INTEESAR Complete Hausa Novel (1).

To don
ubanku ku fito ku gya min ko ubanku ne ya
dasa
ma da’na famfofi a gidan, ku fito ku gya min
ko
nairan ku nawa ne a ciki na biya ku. Sbda
me
xaku sa min ‘ya a gaba a cikin gidan nan,
uban
me ta tsare maku? Ku fito ku gya min me
xainabu ta tsare maku nace matsiyata ”
cikin
daga murya inna ke ta xuba masu rashin
mutumci.
Momy ta dube intisaar fuskarta daure tace
“don ubanki sai da kika je kka gyawa inna
wannan mgnar bayan abinda…..” intisaar ta
xaro
ido a tsorace tace “wllh momy ban gya ma
inna
komai ba, tana bani tsarabar mu ae ban
sake
komawa ba ma.” abin ya daure wa momy
kai, to
waye ya gya ma inna wannan mgnar? Hajiya
kuwa kasa xaune tayi sae kaiwa take tana
komowa a palonta, ynxu xainabu sae da
taje ta
gya ma tsohuwar nan wannan mgnar. Hka
ma
umma dake ta lekar innar ta taga da ‘ya
yanta,
tsinuwa kam sun sha shi ba adadi . Ganin
inna
taki barin tsakar gidan ne tana ta masifa
yasa
momy ta fito ta dinga bata hkuri ta koma
sashinta, amma kememe inna taki ta dinga
xunduma masu ashar tana cewa ae yau sai
tasa
sun bar gidan nan, momy tayi sumsum ta
koma
sashinta ganin ba sauraranta inna xatayi ba.
Tun
a kofar gida haisam da Aliyu suka dinga jin
muryar inna kmr speaker, Aliyu ya tabe baki
ya
koma mota ya ciro apple dinsa da ya manta
a
ciki, haisam kadae ya karaso gate din ya
shiga
gidan ransa a bace, wannan wani irin
masifa ce
hka, kullum sae anji hayaniya a gidansu sae
kace
makaranta, yana shiga gidan ya ga irin
rashin
mutuncin da inna ke xubawa a gidan ya
juya ya
bar gidan kawai. Dariya Aliyu yyi ganin
yanda
Haisam ya fito daga gidan, ko kallonsa
Haisam
bai yi ba ya shige motarsa yyi gaba. Aliyu ya
shiga gidan ya dauki farar kujerar roba ya
xauna
gefen wani flower yana ta kallon inna yana
cin
apple dinsa with much interest. Tana ta
masifa
har da kukanta, “wllh kwado xan sa wa
duka
famfofn gidan, duk shegen da xae yi amfni
da
ruwa yaje waje ,” tana kai wa nan ta fice
daga
gidan tana gunjin kuka. Dariya Aliyu ya
dinga yi
har da buga kafa, hajiya ta fito jin muryar
dan
nata, ta rike haba tana cewa “ka ga makirci
ko
Ali, ynxu bayan duk abinda Alhaji yace sae
da
wannan tsinanniyar matar ta gya wa
wannan
mayyar tsohuwar ko?” shi dai bai ce komai
ba
yana ta cin tufarsa. Umma ta fito ita ma tana
cewa ” wannan anyi makirar mace…..”
shigowar
inna ce ta sa su yin tsit. Kananan
kwadunaye
inna ta shigo da har guda biyar, su ka bita
da
kallon mamaki. ” idan akwae shegen da ya
isa ya
matso kusa da famfofin da na ya gani.” hka
inna
ta dinga dasa wa famfofin kwado tana mita,
sashinsu intisaar da nata kadae ne bata je
ba,
Aliyu binta yke tayi da kallo har ta gama, ta
dawo tsakar gidan ta dauki kujera ta xauna
tana
girgixa kafa. Sumsum su hajiya da umma
suka
shige gida, Aliyu ya mike yyi hanyar kicin sae
gashi ya fito da tabarya, yyi hanyar daya
daga
cikin taps din, bugu uku yyi ma kwadon ya
balle,
inna ta taso da gudu tana cewa xan ci
ubanka
wllh idan ka sake shiga gonata Aliyu….
Tsawa ya
daka mata yana cewa “to me kke nufi hajiya,
baxan wanke hannuna ba kuma ko meye?”
yyi
tsaki ya bude tap din yana wanke
hannayensa,
depend a gado ba mum, Allah ya hore min
don
hka, 4 ol i care,” ya fice yana ci gaba da
dariyarsa don yasan drama xa ayi a gidan
yau
idan abba ya dawo. Abba ne tsaye kan inna
yana
faman bambamin fada kmr xae maketa,
inna ba
baki sae idanuwa, “kinsan nawa na sayi filin
ne
xakiyi min hka inna, daga baki ajiya sae ya
xama
naki, ina aka taba yin hka? Bbu shawara
bbu
komai xaki je ki walakanta min abun da
akalla
xan iya saida shi miliyan daya da rabi.”
hajiya da
umma dake palon ji sukayi kmr su shide
don
murna, Aliyu ya kasa hadiye dariyar dake
cinsa
ya fasheta, abba ya juyo kansa ya dinga
masifa
kmr xai maresa, ba shiri ya kame kansa, don
ran
abba yyi mugun baci ranar. Ganin ba sarki
sae
Allah yasa inna ta fashe masu da kuka tana
cewa “tunda yusufa ya rasu dama nake
shan
wahala a duniyar nan, daga kai har ‘ya
yanka
bakwa tsinanani da komai, ni ke yi ma kaina
duk
bukata, Abba ya bude baki yana kallonta ya
ma
kasa cewa komai, shi din ne baya mata
komai?
Gnin ta dage sae rera msu kuka take ne
yasa ya
shiga bata hkri, tce “hka kawae baxan
kyautatawa
aminiyata ba jikarta xatayi aure, kuma
nasan idan
na tambayeka ba bani xakayi ba,” Abba ya
girgixa kai yana mamakin uwartashi, duk
juma’ah
sae ya bata dubu goma bayan abubuwan
da yake
siyo mata duk karshen wata sannan ya
damka
mata dubu ashirin ko tana da bukatar kudi,
amma yanxu kiri-kiri tace bbu mai taimaka
mata
a duniyar nan sae Allahnta, komai ita take
ma
kanta. Abba yace “to shknan inna, Allah yasa
hkn
shine mafi alkhairi, kudaden sun isheki de
ko? Ta
dan fara kame kame tana goge kwalla tace
“ni
idan san samune akara min dubu hamsin,
ko
kuma dari ma.” takaici yasa abba gyada kae
kawae, ya dubi Aliyu yace anjima ka ciro
mata
dubu hamsin Ali, xan bka, “tab! Ai ni abba
accnt
dina ko dubu goma bai kai ba ina ga ma.”
… Inna ta galla masa harara tace “Allah ya
dauwamar dasu a hka,” Haisam yace
“anjima xan
ciro na kawa maki inna.” nan ta dinga sa
masa
albarka, abba yyi mata sallama ya fice daga
palon nata cike da jin haushin hali irin nata,
Aliyu
ya bi bayansa yana cewa “wannan ai sata
kiri-kiri
ne kawae, daga an baki ajiye sae ki
maidashi
naki” bai jira me xata ce ba ya fice da sauri
yana
dariya. Haisam na fitowa daga palon innar
umma
ta aika a kira mata shi yaje, nan kuwa ta
balbalesa da masifa tana cewa” kai dinnan
soko
ne wllh, Aliyu ya fika wayo nesa ba kusa ba,
kana tunanin idan ka dauki kudin naka har
dubu
hamsin ka bata Alhaji bka xai yi ne? Kai dae
bn
san wani irin yaro bne Allah ya bani, don
meyasa
baxakayi koyi da Aliyu ba, duk ka bi ka tare
gurinta sae kce ta asirce, wllh idan baka yi
gaggawan sauya wannan mugun halin
naka ba
sae na saba mka” haisam ya girgixa kai cike
da
takaicin hali irin na uwartasa yace “Allah ya
kyauta! Sannan yafice a fusace. Shi kam
Aliyu
hajiya yaba masa ta dinga yi tana sa masa
albrka, shi dae bai tanka mata ba. Da
yammacin
ranar Haisam ya kaita gidan aminiyartata
bayan
ta shiga kasuwa tayi kaca-kaca da kudin, a
dole
ita wae sae ta kyautatawa kawartata tunda
bikin
jikarta ce. Su hajiya kam sun ji ddin xuwan
inna
gidan bikin don kwana biyar tace xata yi, ko
ba
komai xasu dan samu sarari a gidan su
sheka
tsiyarsu yanda suke so. Intisaar na daki
wajajen
karfe goma na safe tana duba wani Novel
na
turawa taji hayaniyarsu hajiya a tsakar
gidan, ba
shiri ta fito ta tarda su hajiya sun saka
momynta
a gaba sae maganganu suke gya mata fadila
na
taya su, “idan banda rainin wayo tun asubar
fari
take ta facakala da ruwa sae kace ita daya
ce a
gidan, ynxu idan ruwan ya dauke mu da
wanne
xamuyi ayyukan mu, mun xo muna mata
mgna
kuma ta maida mu mahaukata, to dae mai
daure
maki kugu a gidan bata nan, idan kikayi
wasa….”
xainab ce ta karaso wajen da sauri ita ma
tana
cewa hva hajiya meye yyi xafi hka da
sassafe xa
ku sa momy a gaba kuna…” kyakkyawan
mari
hajiya ta watsa ma xainab din tana cewa
“wuce
ki bni waje munafuka kawai, dama tun ba
yau ba
kike nuna ni ba komai bace a wajenki, idan
bnda
hka taya xa a maida ni mahaukaciya baki xo
kin
tsaya min ba xaki gya min mgnar bnxa, baki
ga
yanda fadila take yi bne don ubanki,”
intisaar ta
kalle momynta da ta tsaya tana kallonsu
kawae
bata ce komai ba, umma ta hankade xainab
tana
cewa bace mana da gani mara xuciya
kawae
warce bata san ciwan kanta ba. Girgixa kai