NOVELSUncategorized
RAINA KAMA (BOOK 1) 15&16

*_♦RAINA KAMA……!!♦_*
_{Kaga gayya}_
????????1⃣5⃣
…….Tunda yafara tafiya bai tsaya ko inaba sai a wata sabuwar anguwa, shiru anguwar take babu yawan hayaniya, dan
gidajenma tsilli-tsilli suke tamkar rugar Fulani, wani gida dakecan nesa da sauran gidajen yanufa, gidane babba mai k’aton bak’in gate, yay horn sau biyu akazo aka bud’e masa. a babbar harabar gidan yay parking, yana cikin motar bai fitoba har kusan 10 minutes bayan yagama waya yace ya iso.
Idanu na zaro waje saboda ganin Muftahu yafito daga wata k’ofa yanufo motar, gaba d’aya mamaki yahanani kwakwkwaran motsi harya k’araso.
Mai taxi yafito ya risina ya gaidashi, sannan yace nagama aikina Oga.
Murmushi Muftahu yayi, sannan ya lek’a Munaya dake barci kashir6an ta glass, janye kansa yayi sannan ya zaro wayarsa daga aljihu yay kiran wani.
“Umh yalla6ai akwai ‘Yar matsala fa, dan barci takeyi sosai, kona d’akkota”.
Da sauri yace “No ina zuwa, amma wannan driver dayay aikin yabar wajen, dan bana buk’atar ya ganni”.
Murmuahi Muftahu yayi, tare da fad’in “angama ranka ya dad’e”.
Muftahu ya sallami drivern daya kawo Munaya, yace zai kirashi ya maidata zuwa anjima, yaje yabar motar anan.
“babu damuwa Oga, saina jika”.
Bayan tafiyar driver Galadima yafito, dama duk yana kallon abinda ke faruwa ta window.
Taku yake cikin tsantsar nuna jinin mulki dake yawo ajikinsa, ga wata izza ta zamowarsa cikakken namiji mai isashshiyar lafiya. fusakarnan babu walwala kamar kullum, ahaka ya k’araso wajen motar, Muftahu ya bud’e masa murfin inda Munaya ke kwance tana kwasar barcinta.
Kallonta yayi na tsayin mintuna uku, sannan ya janye idonsa ya rankwafo da kansa cikin motar, saida yad’an cije lips d’insa sannan yasaka hannayensa biyu ya tallafota ahankali ya fito da ita, tamkar ‘Yar baby haka ya d’akkota acikin hannayensa, sai wani kuma d’aure fuska yakeyi yana kauda kai, kaikace anmasa dolene ya d’auketa.
Hannu Muftahu yasaka yatoshe bakinsa saboda dariyar dake Neman kwace masa.
Wai yau Galadima gudane d’auke da mace a hannu, mutumin da ko kallon mata bai cika yiba, inkaga yana walwala ko dariya wa mace to Momma ce ko aunty Mimi.
Jakarta ya d’auka shima yabi bayansa.
Ya iske harya shinfid’eta a doguwar kujerar dake falon, yana gyara hannun rigarsa daya nannad’e yana jan k’aramin tsaki, ganin Muftahu na murmushi saiya kuma had’e fuska, Muftahu ya ajiye bag d’in yana had’iye dariyar da k’yar saboda gudun yin laifi.
Hannu yamik’ama Muftahu.
Muftahu yabashi handkerchief d’in daya zaro a aljihu, rankwafowa yayi kanta ya d’ora Handkerchief d’in bisa hancinta, tsayin minti 2 ya janye.
Tari tafarayi, saikuma ta fara k’ok’arin bud’e idanunta tana lumshewa, Muftahu ya mik’o masa gorar ruwa mai d’an sanyi.
Cikin hannunsa ya tsiyaya kad’an ya shafa mata a fuska, ahankali ta fara bud’e idanun ta, shikuma yaja da baya yakoma ya zauna bisa kujerar mai zaman mutum d’aya.
d’ora k’afa yayi d’aya kan d’aya ya jingina kansa jikin kujerar ya lumshe idanu, saika rantse idonsa arufe suke, amma ya zubasune akan Munaya dake ta mutsu-mutsun tashi zaune.
Da k’yar ta iya tashi ta samu ta jingina da kujerar tana k’arema falon kallo, yayinda hawaye ke zirara a kumatunta.
Ruwa Muftahu ya mik’a mata, babu musu ta kar6a dan wata kishirwa takeji, tunda tafara shan ruwan bata ajiyeba saida ta shanye tas, nan wata zufa tafara karyo mata kuma.
Mik’ewa Muftahu yayi yak’ara gudun AC n.
Ahankali zufar tafara tsanewa, saikuma tad’anji k’arfin jikinta, Muryarta na rawa alamun kuka tace, “Please Ku suwaye? miyasa kuka kawoni nan? dan ALLAH kuyi hak’uri karku cutar dani, karku lalatamin rayuwa dan girman ALLAH, Ku tausayama mahaifiyata, damuwar damuke ciki kad’ai ta ishemu, wlhy daku keta mutuncina gwamma Ku kasheni yafimin sauk’i”.
Daga Muftahu har uban gayyar kallonta kawai sukeyi, ita ko kad’anma bata gane Galadima ba, saboda yayi sama da fuskarsa.
Muftahu ne yace “ki kwantar da hankalinki, kuma ba abinda yasa muka d’akkokiba kenan”.
“to miyasa kuka d’akkoni? bawan ALLAH, mina muku?”.
Muftahu ya juya ya kalli Galadima, amma saiyaga ko motsawa baiyiba, bashima da niyyar tanka musu.
Itama Munaya saita maida kallon nata ga Galadima, a kuma lokacinne yad’ago kansa zai gyara zama.
Wata razananniyar k’ara Munaya tasaki saboda tsorata, da Sauri Galadima ya toshe kunnensa, shima tsawar ya Daka mata wadda tasakata nutsuwar dole.
“k!!! Dalla karki ciremana dodon kunni!!!!”.
Dole Munaya tayi shiru jikinta na 6ari da k’yarma.
Yaja wani wawan tsaki, tare da janye hannayensa daga kunnensa yana harara Munaya. “k wace irin shashashace ne?”.
Sukda halin da take ciki saida ta watsa masa harara, amma bata iya cewa komaiba.
Hannu yakai tamkar zai maketa saikuma ya FASA, komi yatuna oho.
Komawa yayi inda yataso ya zauna, ya maida k’afafunsa yay crossing d’insu.
Shi dai Muftahu yana kallonsu yakasa cewa komai, bakajin motsin komai saina shashshekar kukan Munaya Dana k’arar AC.
Cikin kuka tace “minamaka kasa aka kawoni nanan? ko sokake kakuma jamin wani sabon 6atancin bayan Wanda yafaru abaya? wane Abu na tare maka waishin aduniyarnan dan ALLAH bawan ALLAH?”. takuma rushewa da kuka mai tsuma rai.
Bakinsa ya ta6e a zuciyarsa yake fad’in daganin yarinyarnan akwai tsiwa dai, saikuma uban tsoro kamar farar kura. banza yamata, azahiri idonsa a lumshe suke, amma kuma abad’ini yana kallon Munaya ne, kukanta Neman saka masa ciwon kai yakeyi, dan haka yay maganar cikeda izza da mulki.
“kinutsu muyi abinda ya kawomu, inba hakaba zaki kwana anan gidan ne”.
Da Sauri Munaya ta share hawayenta, “indai kukane na daina wlhy, kayi hak’uri ka sanarmin, dan ALLAH ka maidani gida kafin hankalin innarmu ya tashi”. tak’are maganar da share hawaye.
Dariya taso bashi amma saiya gimtse, saikace ba itace tagama tsiwa ba yanzun.
Muftahu dai kasa hak’uri yayi saida yad’an dara, Galadima ya balla masa harara, hakanne yasashi yin shiru ya had’iye dariyar.
“kin shirya tafiya kenan?”. ‘galadima yafad’a tamkar an masa dole sai yayi maganar’.
Munaya tace, “wlhy na shirya ranka ya dad’e”.
Yace “good girl” yana ta6e baki.
“ki fad’amin waye yasaki aikin nan?”.
Cikeda rashin fahimta Munaya tace, “wane aikin?”.
Shiru Galadima yayi bai tanka ba, sai Muftahu ne yaymata bayani dalla-dalla akan abinda yafaru a plaza kwanakin baya”.
Cikeda k’unar zuciya Munaya tace “ni babu Wanda yasakani, saima tozarci da hakan ya jawo mana muda mahaifiyarmu, bansan komaiba, amma tunda al amarinan yafaru muka kuma tsintar kanmu a k’unci, kullum da irin abin kuka dazamu gani agidanmu, yanzu haka akan waccan abin maganar aurena sau biyu tana lalacewa, yanzu haka satina guda kenan da baro asibiti saboda tashin hankalin dana shiga a dalilin fasa aurena da cin zarafi dana fuskanta daga Wanda yafasa aurena nawa, wlhy Ku yarda dani bansan komaiba”.
Muftahu ya juya yana kallon Galadima da idonsa ke a rufe, amma yana sauraren Munayar.
Kusan mintuna 3 sannan ya bud’e idonsa, akan Munaya ya zubasu, bazata iya jurar kallon kwayar idonsa ba dan haka tayi azamar janye nata, shima janye nasa yayi ya gyara zamansa. “kince babu hannunki? amma miya kaiki plaza a wannan time d’in daya kamata duk yarinyar kwarai tana gidansu?”.
“Muna bikine, bayan munkai amare mun dawo sai fu’aad yamatsa akan saimun shiga, ba dan nasoba nayarda, kuma bani kad’ai baceba, harda ‘yan uwana su uku”.
“waye shi Fu’aad d’in?”.
“Saurayinane, awajen bikin muka had’u dashi”.
da sauri Galadima yace “miye kamaninsa? kuma ya kukayi dashi bayan abin ya faru?”.
A nutse Munaya tabasu labarin komai, sannan ta zano musu kamannin Fu’aad dalla-dalla, danma bawani kallon tsaf tamasa ba a cikin kwana biyun.
Muftahu yace “kozamu iya samun Horton shi Fu’aad d’in?”.
“banida hotonsa, dan bai yarda munyi ko photo d’aya ba awajen bikin, amma zamu iya samu a video d’in da akayi maybe awajen dinner? ”.
“galadima yace “a ina zamu CD d’in yanzu?”.
“gaskiya wannan shine mai wahala, dan bansan taka maimai cikin angunan waye yasaka ayiba”.
Galadima ya cije lips d’insa da k’arfi, sai kace zai hudasune.
Kusan mintuna 3 kowa baice komaiba, sai can munaya tace “kunji na fad’a muku gaskiya, Ku maidani kafin afara nemana”.
“zamu maidaki bisa sharad’i guda d’aya”. ‘cewar Muftahu ’.
“wane sharad’ine?”. ‘Munaya ta tambaya’.
“Sharad’in shine zakuyi auren 1year keda Galadima”.
Cikin zaro idanu waje munaya tace “kamar ya? ban fahim cekaba fa?”.
“ina nufin Auren yarjejeniya zakuyi na shekara 1 ko 2, ta wannan hanyarne kawai zamu iya kamo bakin zaren, sannan kekuma zaki sama ma iyayenki kwanciyar hankali, nanda kafin adadin da aka d’ibama auren yacika kinga komai ya wuce, saiya sakeki kiyi idda ki sami Wanda kikeso sannan kuje gida a d’aura miki aure dashi, Galadima ma zai iya sawa har auren a d’aura muku, daga baya sai kuje ya warwarema iyayenki komai, yakika gani?”.
“tabd’i, wannan wace irin maganace saikace labarin Novels ko films? to tayayama za’ayi hakan yafaru? bayan nama sanarma iyayena banida wata alak’a dashi”.
Murmuahi Muftahu yayi, yace “dan wannan duk mai sauk’ine, kedai amincewarki kawai muke nema”.
“amma dai kun maidani wawuya wlhy, to ban aminceba, gara na dawwama banyi aureba ai”.
Baki Muftahu ya bud’e zai k’ara magana Galadima ya d’aga masa hannu alamar yayi shiru ya barta.
“kinga tashi kije kawai, amma wannan maganar tazama iyamu ukunnan, idan najita awani waje saina zubar miki da hanjin ciki waje, duk shawarar dakika Yanke da zuciyarki zaki iya nemanmu daga nan zuwa kwana biyu kawai”.
Da sauri Munaya tazaro idanu waje tana kallon Galadima.
Harara ya zuba mata yace “karki cinyeni”.
Baki ta zun6ura gaba tana k’unk’uni, bayajin mitake fad’a, sai motsin la66anta kawai yake gani.
Sai da aka rufemin iso sannan aka baro gidan dani, bankuma kwanceba saida motar ta tsaya, Wanda yake tare dani yacire k’yallen sannan yace na fita.
Ko kallonsa banyiba saboda tsoro nafice amotar da sassarfa.
Gudu-gudu sauri-sauri na Isa gidanmu, mutane sai kallona sukeyi, ALLAH ma yasoni babu kowa a tsakar gida, inaga matan gidan duk sun shige sallar magriba yaran kuma basu dawo daga islamiyya ba.
A 6angarenmu ma innarmu na d’akinta, hakanne yabani damar shigewa d’akinmu wuff, na iske Munubiya na barci itama, na sauke ajiyar zuciya mai k’arfi ganin ALLAH ya tsareni babu Wanda ya ganni, kayana nacire daketa kamshin turaren Galadima, bayi nashige nida kayan, nayi wanka sannan suma na wankesu na shanya a bathroom d’in.
Harna fito Munubiya bata tashiba, nayi sallar magriba sannan nafito wajen innarmu.
Da mamaki take kallona, “yoni har ina shirin kiranki naji lfy baki dawoba had dare yarufa?”.
Zama nayi ina murmushin yak’e, dan abinda yafaru tsakanina dasu Galadima d’anzu ya min kane-kane a zuciya. ganin abin nakeyi kamar a mafarki. “ayya innarmu ai tun d’azun nashigo, lokacin kina salla, harfa nayi wanka ma nad’an huta. tace tana gidaki, yaya jikin Munubiya?”.
Jikinta Alhmdllh, tad’an watsa ruwa takoma ta kwanta bayan taci d’an abinci”.
To Almdllh, ALLAH yak’ara afuwa.
Amin innarmu ta amsamin, daganan muka koma hirar gidan Inna lami.
Munkai tsawon lokaci afalon muna hira da innarmu, sai dai nifa bama fahimtar hirar nakeba, dan fili kawai nakeson samu nayin tunanin maganar su galadima.
★★★★
Tun bayan tafiyar Munaya Galadima yakoma kan doguwar kujerar yay kwanciyarsa tamkar mai barci.
Muftahu dake kallonsa yace, “Amma miyasa kace ta tafi? batareda ta bamu gamsashshiyar amsa ba kuma?”.
Shiru Galadima bai amsaba tsawon mintuna uku, sai zuwa can yabud’e idonsa yana kallon Muftahu, baki yad’an ta6e “karka damu kanka, tama yarda, amsa ce kawai bata bamuba, itama kuma zata bayarne, tuni naga yardarta cikin kwayar idonta, akwai abinda take shakku akansa shiyyasa tak’i amsa mana”.
Kai Muftahu ya jinjina kawai, yasan tunda Galadima yafad’i haka to hakanne kuwa, amma sai yace “to amma bamu bata koda number ba, tayaya zata sanar damu amincewar tata kenan?”.
Murmushi kawai Galadima yayi baice komaiba.
Hakanne ya tabbatarma Muftahu murmushin Galadima shine amsar tambayarsa. Daga nan bai sake cemasa komaiba shima.
Falon yay tsit.
★★★★
Gaba d’aya a kwanaki biyunan banida wani sukuni, tunanin maganar yak’i barin zuciyata, a kowacce dak’ik’a zuciyata tunzurani takeyi akan Na amince kawai, dan banida wata mafita sai wannan, ni kaina inason sanin Wanda ya aikata mana wannan abun, sannan bana fata sauran ‘yan uwana suyi aure su barni a gidannan, hakan ba k’aramin tozarci zai zamarminba, ga Munubiya tadage akan innarmu ta sanarma Abba itama ad’aga bikinta har saina samu miji nima ahad’a ni da ita, na nuna mata 6acin raina akan maganar amma abanza, tanuna Sam ita tana a kan bakanta, nikuma harga ALLAH ba zanso hakan ta kasanceba.
Ita kanta innarmu nakula danne zuciyata kawai takeyi akan fasa aurena, amma tana cikin matsananciyar damuwa.
Yanzu yazanyi kenan? Na amince ko karna amince? gashi ya gargad’eni akan kadda Na nemi shawarar kowa, ni kaina nama kasa sanarma koda Munubiya, kuma kullum cikin tanbayata take mike damuna? duk da ita zatonta akan maganar Haidar ne har yanzu nake cikin damuwar.
Yau dai kwanaki biyu kenan da faruwar abin, har yanzu kuma nakasa tsayawa a matsaya d’aya.
Kusan tashin hantsi muna tsakar gida a baranda muduka ‘yan matan gidan, kowa da hidimar dayakeyi, sai wasu daga cikin k’annenmu dake wasa agefenmu, iyayenmu kuma Na daga can k’arshen barandar suma kowa da hidimarta, innarmu ce kawai babu tana gidan mama Rabi’a taje duba feena da jikinta yad’an motsa.
Tsayuwar mota mukaji a k’ofar gida, yara suka tafi da gudu dansuga wanene? azatonsu cikin su Dady ne.
Mintuna baifi 10 ba saigasu suna shigowa da ledoji, saikuma ga Zarah tashigo cikin kwalliyar kece raini, tana taku d’ai-d’ai, daka ganta kaga mai yaron ciki, cikeda muran muka hau mata sannu dazuwa, itako saiwani ciccijewa take tana kuma Jan kai, ita adole matar manya.
Abin kallo bai k’areba saida mamansu yaa Hameed ta iso da d’an gudu ta rungume Zarah a jikinta, duk mukai galala muna kallon wannan sabon salo.
“masha ALLAHU Zarah sarkin haske, kinganki kuwa, da anganki anga matar manya yarinyata, kai ai aure Ni’ima ce babba, duk wacce ALLAH yabama ‘yarta miji matan gidannan ta godema ALLAH, Dan wlhy yana sonta”.
Caraf Momy Hadiza ta kar6e da fad’in “wlhy kuwa Yaya, ai babu babban bak’inciki irin kanada gandamemiyar budurwa a d’aki tayi kwantai takasa auruwa, aimu sai godiyar ubangiji wlhy, babu ta inda ni’ima bata saukar manaba, Zarah zoki zauna ki huta kinji ‘yar albarka”.
Maman safara’u da gwaggon haleema da maman su Fiddausi suka kwashe da dariya.
Kowa yasan damu ake wannan gugar zanar, amma sai mukayi murmushi kawai bamuce komaiba, maman fauziyya ma batace komaiba, nama godema ALLAH da innarmu bata nan balle ranta ya 6aci.
Tsam namik’e nabar wajen zuciyata Na suya, Na danne kukan dake shirin tahomin…
Maman Safara’u tace, “to yanzu ke bazaki iya danne zuciyarki ba saikin nuna hasaadarki a filin ALLAH?, to Ashe ranar auren ‘yan uwanki mutuwa kuwa zakiyi?, dan kina gani za’a d’auke kowacce abarki agidan.
Wani k’arfine yazomin a zuciyata, Na had’iye kukana, najuyo ina kallonta ido cikin ido, wani murmushin takaici nasaki, sannan nace “maman Safara’u ke uwace agareni, sannan innarmu takoya mana tarbiyyar girmama kowacce mace agidannan, badan hakaba dana fad’a miki maganar dabazaki ta6a mantawaba, kuma ba hassadar tasani tashiba kamar yanda tunaninki yabaki, natashine Na d’aukama Zarah ruwansha, naga tashawo rana kuma babu Wanda yayi yink’urin bata”.
Ina gama fad’ar haka nabar wajen. tsit banji kowa yasake maganar ba, bansan miyasa ba, maganar tawace tasakasu yin shiru kokuwa oho.
Ina shiga falonmu Na fashe da kuka, anzo ga6ar da kawai zan amince da buk’atar Galadima, insha ALLAHU aranar datake fad’ar za’a tafi abarni, aranar nima zanbar gidan, Na gwammace nayi auren shekara d’ayan nafito.
Tunanin tawace hanya zanbi Na fad’ar musu Na amince na farayi, dan basu bani number ko wata hanyaba dazan iya nemansu, gashi kuma bazan iya gane gidan dasuka kainiba.
Tunawa dawata farar takarda nayi, wadda nagani a bag d’in dana fita da ita a ranar, kuma nasan ni bani Na ajiyeba.
Da Sauri Na d’auki bag d’in na zazage, saiga takardar tafad’o, na d’auka na bud’e, Number wayace ajiki kawai.
Jikina har rawa takeyi na d’auki wayata na kwafe number, sai kuma nakasa kira, na fara zagaye d’akin.
Motsi naji kamar na tafiya, da Sauri na shige bathroom d’inmu dan nasan Munubiya ce.
fanfo na kunna yanda zata d’auka wanka nakeyi.
Sha warar tura massage kawai na yanke. dan haka na rubuta
*_“na amince inhar bazai zama ka wulak’anta rayuwa taba”._*
Haka kawai natura masa na cire kayana nafara wankan gaskiya………..✍????
⛹????♀⛹????♀⛹????♀time d’in wasa yafara.????????♀
*_Ya ALLAH ka gafartama iyayenmu_*????????????
[4/19, 9:44 PM] +234 706 231 6249: *_Typing????_*
*_HASKE WRITERS ASSO…????_*
_(Home of expert and perfect writer’s)_
*_♦RAINA KAMA……!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
????????1⃣6⃣
…….Zaune yake cikin wata runfar bunu dake harabar gidan, dagashi sai wando 3quarter da t-shirt mara nauyi, k’afafunsa hard’e saman table dake tsakkiyar kujerarun, an yisane da ainahin siminti kamar kujerun, sai dai anmusu ado da katifa a sama wadda inma bakayi kallon tsaf ba zaka d’auka na katakone.
Laptop ce ajiye asaman cinyarsa, yayinda idanunsa ke sakeye cikin siririn farin medical glasses d’insa Wanda har kana iya hango fafaren k’wayoyin idonsa aciki.
Gaba d’ayan hankalinsa naga aikin dayakeyi a laptop d’in, lokaci-lokaci yakan d’auki fresh milk na hollandia dake a cikin kofin glass ya kur6a ya ajiye. d’an k’aran da wayarsa tayi yasashi waigowa ya kalli wayar, saikuma ya d’auke kansa ya maida ga system d’in. Saida yagama duk abinda yakeyi sannan ya ajiye laptop d’in bisa table ya sauke k’afarsa d’aya k’asa.
Ruwa ya d’auka yasha sosai sanann ya ajiye ya d’akko wayar da sak’o yashigo d’azun yana k’ok’arin dubawa. sabuwar number ce, dan haka yabud’e cike da mamakin waye?.
*_na amince inhar bazai zama zaka wulak’anta rayuwata ba._*
Shiru yayi yana nazarin massege d’in, dan yakasa fahimta India ya dosa, Yakuma maimaita karantawa har sau biyu, ana ukunne yarinyar shekaran jiya tafad’o masa arai.
Murmushin gefen baki yasaki, tareda d’age girarsa d’aya yana ta6e baki da fad’in “iyimm!. kingama Jan ajin kenan? Well dama nasan zaki amince ai”.
Wayar ya ajiye gefen table d’in, yazame ya kwanta a kujerar idonsa na kallon rufin bunun, yanzu dai yarinya ta amince, amma tayaya zai tunkari ahalinsa kuma da wannan batun? Mai martaba mahaifin Momma ne matsalar farko, saikuma k’anin mahaifinsa Sarki, Momma bashida matsala da ita inhar papi ya amince, yad’an cije lips d’insa yana lumshe idanu, dole yay gaggawar nemo mafita, dan bak’aramin aiki baneba agabansa, musamman daya zam duniya tagama saninsa da yarinyar a yanayin da bai dace da d’iyan bahausheba musulmi.
Ya sauke ajiyar zuciya mai k’arfi, kafin yaja kuma siririn tsaki.
Zumbur yamik’e saboda wani tunanin daya zo masa a zuciya. waya ya d’auka ya lalubo wata number da aka rubuta my second Momy. kusan mintuna biyu yana kallon number d’in batare da yayi dailing ba, saikuma ya danna cikeda jimami.
Ringing uku aka d’aga daga can.
bayan yayi sallama aka amsa daga can tace “a’a yarona dama kana k’asar?”.
Murmushi yayi tamkar yana gabanta, yad’an zame ya kwanta jikin kujerar yana shafa kansa. “Sorry my mom, wlhy 2days kawai da shigowata, kuma babu ma Wanda yasan nazo, wani d’an aikine ya kawoni”.
Dariya tayi daga can, cikin tsokana tace “yo dama ai kai kullum cikin aiki kake katafila”.
“oh my mom sunan dakika samin kenan? to nagode”.
“ai shine yadace dakai, yaka baromin ‘Yar uwa da jikin yayana?”.
“Everything Alhmdllh mom. wlhy nakiraki muyi wata muhimmiyar maganane, ALLAH yasa ke kad’aice?”.
“ni kad’aice yarona, inama bedroom kwancene, miya faru?”.
“uhmmm mom inason nayi a…” saikuma yay shiru yakasa k’arasawa.
“ina jinka mana”.
“ai mom maganarce bansan yanda zaki fahimceta ba, amma zancene inason nayi auren ”.
Zumbur tamik’e zaune, saboda jin maganar tayi tamkar daga sama, dan bata ta6a jin makamanciyar wannan maganar daga bakin Galadima Sameer d’in ba, hasalima bata ta6a jin ance yanada budurwa ba, kullum cikin yimasa maganar aure suke yana basarwa da cewa akwai sauran time, shiyyasa koda maganar jaridar nan tafito kai tsaye ta k’aryata zancen. “yarona wasa ko gaske dan ALLAH?”.
murmushi mai sauti ya saki tareda ajiyar zuciya, har yanzu hannunsa na yawo bisa Kansa yana shafawa “mom da gaske nakeyi, aiban ta6a kawo miki irin wannan maganar ba”.
“hakane, to ‘Yar wace masarautace ka samo mana?”.
Sai da yad’an ta6e bakisa sannan yace “no mom, babu kowacce masarauta”.
“tofa, d’iyar waye to?”.
“ba ‘Yar kowa baceba mom, yarinyar Nance dai da aka mana 6atanci tare”.
“Sameer ban gane mikake nufiba? kana haukane? Koma kafara shaye-shaye bamu saniba?”.
tashi yayi zaune sosai, ya d’auki ruwa yad’ansha, “ban fara shan komaiba mom, inason ki fahimceni da k’yau, dan kece ta farko Dana fara sanarma maganar, sannan kinsan Ku ukune kuka iya Sanin damuwata kai tsaye aduk duniyarnan. nasan zuciyarki zata kawo miki abubuwa dayawa akan maganarnan, to duk ba haka baneba……………”.
Anutse ya zayyane mata tarihin su Munaya, har zuwa maganar aurenta data lalace, yad’ora da fad’in mom banason nazama silar tawatsewar rayuwar yarinyar da bata jiba bata ganiba, ki fahimta mana, inason na bibiyeta ta hanyar auren Nata kozan sami wasu evidence akan case d’inan”.
Ajiyar zuciya mom ta sauke daga can, “to na fahimceka, amma ni mikakeso nayi yanzun?”.
“yauwa momyna, sonake kisamu inno da mai martaba da maganar, amma kinuna kamar kece kikayi tunanin su Sani na auri yarinyar”.
“iyim nagane, kenan dai yazamto kamar kaid’in bakasan komaiba?”.
“yes my mom, kin fahimceni dai-dai”.
Murmushi tayi, “ok babu damuwa, kamayi sa’a zanje gidan anjima dama na duba inno datayi mura”.
“wayyo ‘Yar tsohuwarnan, karfa ta wuce bataga ‘ya’yanaba”.
“k’aniyarka Sameer, aiko zan fasa kenan”.
“no please, sorry mom, nabari, ALLAH ya k’arama ginbiya inno lafiya”.
“zan kamakane fitsararre”.
Dariya yayi yana kissing d’in wayar sannan ya yanke kiran Yana cigaba da murmushi, yasan inhar inno da papi suka amince komai yagama yuwuwa, dan ko masarautarsu dolene kowa ya amince.
★★★★
d’aure nafito da zani ina goge ruwan goshina, Munubiya data zubamin ido tace “kuka kikayi ko sweetheart? ”.
“lah a’a wlhy, aini basukai namusu kuka ba wlhy Sweetheart, dan haka kima share batunsu. nifa kitsoma nakeson muje wlhy, kaina yagama yin datti har d’an tsami-tsami yakeyi”.
“kice kawai kin zama k’azama baby?”.
janbaki na d’auka na wurga mata, tai saurin cafewa tana dariya. nima dariyar nayi ina fad’in “kin tsira yanzu, amma next time bazan barkiba”.
“hhhh idan na zauna ko? kinga shirya kawai muje wajen aunty Salamah mu wanke kai, daga can saimu biya muga jikin feena ma ko?”.
“ok, hakan yayi”.
Shirina nayi cikin zani da Riga na wata oxblood d’in atanfa da ratsin milk, nakawo milk hijjab na saka batareda na d’aura d’an kwaliba, itama Munubiya irin kayan nawa ta canja. tsaf muka fito damu, saida Munubiya takira Innarmu ta sanar mata sannan muka tafi.
Mun tarar duk sunbar tsakar gidan, kowacce tashige 6angarenta, 6angaren su fauziyya muka lek’a domin sanarma mamarsu zamu fita.
bamu wani jimaba muka fito muka tafi.
Tunma a layinmu muka sami napep. har k’ofar shagon Aunty salamah ya saukemu..
Kamar yanda ta saba haka tamana tarba ta mutunci da d’oki. muma hakan ne daga garemu, dan muna k’aunar auntynmu data koya mana aiki, tace “’yan ukuna ina hasaanar to?”.
Dariya mukayi, dan munsan Ayusher take nufi, mukace bama tasan mun tahoba amma daga nan gidansu muka nufa.
An wanke mana kai, sannan mukayi kitso bawani mai yawaba, aunty ce tace dole sai ammana kunshi ko kad’anne, dole badan mun soba aka mana Jan lalli sai bak’i daya zamo kad’an, bamu baro shagonba sai bayan la’asar, dan mund’an taya aunty aiki.
Kai tsaye gidansu Ayusher muka nufa, mun iskesu gaba d’aya afalo suna hira, Ayusher na tacema Feena tafarnuwa dazafa sha. yayinda innarmu da mama Rabi’a ke zaune kusada juna suna hira k’asa-k’asa. Aiyaan Ahmad da Aryaan kam hankalinsu nakan wasa a can gefe.
Yaa fadeel ne yafara fad’in “oyoyo ‘yan biyunmu”.
Dariya mukayi, sannan muka k’arasa cikin falon, bayan mun gaida iyayenmu muka gaida yaa Fadeel, sannan mukaima Feena ya jiki, ta amsa tana murmushi.
Ayusher daketa antaya mana harara Na kalla, “kekuma lafiya kike wani hararmu?”.
Harar takuma watsa mana tana mik’ama Feena kofin tafarnuwa, “ban saniba ‘yan rainin hankali, tun k’arfe nawa kukace zaku taho amma sai yanzu?”.
Munubiya tatashi taje inda take ta rungumeta, sorry habibati, wlhy mun biya shagon aunty ne munyi kitso, saikuma ta tsaremu wai sai munyi k’unshi, tamace a gaidaki”.
“kai shine baku kirani mun jeba? wlhy nima kan nan nawa yana buk’atar kitso, tana lafiya”.
Namik’e ina fad’in “Sumul- sumul, mukuka dafa? ALLAH yunwa nakeji?”.
Cikin tsokana mama Rabi’a tace “tuwo”.
Na tunzuro baki gaba, kai mama wai keda innarmu kullum tuwo bakwa gajiya?”.
“yo yaza’ayi mu gaji tunda shi mukaci muka girma, kajimin ja’iran yara, wai kukam bakuda mak’iyi sai tuwone?”.
yaa Fadeel yace “yo k’aton ciki yake saka mutane, ina dalili”.
Dakuwa innarmu tamasa, “gidanku Fadeel, mu miyasa bamuyi k’aton cikinba?”.
Feena tace “ALLAH innarmu gaskiya yaa Fadeel yafad’a fa”.
“lallai Nafeesa, kema ina ganinki salo-salo Ashe k’yallece”.
Dariya muka sanya gaba d’aya, akuma wannan lokacinne yaa Marwan yashigo da sallama.
Su Aiyaan sukaje da gudu suka taryoshi da amsar kayan hannunsa.
Waje yasamu ya zauna yana gaida su innarmu, muma muka gaidashi.
Ayusher datasan dokarsa ta yana shigowa a kawo masa ruwa ta kalli Munubiya, sis…. Please kibama yaa Marwan ruwa, ni nariga da na ta6a tafarnuwa”.
Kamar munubiya bazata tashiba saikuma tamik’e saboda harara daya antaya mata, shi zatonsa ma nice, dan yasan Munu…. Akwai sauk’in kai.
Mama da innarmu kam hirarsu suketa zubawa kamar basusan mi mukeyi ba.
Babu dad’ewa saiga Munu… da k’aramin tire tazubo ruwa mai sanyi a jug, ajewa tayi a gabansa, ta durk’usa ta tsiyaya masa tabasa, sai da suka had’a ido ta janye nata da Sauri, alokacin ya fahimci Munubiya Ce, yana gama shan ruwan yadire kofin yana mik’ewa, “ki kawomin abinci d’aki”. ‘yafad’a yana yin gaba abinsa’.
Tad’an bishi da kallo sannan tamik’e takoma kitchen d’in.
Kallon juna mukayi nida Ayusher muna d’aga gira, yaa Fadeel daya gammu shima saiya saka dariya, k’asa-k’asa yanda su inna bazasuji ba yace “muma ALLAH kabamu masu sonmo”.
Muma ahankali mukace amin nida Ayusher.
Feena tace “ALLAH ya shiryeku, dama yajiku wlhy”.
Yaa Fadeel yace “saidai su susha duka, nikam ai bani dokuwa”.
Nanma dariyar mukayi.
Da sallama tashiga d’akin, yana zaune bakin gado dagashi sai vest da dogon wandon kayansa bai cireba, wayace a hannunsa yake latsawa, ta dire tiren abincin a gefe sannan ta janyo k’aramin table d’in gefe gabansa, abincin ta zuba masa, har sannan bai kalleta ba, saida tagama zata tashi yace “wato k saima ance kibani ruwa ko?”.
Shiru Munu… tamasa, Dan batasan mizata ceba, yad’ago idanunsa irin nata (dan duk ‘ya’yan mama Rabi’a kama muke da juna, saboda ita suka biyo, idan kacire Feena dake kama da babansu) yana kallonta, itadai kanta ak’asa tana wasa da zoben hannunta.
“baki jina ne?”.
Ahankali tace “kayi hak’uri to”.
Shiru yamata bai tankaba, yaja abincinsa yafaraci anutse, baice ta tashiba itakuma bata tashinba, gashi bawata hira sukeyiba, ita tunaninma yanda zatayi zaman aure da yaa Marwan takeyi, Yaya za’ayi rayuwa tayi dad’i Dan ALLAH?………
maganarsace tasaka ta d’ago ido tad’an kallesa, shima idonsa Na kanta. ta janye nata idanun.
Yakuma fad’in “nace yaushe zakije kiga gidanki?”.
Saitaji maganar wata iri, wai gidanta, gidansa dai, muryarta a sanyaye tace ai basai najeba”.
Yace “ko?”.
Kai ta d’aga masa alamar eh.
Yad’anyi wani munafukin murmuahi, Sanan yamik’e yanufi hanyar bathroom yana fad’in “ki shirya jibi zanzo na d’aukeki da yamma”.
Bai jira amsarta ba yashige abinsa. tadad’e zaune tana kallon k’ofar toilet d’in, tamkar nanne zata ganoshi, saida taji motsin kamar zai fito sannan tamik’e da sauri ta kwashe kwanikan ta fice.
Bamu bar gidanba sai bayan sallar isha’i, yaa Marwan da kansa ya kaimu har gida.
_____________________________
Yana kwance a falon gidan daya zama mafakarsa, waya suke da momma akan yaushe zai koma? dan doctors d’in Abie nason ganinsa.
“maybe ma gibe ki ganni Momma dan nagama abinda ya kawoni”.
“shikenan babu damuwa, amma kana ganin a masarautar ku babu Wanda yasan kazo?”.
“babu Wanda yasani momma, hatta da Harun, sai Muftahu kawai”.
Cikeda mamaki tace “Muftahu kuma?”.
“eh Momma miya faru?”.
Tayi d’an jim sannan tace “babu komai, amma ka dinga kula dai Muh’d”.
Shima yad’anyi shiru yana nazarin maganarta, sai kuma yace “ok Momma insha ALLAH”.
Yana ajiye wayar kuwa saiga Muftahu ya shigo, kallonsa Galadima yayi.
Muftahu dake shirin zama yace “yalla6ai barka da rana”.
“ykk?”.‘cewar galadima’.
“wlhy Alhmdllh, dama akan yarinyarne, kagafa har yanzu bamuji daga gareta ba”.
Murmushin gefen baki Galadima yayi, sannan yabud’o massage d’in da Munaya ta turo masa yamik’ama Muftahu wayar.
Babu musu Muftahu ya kar6a, saida ya gama karantawa sannan ya d’ago yana kallon Galadima fuskarsa washe da murmushi, “Alhmdllh yalla6ai ta amsa Ashe?”.
Kallonsa kawai Galadima yakeyi cikeda nazarinsa, yana mamakin yanda Muftahu ke d’okantuwa da wannan maganar auren, tunda yabashi damar binciken su Munaya bai barsa ya hutaba, haka kawai sai zuciyarsa ta d’arsa masa wani Abu, musamman idan yay dubi da yanda Muftahu ya nuna tsantsar farincikinsa dayace zai auri yarinyar na shekara 1. to koma dai miye, zai sanya masa idanu.
Muftahu yace, “yalla6ai to yanzu ya za’ayi dasu mai martaba ne?”.
Galadima dake latsa d’ayar wayarsa yace, “no, karka damu da wannan, zan k’arasa komai kawai”.
Kamar Muftahu baiso hakanba, amma saiyayi murmushin yake, “shikenan ALLAH ya tabbatar da alkairi, yasa ayi damu”.
d’ago ido Galadima yayi ya kallesa, “to miye kuma na wannan doguwar Addu’ar? Saikace wani auren gaskiya?”.
“Hakane kuma yalla6ai, sorry”.
Shiru Galadima bai amsaba. falon ya d’auki shiru kowa da tunaninsa.
★★★★
Harda safe inata yawan duba wayata kozanga replay daga Galadima amma shiru, hardai munubiya tace “wai miye bini-bini saiki duba waya?”.
Kallonta nayi ina k’ak’alo murmushin yak’e nace “babu komai fa”.
Badan ta yardaba ta k’yaleni, cigaba mukayi da aikin da innarmu ta samu.
Aryaan yashigo yana kuka, muduka mukace miya faru kaikuma?.
Cikin kukan yace “ba Abdul bane ya dakeni, wai dan Zainab ta zubamin ruwa na rama”.
Nace “ina Abdul d’in?”.
“Suna wajen fanfo”. ‘cewar Aiyaan daya shigo yanzun’. “Auntynmu kuma wlhy sosai yabama Aryaan mari a fuska, sannan ya halbeshi ga k’afarsa har yafad’i”.
Da hanzari nafice daga sashenmu, na iske Abdul da sauran yaran gidanmu a bakin fanfo suna wasa da ruwa, rankwashin Abdul nayi tareda murd’e kunnensa, “mi Aryaan yamaka ka dakesa dan k’aniyarka?”.
Hannuna yadafe saboda zafin dayaji na murd’ar kunnen, cikeda tsiwa yace “yoba Zainab ya daka ba danta watsa masa ruwa bata ganiba”.
K’eyarsa na mangara, “to ina ruwanka, Zainab d’in ba k’anwarsa baceba? kokuwa dan kai mama d’aya ta haifeku? daga yau kasake dukan wani acikinsu saboda yadaki Zainab ko Fahad saina lallasaka agidannan, masu shegen ‘yan ubancin tsiya, iyayenku duksun 6ataku da k’in ‘yan uwanku jininku”. nak’are maganar dakuma rank’washinsa.
Aikam ya daddage ya kwantsama kuka, kaikace wani uban bugu namasa.
Kamar jira gwaggon haleematu keyi tafito tana tambayarsa miya faru?.
Fad’a mata yayi waina mareshi da murd’a masa kunnen saboda ya daki Aryaan, harda cewa na zageta.
Hummm tamkar dama kad’an take jira damu, har k’ofar d’akinmu taje tana zazzaga masifa da zagina.
Innarmu tafito tana tambayar miya faru? dan ita bama tasan an bigi Aryaan d’in ba.
Maimakon tama innarmu bayani saita koma kanta da cin mutunci, kamar innarmu tayi shiru amma yau saita kasa.
Ta kalli Goggon haleema tana murmushi, Sadiya bakinki yasan mizai fad’a, inba hakaba zan baki mamaki agidannan wlhy, bakinki ya tsaya iya maganar yara, idan kika kuskura iyayena suka kuma shiga a furicinki zakiyi nadamar sanina”.
Innarmu nagama fad’a tashigewarta.
Galala gwaggon haleematu da duk matan gidanmu sukayi da mamaki, duk kuma sai shakkar innarmu ya shigesu, Ashe akwai ranar dazata iya maidama wani murtani acikin gidan?.
Murmushi nasaki, sannan nabama Munubiya dake kusadani hannu muka tafa, nace “ho innarmu, kina aljanna ina binki da addu’a, haka nakesonki agidannan, kiringa watsema kowa aniya”. naja hannun Munu…. muma muka shige ciki.
Abbanmu dake kallon komai ta window d’akinsa yasaki murmushi yana girgiza kai, yasan gaba d’aya halayen Munaya nashine, yarinyar batada tsoro, amma yau Ai’sha ta birgeshi datama Sadiya haka, koba komai tasaka musu shakkarta azukatansu.
Aikan kowa jiki babu kwari taja k’afarta tashige d’aki tana gulma da zuciyarta.
Gwaggon Haleema kam ai saida Nusaiba taja hannunta sannan ta iya d’aga k’afarta.
Koda muka Shiga sai innarmu tahau mana fad’a akan dukan Abdul d’in da nayi, hak’uri kawai na bata danni yau raina fes, innarmu tafara maida murtani.????
★★★★★
Da k’yar ya iya bud’e idonsa ya janyo wayarsa dake ringing, batare da ya dubaba ya amsa yasaka a kunne.
“Assalamu alaika Muhammad kana lafiya?”..
Zaram ya mik’e zaune tareda watstsayewar dole saboda jin muryar mai martaba mahaifin Momma papi………✍????
To ko mai martaba zai amince da auren Munaya? duk da baisan kai tsaye auren yarjejeniya baneba?????.
Karku manta Amincewar mai martaba itace ta kowa.