JIDDATUL KHAIR 54

fara’a ae, sannan ba a sanin cikinsa balle kasan me ya damesa” Aunty Nafisah tace “Toh Allah ya kyauta” Ramlah ta dau jakarta da na jiddah tayi ma su Ummi sai da safe, Ummi tace “Jiddar fa?” Ramlah tace “Kilan tana dakin Hajja, can xan je in duba…” Daga haka ta fita, Jiddah na xaune tayi jigum tana ta kallon Hajja dake ta surutanta, amma kusan duk bata ma san abinda Hajja ke cewa ba, Ramlah ta shigo tana
kallonta tace “Taso mu tafi Jiddah” Hajja tace “Toh xa ku tafi, Ahmad din ya xo ne?” Ramlah tace “Ehh” Hajja ta tabe baki tace “Shi dai baya ba mutane komai, bakar rowa kamar uwarsa wllh” Ramlah dai ta juya ta fita, Jiddah na kallon Hajja a hankali tace “Sai da safe” Hajja tace “To Allah ya kai mu, ai ni ban san
gidan Ramlah kike ba da na dinga kai maku xiyara a kai a kai tunda babu wani babba a gidan, Shi kuma Bashir idan ya aiko wayar xan amsa in ajiye maki, kuma babu shegen da ya isa yace baxa kiyi amfani da shi ba da rai na dai” Murmushi Jiddah ta kirkira ta mike ta fita, sai da ta fara xuwa tayi ma su Ummi
sallama sannan ta fito, parlor ta tarda Ramlah na jiranta, ta amshi jakarta a hannun Ramlah sannan suka fita, har suka fita kofar gida babu wanda yace komai cikinsu, Jiddah ta dinga kallon motar da Ramlah ta nufa, lkci daya jikinta yyi sanyi sosai ta bi bayanta walking slowly, back seat Ramlah ta bude ta shiga, a
hankali ta kai hannu gaban motar ta bude ta shiga sannan ta kulle, Abuturrab na kallon Ramlah yace “Ke gidanki xa a ajiye ki ai?” Ramlah ta kalli Jiddah da d’an confusion, sai kuma tace “Ohk to shkkn” Jiddah ta xaro ido tana kallonsa sai kuma ta kalli Ramlah, ya tada motar suka bar layin. fear Allah and pay for Jiddatul Khair before reading