaddara, sannan maganan ibtisam gaskiya ta fad’a babu wacce zatai burin samun miji Dan giya har tai fatan ta had’a zuri’a dashi……
Abba ya katse Dad da fadin karka fad’i haka, komai da Allah ya tsara yana cikin kaddaran mutum, kaman yanda ka fad’a su amshi kaddara, haka shima abunda najeeb yake yana cikin kaddaranshi duk da akwai sakaci a ciki…..
Granny tace Kai Wai ba zaku fad’amin abunda ke faruwa bane??
Mum ce ta Fara Mata bayani harta gama granny ta kamo hannun najeeb Tana kuka Tana fad’in najeebu kayi hakuri dan Allah karka rabu da ibtisam na dad’e Ina fatan kuyi aure, sai gashi Allah ya yarda kunyi, kayi ma Allah kuyi hakuri ku zauna, Nayi farin ciki na Farko ranan da aka d’aura aurenku, yanzu babu abunda nake so in gani kafin in mutu sai yaranku, idan naga wannan kad’ai ya isheni dan Allah ku barni inga cikan burina na ro’keku…..
Najeeb yana jin abunda Granny take fad’a amma bazai iya bata amsa da Hausa ba…. Gaba d’aya yauce rana ta farko da yaji tausayin tsohuwar wanda ta kasance abokiyar fad’anshi….. Idonshi ya sauka akan ibtisam dake kuka itama wanda gaba d’aya maganan Granny yasa jikinta yayi sanyi
Granny ta kamo hannun ibtisam ta had’a dana NAJEEB tace wlh Idan kuka kasance a haka, koda banga abunda kuka haifa ba, zan mutu cikin salama, amma bazan iya juran ganin kun rabu ba dan Allah……
Najeeb ya janye hannunshi daka na ibtisam tare da fad’in I have make a decision bazan zauna da itaba, granny am sorry bazan zauna da matar da bata so na ba, na tabbata Idan ina tare da ita bazan juri Kalman cewa Tana son wani namiji a gaba naba Dan haka am sorry to say na sakeki saki d’aya…….
Ibtisam wani dum dum taji Wanda komai nata taji ya tsaya cak…… Lokaci d’aya kuma ta saki kuka mai sauti tare da fad’in Wlh najeeb baka da imani baka da tausayi, kaman yanda ka fad’a ban taba Sonka ba, amma yau kawai just for granny happiness naji Ina son zama dakai, dan kawai in sata farin ciki but you divorce me…. Hawayen idonta ta share tare da fad’in Allah yasa haka shine alkhairi, tana fad’in haka tayi Fuuuuu ta shige ciki
Najeeb ganin haka yasa ya lumshe ido, abunda baya son ji daka bakinta shine ta fad’a ban taba Sonka ba….. Wannan Kalman yana bata mishi rai, a kullum ya tuna irin yanda take cewa I hate you Abun yana sashi cikin takaici
Mum ce tace wannan sakin daka aikata bai saku ba……
Da sauri ya kalli mum alaman Mai take fad’i…..
Mum tace idan namiji ya saki mace tana jini wannan sakin bai saku ba, karka manta ibtisam tayi Bari kuma Tana jini a halin yanzu…..
Najeeb kallon mum yayi wanda Abba ya cabe da wannan hakane, ibtisam har yanzu tana matsayin matarka
Najeeb barin falon yayi inda jim kad’an sai gashi da k’aramin akwatin shi
Dad yace ina zaka??
Yace am leaving the country now
Dad yace taya zaka tafi Bayan baka da lafiya anyi maka aiki
Yace Dad plz am not a child yana fad’in haka ya fita Fuuuuu yabar gidan
Ibtisam itama tunda ta shiga d’aki ta Fara had’a kayanta domin yau take son barin gidan, Toh zaman Mai zatayi a gidan? Bayan ta gama had’a kayanta ta fito inda ta gansu a falo
Mum tace ke Ina zaki Kema haka??
Granny tace ni kun barni a duhu ko binshi za tayi ne??
Ibtisam tace Mum zan tafi skul yau, dan Allah karku hanani Ina bukatar in tafi wajan da……
Abba yace babu inda zaki
Dad yace a’a ka barta, ibtisam ki koma d’aki ki bari gobe sai driver ya kaiki
Komawa tayi inda su kuma suka zauna suna tattaunawa akan yanda zasu bullo ma al’amarin, inda Dad ya fara magana da fad’in nasan na cuci Najeeb Wlh komai yayi laifi nane, gaba d’aya ban bashi llimin sanin uban gijinsa ba, na D’aukeshi na kaishi rayuwar data Tamu ba, lallai Ina jin kunyar kiran kaina mahaifi Domin ban kasance d’aya daka cikin iyaye na gari ba, sai ga hawaye akan fuskan Dad,
Gaba d’aya kowa yayi shuru domin jikinsu yayi sanyi Sosai dajin kalaman Dad.
Dad yaci gaba da fad’in lallai sai yanzu na gane babban gatan da mutun Zaima d’ansa shine ya nema mai ilimin addini, bana zamani ba, domin daka ranan da mutum ya mutu wannan ilimin nashi na boko baida amfani ko kad’an, amma ilimin addini kam shine zai taimaki mutum a lahira, inda har yana dashi kuma yayi aiki dashi, gaba d’aya najeeb baya ganin girman mu which irin abunda yaga anayi a k’asar daya taso kenan, yaro yana abunda yake so, iyayenshi basu isa su hana shiba, rayuwar da kowa yake ganin yana da y’anci, na cuci d’ana da kaina
Yanzu idan NAJEEB ya mutu baida wani hujja, shikenan na bata mishi rayuwa….
Granny tace Alhmdlh tunda har Allah yasa ka fahimta kuma harka gane hakan, dama abunda naita kokarin nuna maka tun Farko kenan, gashi yanzu ka fahimta wanda a yanzu zan iya cewa lokaci ya k’ure maka, gaba d’aya kun d’auki rayuwar boko Kun sama kanku, bakwa tuna addini, wanda shi wannan bokon iyaka duniya ne, daka nan cikin duniya ya gama amfani, ku a’a bakwa tuna haka kudai burinku kawai kuyi boko shine wayewa, Hmmm Allah sarki rayuwa, Allah yasa mu dace
Duka suka amsa da Ameen
Abba yace yanzu lokaci bai k’ure Ba, ya kamata NAJEEB din a zaunar dashi Ayi mishi magana domin yasan addininshi
Mum tace inaga gaskiya babu wanda zaiyi mishi wannan taimakon sai a ibtisam, domin gaba d’aya na lura da NAJEEB yana Sonta, duba da irin yanda yake mata abu, na tabbata inda ibtisam zata kwantar da hankalinta ta nutsu ta amshi kaddara ta D’aukeshi matsayin miji ta nuna mishi muhimmancin ilimin addini na tabbata zai nema ilimi, domin ko dazu da take fad’in a mata adalci taya zata haiyu da Wanda yake aikata manyan laifi, na lura dashi kaman abun ya bata mishi rai sosai Wanda nake tunanin shine yasa har ya yanke hukuncin rabuwa da ita, wlh Nasan NAJEEB yana Sonta, shi a nashi tunanin inya rabu da ita shine zai bata daman samun abunda take so…..
Abba yayi murmushi tare da fad’in Nima na Lura da hakan ai koda aka fad’a mishi sakin bai saku ba, Kinji ai baice komai ba, sai barin gidan da yayi
Itama ibtisam d’in tana sonshi, duba da irin yanayin data shiga daya furta mata Kalman saki, tunda gashi itama daka karshe kwaso kayanta tayi zata bar gidan, wanda Ita bata san yama tafi ba, amma inaga tunda hakan ta faru mu barsu su hutu, dukansu suna jin haushin junansu, musamman NAJEEB da yake ganin itace ta zubar mishi da ciki, idan ya huce Nasan komai zai dai daita
Granny tace hakane,, Allah ya zaba mana abunda yake alkhairi
Duka suka amsa da Ameen
Inda Aka Kai abba d’akin ba’ki
Granny kuma tayi wajan ibtisam inda ta sameta tana kuka, tasan bata san najeeb amma gaba d’aya bataji dad’in raguwar aurensu ba, duba da yanda Granny take son su zauna a tare….
Granny tace ibtisam wannan kukan, fah???
AI kamata yayi kiyi murna tunda auren ya mutu, ba kince baki sonshi ba, toh ya rabu dake sai kije ki auri kabiru Mai Mata, wanda nake tunani hala harda ciki ma, ya manta dake, inma bai manta dake ba kyaje ki had’u da kishiya……
Ibtisam gaba d’aya ji tayi ta shiga rud’ani, ita fah duk wannan abunda ake ta manta ma fah ance kabir shima an d’aura Mai aure da wata….. Lokaci d’aya ta lumshe idonta domin yanda taji zuciyarta na Mata zafi, wannan zafin da takeji bana komai bane saina sakin da najeeb yayi mata, gaba d’aya ji tayi duniyar babu dad’i
Ganin granny ta dameta yasa ta tashi tayi toilet Tana kukanta, tare da kosawa gari ya Waye tabar gidan ta taji skul wanda sun kusa Fara exam
Najeeb kam America ya koma, domin yana bukatar tambayan malami game da wannan sakin da yayi ma ibtisam akace bai saku ba, kai harma da Wanda yayi mata sanda yasha giya, domin yana ganin kaman sharri ma tayi dan kawai ta rabu dashi, murmushi yayi sannan yace na barki ibtisam…..
Najeeb koda ya koma gidansa dake America sai yaji gidan yayi mishi empty, gashi tunanin ibtisam da abubuwan daya faru tsakaninsu shine ya fara dawo Mai cikin rai…… Ganin tunanin yayi mishi yawa yasa ya d’auko kwalban alcohol d’inshi ya bud’e harya kafa Kai zaisha yaji maganan ibtisam cikin kunnenshi ” amin adalci babu wacce zata so ta had’a zuri’a da Wanda yake shan giya, NAJEEB na tsaneka mashayi, you are drinker I hate to see your face…… Sakin kwalban yayi ta fad’i k’asa ta fashe tare dajin wani irin bugun zuciya, gaba d’aya ranshi babu dad’i ganin rad’adin yayi mishi yawa gashi tunanin ibtisam din ya hanashi sakat dole ya d’auko wata kwalban ya bud’e tare da kafa kansa ya fara kwankwada yasha wajan kwalba uku….. Gaba d’aya ya kasa tashi sai sumbatu yakeyi …….
Washe gari kaman yanda Dad yace hakan ya faru inda yasa driver yakai ibtisam skul Bayan dad yayi mata nasiha akan ta ri’ke mutuncin ta
Gaba d’aya ibtisam kallo d’aya zaka mata ka gane tana cikin wani hali, har rama tayi na wuni daya kaman wacce tayi ciwon kwana da kwanaki
Abba ya K’ara da fad’in sannan maganan aurenki da najeeb ki d’auka bai mutu ba….
Da sauri ta kalli Abba
Abba yaci gaba da fad’in Domin kuwa zamu tambayi malamai akai muji, saiki d’auki kanki matsayin matar aure
Jiki a sanyaye ta tashi ta fita gaba d’aya ta rasa maike Mata dad’i a duniya…..
Haka driver yaja suka wuce bayan Dad ya bata kud’i masu yawa
Bayan tafiyar ibtisam ne Abba yace suma Bari suzo su Kama hanya….. Abba yace lah kaga wani abu Aida ma mu muka sauketa a skul d’in
Dukansu dariya suka sa, domin Sun manta shap hanya ne..
Dad yace ai yanzu tunda hakan ta faru shikenan Allah dai ya kaisu lafiya
Suma su Abba kama hanya sukayi
Ibtisam wajan 3 suka k’arasa inda ta d’auki kayanta tai ciki, tazo zata k’arasa d’akinsu ta had’u da kubra
Kubra tace ibtisam sai yau?? Kai gaskiya kinsha ciwo Wlh har kin rame, sannu Allah ya k’ara sauk’i Bari ana jirana zanje in dawo
Gaba kubra tayi inda ibtisam tayi d’akinsu ta samu kofar a bud’e… Kai tsaye ta shiga inda taga zarah na girki
Zarah ganin ibtisam yasa ta saki ihu tare da rungumeta tana murna
Ibtisam kam kuka ta saki tare da fad’in Zarah NAJEEB ya sakeni…..
Zarah tace what saki?? Garin yaya??
Nan ta Fara bata Labarin abunda ya faru daka karshe tace zarah NAJEEB yana zargin na zubar da cikin ne da gangan wanda da farko Nayi yunkurin yin hakan amma na fasa sai gashi daka baya ya zube, which jinin da naga yana zubar Mai yasa gabana ya Fadi duka zatona ya mutu ne…..
Ajiyan zuciya Zarah tayi tare da fad’in haka abubuwa marasa dad’i sukai ta faruwa?? Amma duk ban sani ba
Ibtisam tace taya zaki sani Bayan bani da sim din da zan kiraki dashi muyi magana
Zarah kallom ibtisam tayi sannan tace ibtisam kina son NAJEEB,..
Ibtisam da sauri ta kalleta tare da sakin tsaki tace, ban taba sonshi ba, har gobe kabir nake so, sai dai kuma shima yana da mata sai kuma ta saki kuka….
Nan zarah taita rarrashinta akan tayi hakuri ta daina wannan kukan,
Dakyar ibtisam tayi shuru baccin wahala ne ya d’auketa
*AMERICA*
NAJEEB gaba d’aya yanzu kullum cikin Maye yake ko aiki ya rubuta musu takardan hutu harna wata biyar inda kullum yana gida yana shan alcohol d’inshi, domin baya son ya bata lokacin shi wajan wani tunanin da yake cewa baida amfani wanda gashi ya kasa daina tunanin
Kaman yanda yayi da Malam akan zaiso America zasu had’u hakan ko ta faru
Domin malamin shida kanshi yayi ma najeeb text akan yana America tare da tura ma NAJEEB harda address d’inshi domin tun sanda sukai waya da najeeb maganan najeeb ta tsaya mai a rai….
Allah yasa lokacin NAJEEB bai kwale ba, wanda hakan yasa dole ya garzaya domin ya sadu da malamin, domin yana son shima da kanshi yasan miye addinin Islam, sannan Abun dake ranshi yanzu yana son sanin miye hukuncin sakin da yayi ma ibtisam…….
Bayan najeeb ya shirya Kai tsaye gidan malamin yaje inda malamin ya amshi NAJEEB hannu bibbiyu
Nan ya mi’ka ma najeeb hannu suka gaisa
Inda yama NAJEEB umarni daya zauna
Bayan najeeb ya zauna sannan malamin yace najeeb koh??
Najeeb yace eh, tare da fad’in Malam mutum ne yasha giya Bayan yasha giya saiya furta ma mace Kalman na sakeki na sakeki har sau biyu ya matsayin sakin yake?? Shin yana matsayi saki Biyu ne duk da bai furta ba??
Sannan Idan namiji ya saki mace tana jinin haila ya matsayin sakin yake??
Malamin yayi gyaran murya tare da fad’in :
Wanda ya saki matarsa cikin Maye bata saku ba
Malamai sunyi sabani game da aukuwar sakin Wanda yake cikin Maye
1) mafi yawan malamai sun tafi akan cewa idan mutum ya saki matarsa, tabbas sakin ya auku, saboda shan giya sabon Allah ne, kuma shi ya jawo wa kansa, don haka sakin ya saku baza’ayi masa uzuri ba wannan itace maganan Abu hanifa, da Malik da shafi’i a daya daka cikin zantukansu
2) sakinsa bai auku ba, saboda lokacin da ma’iz yazo ya tabbatarwa Annabi (S A W) yayi zina, saida ya tambaye shi ko kasha giya ne, kamar yadda baihaki ya rawaito a sunanul kubra, hakan sai ya nuna mashayin giya ba’a amsar magananrsa.
Sannan an rawaito daga SAYYADINA USMAN da ibnu Abbas cewa :sakin mashayin giya baya aukuwa, kuma ba’a San wanda ya saba musu ba a cikin sahabbai. Wannan itace maganan imamu Ahmad da zahiriyya da ibnu taimiyya
Sannan akwai mutanan da sharuddan saki basu rataya a wuyansu ba
Halaye biyar da Shari’a tace in mutum ya saki matarshi a wannan halayen bata saku ba.
1) sakin mahaukaci: wannan ma wani abu ne sananne a shari’a cewar hankali na daga cikin sharuddan karban ko wane irin aiki na ibada
2) sakin mutumin dake cikin Maye : wasu Malaman na ganin ta saku saboda shi ya Sanya kansa a halin Maye, amma wasu Malaman na ganin matar bata saku ba saboda akwai hukuncin da Allah zaiyi masa akan shan kayan Maye da yayi Allah ne mafi Sani.
3) sakin mutum da aka tilasta: dole ne miji ya kasance Mai ra’ayi kansa Idan kuma har wasu zasu yi amfani da matsayi na jini ko kusanci ko kuma karfi a tilasta a sakar ma mutum mace to bata saku ba, ciki harda iyaye
Sai dai mafi kyawun a duk lokacin da iyayen mutum suka nuna masa ba su son wani abu, sai yabi hanyar data dace Don fahimtar dasu ta yadda zasu amince da abun, in kuma basu har suka k’i yarda suka cije sai ya duba darajan su na iyaye ya musu biyayya Don neman yardan Allah
4) sakin mara lafiya Wanda yakai gargara : malamai sunyi magana cewar Idan har ya saketa ne da gangan Don ya hanata cin gado to bata saku ba, in kuma ita da kanta ta nema ko kuma tayi laifin da yana iya Kai wa ga sakin shima wasu malaman na ganin ta saku.
5) sakin da akayi cikin zuciya ba tare da furuci ba. Mafiya rinjayan malamai sun tafi akan wannan saki bai inganta ba, saboda fadar Annabi (S A W) da yace lallai Allah ya yafe wa Al’ummata abin da zukatansu suka ambata muddin basu furta ko suka yi aiki dashi ba.
Malamin yace sannan yazo cikin sahih Muslim daga Manzon Allah ( S A W) cewa :
A duk lokacin da wani mutum ya saki matarsa yayin da take cikin al’adarta, lallai ya zama wajibi kada ya kula da wannan saki da yayi mata (Ma’ana sakin bai yi ba) yaci gaba da zama da matarsa har zuwa lokacin da zata yi tsarki, sannan ya saketa idan yaga dama, sahin Muslim kitabut talak juzu’i na 2
Maganan saki cikin Maye bata saku ba, kallon NAJEEB yayi sannan yace ko kaine ka aikata hakan??..
Najeeb yace nine na aikata hakan bayan nasha giya, na furta Kalman har sau biyu
Malamin yace Toh kaji yanda abun yake Sannan shima saki cikin haila shima bai saku ba……
Najeeb gaba d’aya wani irin Abu yaji cikin ranshi shidai ba ba’kin ciki ba haka ba murna ba
Malamin yace sannan ka tambayeni a waya akan shan giya haramun ne tare da zina??
Najeeb yace eh hakane, ina bukatar sanin hukuncin Mai shan giya a addinance da kuma hukuncin zina……
Malam yace shan giya haramun ne saboda fadar Allah a cikin SURATUL MA’IDAH Aya ta 90
Hukuncin mai shan giya kuwa in an kamasa za’ayi masa bulala 80 a mazhabar Abu hanifa da Malik da wata ruwa daga Ahmad bin hambul
Amma a wurin imam shafi’i da Ahmad a wata ruwayar daga gareshi za’ayi masa bulala 40 ne, duk suna kafa hujja da hadisin Anas dan Malik, wanda imamu Muslim ya rawaito shi a Lamba ta 1706.
In kuma ya mutu bai tuba ba zai shiga wuta, kamar yadda hadisin Abdullahi ibn Umar wanda ke cikin bukhari 5147 da Muslim 3736 ya nuna
Sannan sallah kwana arba’in mashayin giya zaiyi ba’a amsa, hadisi ya tabbata cikin sunan na imam nasa’i 5570, Sheihk albani ya inganta shi cikin silsila sawahiha 709 hadisin Abdullahi dan Umar.
Sannan ga cuttuka da giya ke haifarwa
Ulcer gyambon ciki
Yawan mantuwa
Tana taba hanta kuma Idan ya taba hanta yana sama mutum hepatitis
Sannan zuciyar mutum zata dinga bugawa da sauri, har zai iya janyo MA mutum kumburin zuciya, ga hawan jini
Sannan hantar mutum zata dinga nokewa
Gashi yasa mutum yayi wani irin girma Mara amfani
Akwai alot of cuta da giya ke sawa…..
Najeeb shuru yayi amma daka duka alama maganan malamin na shigarshi
Ajiyan zuciya najeeb ya sauke sannan yace yanzu wannan shine hukuncin mai shan giya???
Malam yace eh
Najeeb yace musulunci babu wani abu daya tanadar ma mutum in yana fushi, wanda in yasha zai huce
Malamin yace akwai mana
Najeeb kara zama yayi alaman yana son yasan Mai musulunci ya tanada
2gnovel
4medicals
Smidris
Malamin yace Al’qur’ani, a duk lokacin da mutum yake fushi ko kunci to tabbas ya d’auki al’qur’ani ya karanta…..
Nan malamin yai ta mishi bayani akan hukuncin zina da sauransu
Najeeb gaba d’aya jikinshi ya mutu lallai sai yanzu ya gane ashe da ba rayuwa yake ba, yana ta aikata manyan laifi ba tare da saninshi ba, lallai iyayenshi basu mishi gata ba, gashi yanzu yana da ilimin boko ga dukiya ya tara amma babu ilimin addini wanda shine zai kaishi da hanyar tsira wani irin hawaye ya silalo mishi a fuska…….
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());