Jadawalin Mutanen Da Zasu Sami Aikin Wucin-Gadi Da Hukumar Zabe Zata Dauka
An bude shafin daukar Ma’aikatan wucin-gadi a hukumar zabe ta kasa
Zuwa yanzu mutane da yawa sun cika wannan aikin wanda a yanzu haka wasu har sun cika wasu Kuma suna son cikawar
Said dai aikin ya kasu Kashi hudu
Gasu kamar Haka
Rukuni na farko
SPOs-(SUPERVISOR PRESIDING OFFICEES)
Shi wannan shine na farko Wanda manya a aikin gwamnatin ko na Al’umma suke cikawa Wanda sai ka Kai GL10-GL14 ko Kuma Ma’aikatan wayan Nan hukumomi Wanda suka chanchanta a NYSC , NOA da kuma NIMC.
Har da Ma’aikatan INEC din ita kanta
Rukuni na biyu
Pos.Apo (I,II,III) (Presiding Officers)
Shi Kuma wannan shine rukuni na biyu Wanda ake bukatar su cika shi sune masu matakin karatun da suke yin service a yanzu wato cops members wadanda suke bautar kasa kenan
Shima Wanda sukayi bautar kasa a shekarar 2018,2019,2020, sai kuma 2021 sune kadai zasu iya cikawa
Sai Kuma Daliban da suke Kan karatun gaba da secondary School wato Daliban University,Nce, Nursing, polytechnic and others school Suma zasu iya cika shi
Sai Kuma Ma’aikatan MDAs na dindindin Wanda suke da OND ko Kuma GL7-GL10 Suma zasu iya cikawa
Rukuni na uku
Rac Managers (Registration Area)
su kuma shugaban makarantun RAC ko Ma’aikatansu daga Level GL07 zuwa Sama zasu iya naiman wannan aikin
Rukuni na Hudu
Ratechs (Registration Area Technicians) shi Kuma wannan Ma’aikatan INEC ta bangaren ICT sune zasuyi wannan aikin sai Kuma Yan bautar kasa da suke services a wannan Ma’aikatan ta INEC
Wadannan sune jadawalin aikin da hukumar zabe Mai zaman ka zata dauka
Fatan alkhairi
Gamu sha’awar cika wannan aikin zaku iya Shiga link na kasa
Yadda zaka naimin aikin INEC