INTEESAR Complete Hausa Novel (1).

suka
rakota suna sa mata albarka, hajiya tace “ki
fa
ba wa hajiya sakona,” tace “xan bata hajiya”
sannan suka wuce ita da Aliyun. Umma tace
“gskya amintakan ku da hajiya mairo yyi,
tunda
har ta dauki tilon ‘yar ta xata ba danki,”
hajiya
tayi murmushi tace “ae ni bbu abinda xance
da
mairo, baki ji yanda naji ba ran da ta kirani
take
gaya min irin rashin mutuncin da tsohuwar
nan
tayi ma safeenah da bama gidan, wllh naji
takaici
sosae” umma tace “to ae laifinsa ne, don me
yasan bama gidan xai daukota ya kawo ta
bayan
yasan yan hassada ne a gidan, idan kin
bibiya
ma xainabu ce ta xuga innar tayi ma
safeenar
hkan.” hajiya tace “ae ba takanas ya dauko
ta ya
kawo ta gidan ba, hanya ce ta biyo dasu ta
nan
shine yace bari ta gaida kakarsa, ae tasan
bama
gidan.” muryar inna da suka ji tana kwada
wa
fadila kira ne yasa suka yi tsit, kursum tace
“bata nan” inna ta rike haba tace “ohh ni
rahmatu
yarinya ta maida kanta gantalalliya kmr
akuya
anki tsawatar mata, amma ba laifin kowa
bne, na
bukar ne, ae da ya aurar da ita da duk hka
bata
faru ba.” tayi gaba tana ta mitocinta. Hajiya
da
umma suka tabe baki, umma tace “randa
wannan
tsohuwar xata mutu ae sae na xuba ruwa a
kasa
nasha,” hajiya tace “ae ba ke kadai ba
shafa.”
Abba yace “gani inna,” bayan yaje kiran da
mahaifiyar tasa ke masa. Dama bukar dubu
ashirin xaka bani nayi ma yaran Nafisa
tsaraba
don gobe xanje gidanta, Abba yace “to inna
bari
haisam yaxo ya ciro maki.” tace “yanxu fa
nake
so ni dae wllh, don bn yarda da wannan
wayon
naka ba, sau dayawa hka kke min” Abba ya
jin
jina kai yace “ynxu xai kawo maki baaba.”
cike da
jin haushi yyi maganar ko sati uku ba ayi ba
da
ta saida masa fili sannan ya kara mata da
dubu
hamsin amma har tana tambayar wani dubi
ashirin din. Haisam tasa ya kaita sukayi
shoppin
din, ta jida kayan kusan dubu talatin, dole
shi ya
cika sannan ya maido ta gida. Washegari ta
samu Abba wae ya samo wanda xai kaita,
haisam baya nan, don hka dole yasa a kira
masa
Aliyusukayi
Aliyu na shigo wa palon Abban nasa ya
nemi gu ya xauna ya gaida shi a ladabce
sannan
yace “gani Abba” Abba ya hade rai yace “ka
gaida
inna ne yau?” inna ta tabe baki tace “ae ni
rabon
da Aliyu ya gaida ni tun ran da na ce shi yyi
min
wannan gulman” Aliyu ya xaro ido yace “kai
inna
ki dinga jin tsoron Allah mana” inna tayi
salati
tana kallon dan nata tace “wllh Bukar tun
ranar
Aliyu ko bangarena baya xuwa, ko ya gan ni
sae
ya kauda kai.” Abba ya dube Aliyun yace
“gidan
nafisa xaka kai ta anjima,” da sauri inna tace
“xuwa karfe sha daya dae” Aliyu ya mike
yana
kallon Abban nasa fuskarsa a tamke yace
“gskya
Abba ina da urgent meetin da xan wuce
ynxu….”
Abba yace “ni kke gayawa hka?” ya kauda
kansa
bai ce komai ba, inna kuwa ta dage da cewa
“wllh shi xai kaini, dolensa sae ya kaini, Allah
kai
xaka kai ni Aliyu” Aliyu ya juya yana mata
wani
irin kallo kmr ya maketa don haushi. “iyye
yaro
bashi da mutumci ba shi da kunya sae kace
ba
jininka ba Bukar, wllh bae yo halinka ba,
Haisam
kadae da xainab suka yo halinka a gidan
nan”
abba yyi murmushin takaici ya kalli Aliyun
yace
“je ka kawai.” Aliyu yyi maxa yace “ohk naji
xan
kai ki ki shirya” inna tace “kaci sa’a wllh”
fice wa
yyi ba tare da ya bari sun hada ido da
abbansa
- Tare da intisaar da xainab inna xata,
amma
hajiya na ganin hka sae ta tura xainab gidan
wata kawarta wae ta karbo mata sako, duk
don
kar ta bi innar, don tasa xainab ko ta hanata
xuwa ba ji xata yi ba shi yasa ta bullo da
hkn.
Intisaar bata san Aliyu xai kai su ba da
baxata
fara bin inna ba, wae sae da suka fito
tukunna
inna ta fara kwada wa Aliyu kira a tsakar
gidan
wae ya fito sun shirya. Intisaar ta dafe kirji
tace
inna shi xai kai mu dama, nayi xaton adai-
dai ta
sahu xamu hau ae, inna harareta tace “ka ji
shirme, gidan dan nawa da motoci xan hau
motar
haya, inna ta sake kwada wa Aliyu kira sae
gashi
ya fito fuskarsa daure yana sanye da polo
fari da
baki, da 3quatre fari kal, shi dae kam yana
san
3quatre, intisaar ta fadi a xuciyarta, inna ta
xabga salati tana tafe hannu tace “uban wa
xaka
bi a hka yaron nan?” Aliyu ya hade rai yace
“kmr
ya wa xan bi a hka?” tace “nashiga uku ni
Rahmatu nace uban wa xaka bi da wannan
dangalallen wandon?” yyi tsaki ya ce “idan
xaki ki
wuce na kai ki, don ina da gurin xuwa
hajiya,
meye ruwanki da abinda nasa” inna ta
girgixa kai
kmr xatayi kuka tana cewa “la! Wlh baxan je
da
kai a hka ba kaji min gantalallen yaro.” Aliyu
ya
tabe baki yace “to Allah ya raka taki gona,
dama
ni bnyi niyar kai ki ba ae,” sae ma a lkcn ya
kula
da intisaar da ta labe a gefen innar, duk
wannan
abinda akeyi su hajiya na labe a taga suna
lekowa, hajiya taji ddin yanda dan nata yyi,
inna
ta lalubo waya tana kallon intisaar tace “kira
min
bukar” da sauri intisaar tace “bn iya ba ni
xainab
ce ta iya.”a fusace inna tace “amma kin ji
haushi
kuwa” nan ta dinga kwadawa fadila kira
taki
fitowa, sae tayi waje don neman wanda xae
ciro
mata nmbr dan nata, a dai-dai lkcn Abba ya
kirata, ta dauka da sauri tana cewa “Bukar
ne?”
Abba yace “nine baaba kun tafi ne” tace “ina
fa,
wandon shaidanu yasa wae xae bini dashi,
irin
wandon nan dae da ya saba sa wa a gida”
Abba
ya kashe wayan ya kira a Aliyun, kasa daga
wayan yyi ji yake kmr ya makure inna don
takaici, can dae ya daga bai ce komai ba har
Abba ya gama sannan Abban ya kashe
wayan,
idonsa yyi jajur, ya juya fuu ya shige ciki,
inna
tace “Atoh dae.” bai jima ba ya fito da
dogon
wando yyi hanyar motarsa inna ta ja
intisaar
suka bishi, tana cewa “hka kawae ya janyo
mana
kallo a gari, yaro sae kace kafiri.” shi dae bai
tanka mata ba har ta ja intisaar suka shige
motar, intisaar dae jikinta bari yake, don
bata
bari sun hada ido dashi ba, “to uban wa
kuka
cewa da wannan yarinyar xan kai ku?” ya
tambayi innar fuskarsa a murtuke, inna tace
“ubanka muka cewa” to bata isa ta xauna
baya
ba na ja ta don bata kae wannan matsayin
ba
tun wuri ta dawo gun da ya dace ta xauna,
gaban intisaar ya fadi ta kalli inna, to ina
xata
xauna, ita fa wannan tafiyar ba dole sae ta
koma
gida, dama don taga tare da inna ne kuma
baxai
iya yi mata komai ba don inna baxata bari
ba
shiyasa ma bata ce ta fasa ba, amma da ace
da
su xainab ne to fasawa xatayi, inna tace “to
bbu
gun da xata xauna da ya wuce nan, bai sake
cewa komai ba don baya son magana, ya ja
motar suka wuce. A hanya hka inna ta dinga
magana a hnkli a kunnen intisaar, intisaar
dae
hadiye dariyarta kawae take don bata ma
san me
inna ke cewa ba ta dage sae mutsu-mutsu
take
mata a kunne, ita a dole xata ba Aliyu
haushi,
kallonsu kawae yake ta madubi, intisaar ta
lura
da hkn sae ta shiga taitayinta, yyi tsaki
kawae ya
kara volume din wakar dake tashi a motar, a
hankli intisar ta matso kusa da inna take
nuna
mata hanyar gidansu faruuq cikin murya
kasa
kasa take magana, inna ta bude murya tana
cewa
“Allah sarki yaron Arxiki” brake Aliyu ya taka
da
karfi, inna ta saka salati a rude tana cewa
“lfya?”
ya fito da sauri ya bude bayan motar, da
gudu
inna ta fito tana cewa “fito intisaar yau mun
shiga uku me ya faru?.
A rude inna ta dinga tambayrsa me ya
sami motar bayan intisaar ta fito, bai ko
kalleta
ba ya shiga kwaso masu ledojin tsarabarsu
da
saurinsa, inna ta dada rudewa tana cewa
“purse
dita na ciki akwae kudade da yawa fito min
dashi
da sauri wllh har da daham dina a ciki, ya
ciro
purse din ya ajiye kan ledojin da yake ta dire
su a