KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KURUCIYAR MINAL COMPLETE HAUSA NOVEL

🏆KURUCIYAR MINAL🏆

1 – CHAPTER 1-10
🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹by miss untichlobanty🌹

🍀CHAPTER 1🍀

Amina ce zaune a kan wani lotsatstsen katifanta Kamar an taka bredi,basai nayi magana akan gadonta ba . Gefe wani kwano ne with a remained smelly stinky tuwo miyan kuka Wanda da alama tunna jiyane bata fitar da kwanon ba.

kuka take rizga Kamar ranta zai fita
innace ta shigo dakin domin ganin Lafiya yau yar lelenta shiru bata fito ta kama aiki ba? Turus tayi tana ganin ikon maleeku

Wani Abu na yar lele sai ita idan Ba haka Ba ya za’ayi mutum shi daya ya zauna yana kuka babu dalili.

innarce ta rafka uban salati Kamar an kama malam da karuwa tace me zangani haka aminatu Lapiya ? wa yatabo min tuwalle? me ya saki kuka?

Sai alokacin Amina ta dago ta soma magana cikin shessheka Kamar haka inna Dan Allah ki yafe min,ki roki kanwata deejeh ma tayafemin,awararta Dana karba tayi hakuri,dukan da nake mata ma na daina,kuma…kuma bazan kara zubar mata da abinci Ba kuma Wlh bazan sake kwace mata rakenta Ba Nayi alkawari har naira 50 din tama zan biyata 😭 duk rashin mutincin danakeyi Allah na dena Wlh na dena ta kara fashewa da kuka.

Galala inna tayi tana kallonta Wai yau aminatuwa ke Neman yafiya harda kiran deejeh kanwarta, lallai za’ayi ruwa da kankara
Inna tace toh yar lelen inna yi shiru kisanar dani ya akayi?me ya faru?
Minal tace inna aradu mafarki Nayi Wai cutar laser fever ta kamani Wai na mutuuu!
Inna tace kinga irinta ai mutum ace sai shegiyar kazanta yaushe Rabon da Kiyi wanka Yanzu?
Kina ganin kin kyautawa kanki kenan ?
Kuka ta fashe dashi tace kwana biyar ne kacal fa.

Inna tace ko kunyar fada bakyaji? wannan Ba laser Ba har ebola ma zata kamaki ai.
Kuka ta kara fashewa dashi tana shure-shure tace haba inna dama Ba sona kike Ba ?
Kuma ai dukda bana wanka ina canja pant fah.😭

Inna tace ni rufe wannan bakin naki karki taramun makwabta gashi duk kin cikani da warin baki.
Tashi dallah kije ki wanke baki Kiyi wanka.
Kurma ihu tayi tahau shure-shure da burbuwa.

Nan inna ta lallabata tace mata ai mafarki Ba Gaskiya bane…. haka dai ta hakura nan inna tace taje tayi wanka taci abinci Dan yau zata rubutar jarabawar karshe a makaranta daga shi next term zasuyi WAEC haka dai ta hakura ta shirya.

Ta fito zata tafi tace inna kin Tina wannan 100 Dana taba aramiki?
inna tace yaushe? tace lokacin nan sanda muka fara jarabawa
inna tace na Tina tace ki Dan banishi,inna tace haba yar inna nawa na baki atsakanin wannan lokacin?

Tuwalle tace ehheeeen wato dama badan Allah kika bani Ba inna ?!cabdi wallahi Nide sai kin bani kudin nan.

Inna tace sarkin jaraba, kin fita naci Kamar me, ta since bakin zaninta ta miko mata wata kodaddiyar Dari biyu tace ingo kuma kikawo mini canji domin shi kadaine gareni. Inna ta fadi dukda ko tasan da wuya ta kawo chanjin.
Yamutsa fuska minal tayi kamin ta karba tare da Cewa dande ina bukatar kudin ne da yasin bazan karba tsohuwar kudinnan Ba.

Nan ta rungumi inna Kamar da gaske sannan ta fita tare da Cewa sai na dawo sannan ta biya ta gidan su kawarta zaliha domin tafiya makaranta.

Koda aka tashi Tara(break) tsallaka katangan makaranta tayi taje tasiyo gurasa a kasuwa na duka kudin tayi sadaka dashi wa almajirai akan Allah ya kara rufawa iyayenta asiri

(dukda Cewa Amina akwai tsiwa da rashin mutunci ga Wanda ya nema amma akwaita da tausayin iyayenta sosai domin kazantarta Nada nasaba da haka acewarta Idan sabulu da turarenta basu Kare Ba ai iyayenta bazasu kashe kudi wajen siyan wani Ba shiyasa sau biyu take wanka a sati su inna har sun gaji da mata magana)

Amina Yusuf yarinya ce er shekara 18-19 farace sosai ga hanci shima daidai misali 8 figure ce ga tsayi daida gwargwado idonta ko sexy eyes ne gashin kanta kuwa ba’a magana.

Babanta wato malam Yusuf Wanda akafi sani da baban kowa carpenter ne bashida karfi amma yanada rufin asiri sannan duk anguwar ana ganin girmansa sosai manya da yara.

Asalin sa fulanin taraba ne wadda yarasa kowa NASA sanadiyyar gobara tun yana shekara 18 haka yarike Kansa har yakai 25 ananne ya dawo kano da zama inda ya hadu da falmata wanda ake kira da inna wacce take kanuriyar barno ce gyaran miki da turaren wuta take a kanon har sukayi aure dagabaya suka Koma Kaduna da zama Inda suke can cikin malali ahaka har inna ta haifi danta na fari wato Abubakar Wanda yanzu yake project a ABU amma shi yake rike kansa domin ya ragewa iyayenshi nauyi sannan yakanyi musu aike idan ya samu hali tunda Ba zaman banza yake Ba.

Daganan inna bata kuma haihuwa Ba sai bayan shekara takwas Inda ta Haifi Amina wacce take yarr jagwal ce ga neman magana,ga tsiwa, saide matsoraciya ce na masifa amma ta rike addininta dukda ko Ba ganewa ake Ba.

Sai daga baya inna ta Haifi khadijah wacce take auta kuma shekaranta 12.

Wannan kenan

Kubiyoni domin jin cigaban kuruciyar minal

26th April 2019

Love you all

Mzz untichlobanty💕
[1/11, 1:06 AM] Mzz_Untichlobanty💞:
🏆🏆KURUCIYAR MINAL🏆🏆

🌹by miss untichlobanty🌹

🍀CHAPTER 2🍀

BAYAN WANI LOKACI DA RUBUTA JARABAWAR MINAL

Morning

Minal rike da sakamakonta a Hannu miftahu (kanin hannatu zamu ganta a gaba #chapter 8 ) yace manya manyan Yan boko har an karbo sakamakon kenan da fatan wannan karan ma ba’a dauko ajinba. Cukumosa minal tayi ta naushi bakinsa tace aiko Ba Komai ni nane makarantar wasu a yawon banza za’a kare. Daidai lokacin sani (yayan bilkisu itama zamu gantaa gaba #chapter 8) ya wankawa minal mari juyowa tayi tace buhun bala’i bai ankareba yaga an nunashi wa sama an nana da kasa suka minal tamai jina-jina sannan tasa yara sukabuleshi da kasa.

Evening

A guje yara suka rugo Suna oyoyo baban kowa oyoyo baban mu! dama ya saba Dan haka yasa kullum baya rabuwa da tsaraba, hanjin ligidi mai yawa acikin bakin laida ya ciro ya basu suka karba Suna godiya kamin suka raba, wata yarinyace tace baba yau wani tatsuniya zaka mana yace tatsuniyar gizo bakin barawo zan muku.
Lado ne ya shinfida masa buhu Kamar yadda suka saba sannan Suma yaran suka zazzauna nan dattijonnan ya soma musu ta tsuniya……

🌹………….

Wasu samarine zaune Suna busa sigari wayan dayansu ta soma kara daukowa yayi yaga karfe alarm dinsa na large hudu ne take ya kashe sigarinsa yace kai yau fa alarm NASA mana aradu lokacin dawowan tsohonnan yayi,dariya suka fashe dashi wani yace Ba mamaki ya tsaya yiwa yara tatsuniyane. Sukace Ba shakka amma fa tsohonnan yana yiwa mutane cikas ka duba abinda yar bra uban yarnan tasa tayi dazu.
Daidai lokacin baban kowa ya karyo kwana,a take suka karkade jikinsu tare da wulla alewa a baki Dan kar yaji warin sigarin tasu.

Nufosa suka farayi Kamar abin arziki shima da murmushinsa yaje nufosu domin yaune karo nafarko dabai kamasu Suna busa sigari Ba.

Saide kash suna motsowa kusa dashi ya jiyota aiko take annurin fuskarsa ta dauke sukace babanmu sannu da zuwa Suna masu durkusawa

bata rai yayi yace Duba su Kamar da haske Kamar mutanen arziki, Wai Ku fi sabillilahi bazakuyi wa kanku fada ba, Kamar da gaske nadau kunyi hankali Ashe da sauran Rina a kaba,

Bakusan cewa wannan shaye shayen naku yana janyowa iyayenku Bacin sunaba?ko kunaso duniya tazagesu ne?girgiza kai sukayi sukace ayi hakuri baban mu Insha Allah zamu daina.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button