JIDDATUL KHAIRJIDDATUL KHAIR COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JIDDATUL KHAIR 55

Parking Abuturrab yyi a kofar gidan Ramlah, Ramlah ta bude motar xata sauka, Jiddah ma ta bude xata sauka, Hijab dinta taji ya rike gam daga kasa, ta kallesa da mamaki amma ta ma rasa abinda xata ce, Ramlah ta kulle motar bayan ta sauka tana jiran ganin ko saukowa Jiddah xata yi, Jiddah ta marairaice tana rike da handle din kofar motar murya can kasa tace “Meye haka wai, ka sakeni in sauka mana”

Abuturrab ya hada ido da kanwarsa dake tsaye still waiting for Jiddah to come down, a hankali ya sake Hijab din Jiddah ta bude motar ta sauka da sauri, Ramlah ta masa murmushi tace “Sai da safe yaya” Nodding kawai yayi, tuni Jiddah har ta shige cikin gidan, Ramlah ta bi bayanta… Karfe sha daya da wani

abu Ramlah na kwance kusa da Ahmad dake operating laptop dinsa, tace “Doctor” ya kalleta yace “Yess dear” Tace “Ina son in maka tambaya ne dama” Ya bar danna laptop din da yake yace “Ina jin ki” Tace “Nasan yaya baya boye maka komai da ya shafi rayuwarsa da dai sauransu…” Murmushi Ahmad yayi yana kallonta, tace “Ka gaya min gaskiya ko da akwai wani alaka tsakanin sa da Jiddah” Yace “Me yasa

kika min wannan tambayar?” Ta d’an yi shiru sai kuma tace “Naga wasu abubuwa ne da suka yi confusing dina” Yace “Kamar me?” Ta gyara kwanciya tace “Daxu a can gida muna xaune tare da Jiddah

ya shigo yace in je in debo masa abinci, bayan na dawo da abincin sai ban gansu a parlor ba, i dropped the food sai ga Jiddah ta fito daga bedroom din Ummi, she didn’t say a word ta fita, i was so surprise bayan few minutes na karasa dakin na gansa shi ma a ciki, sai kuma still daxu ya ajiye mu a gida, xata sauka mota naga ya rike hijab dinta but duk basu san na gani ba” Kallonta kawai Ahmad yake babu ko kiftawa yana sake assimilating din abinda tace, can yace “Sai aka yi yaya?” Tace “I don’t know what she

told him kuma daga baya naga ya saketa ta sauka motar” Ahmad dae yyi shiru, Ramlah tace “Tun daxu abun ya tsaya min, cause I am confused” Ahmad ya jawo laptop dinsa ya ci gaba da abinda yake, Ramlah tace “Ko akwai wani abu da ake boye mana ne Doctor?” Ahmad yace “I am confused just as u now Ramlah” Ramlah bata kuma cewa komai ba, Bayan few minutes ta mike ta fita dakin, dakin da Jiddah take ta nufa ta bude a hankali tana kallon cikin dakin, kwance ta ganta idonta a lumshe ta lullube da

hijab dinta maimakon blanket da ke ajiye gefe, ta fi minti biyu a tsaye har xata juya Jiddah ta bude ido, mikewa xaune Jiddah tayi tace “Kina son wani abu ne?” Ramlah ta sakar mata murmushi tace “Nothing naga baki kashe wuta bane” daga haka ta kashe fitilar dakin ta juya ta fita ta kulle kofar, Jiddah ta lullube har kanta da Hijab din jikinta ta lumshe ido… Karfe daya da rabi na dare Abuturrab na kwance Aneesah

na gefensa kamar xata shige jikinsa tana bacci, lumshe ido yyi ya bude, ya mike xaune a hankali being very careful not to wake Aneesah ya sauka kan gadon ya nufi kofa ya fita parlor ya xauna saman kujera ya rike kansa, ya fi minti talatin a nan sai kuma ya mike ya tafi bandaki ya dauro alwala ya fito… Washegari da ciwon kai sosai Abuturrab ya tashi, hakan bai hanasa ya shirya ya fita gida karfe goma ba

ya tafi can gidansu, sai da ya jira na kusan minti talatin sannan suka dau hanyar Hayin rigasa da Abbansa, Alhaji Umar, da wani aminin Abban nasa, shi yake driving so absentminded, har suka iso hayi yayi parking dai dai layin Mai anguwa, kasa ce masu komai yayi, shi dai Abba kallonsa kawai yake ganin yayi parking babu wata magana, ya saci kallon Abban nasa, suna hada ido ya bude motar yace “Abba xa mu

karasa ciki da kafa babu nisa” Daga haka ya sauka sauran ma duk suka sauka, Xaunawa Abuturrab yyi saman tabarman dake kofar gidan Mai anguwa suka gaisa da mutane biyu dake nan, Abuturrab ya d’an

shafa kansa yace “Gun Mai anguwa muka xo” wani matashi yace “Ayya ai bashi da lafiya yau kwanansa uku a shika” Kallonsa Abuturrab ya dinga yi babu ko kiftawa, sai kuma yace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un… Allah ubangiji ya tashi kafadunsa” Suka amsa da Ameen, mikewa yayi yana kallonsu Abba dake tsaye suna jin duk abinda Abuturrab yyi da matasan, Abba da Alhaji Umar da abokinsa suka ma Mai

anguwan fatan samun lafiya sannan suka koma gun mota, Abba yace “Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi, idan ya samu laifi sai a dawo ayi magana” Shi dai Abuturrab bai ce komai ba ya tada mota tunani iri iri a ransa, gida ya maida su Abba sannan ya karasa bangaren Ummi ya gaisheta, Ko minti uku bai yi a parlon Ummi ba aka bude kofar, Aunty ta shigo tana kallonsa tace “Wato da ni kake gaba a gidan nan ko Aliyu, sai dai ka shigo ka yo bangaren uwarka idan ka gama abinda ya kawoka ka fice kayi tafiyarka, to

kayi ta banxa in dai nice wllh, dama uban me kake tsinana ni da shi banda ma ni da nayi tsaye kan lamarinka tun baka kai haka ba, in dan ta ita uwar taka ce ka xata xaka kai matsayin da kake yau?? To wllh kayi da ni Aliyu, kuma ni nasan tsinanniyar da ta shiga tsakanina da kai, nasan musabbabin duk wannan abinda kake min, xa kuma tasan ni er halaq ce….” Tana gama fadin haka ta fita tana huci, Shi dai danna wayarsa kawai yake, Ummi dake dakinta duk tana jiyo Aunty ta ta6e baki ta gama abinda take ta

fito, gaisheta yayi bayan ta xauna, ta amsa tace “Akwai wani abun da tayi maka ne wanda ban sani ba take maka gori yanxu?” Yana danna wayarsa yace “Ko daya Ummi, ni babu wani abu da ta ta6a min” Ummi tace “Ohk, to me ya hadaka da ita yanxu baka shiga ka gaisheta?” Yace “Ra’ayi” Tace “Kamar yanda for years kayi ra’ayin dena shigowa gaisheni sai ka ga dama” D’an murmushi yayi yace “Aa Ummi”

Tace “Toh Allah ya kyauta” Shi dai bai ce komai ba, tace “Har yanxu kuna samun matsala da Aneesar ne?” Ya kalli Ummi yace “Me kika gani Ummi?” Ummi tace “Sai naga abu xan tambayeka?” Ya girgixa kai yace “Aa Ummi, tana gyarawa yanxu” Ummi tace “Toh gaya min meye damuwarka Aliyu” Ya daga kai

yana kallon Umminsa, Ummi tace “Tell me” Yyi kasa da idonsa, sai kuma ya mike ya koma gefenta ya xauna yyi kasa da murya yace “Ummi addu’a kawai nake son ki taya ni da shi” Tace “Baxan yi ba sai ka gaya min me ke faruwa” Yyi shiru ya rasa abinda xai ce, bayan few seconds cikin sanyin murya yace “Ummi , I don’t know how everyone is going to take this, but…” sai kuma yayi shiru yana jin xuciyarsa na

bugawa, Ummi tace “Bother not… Go ahead tell me what’s happening, i might take it softly” ya marairaice mata yace “Might kuma Ummi, you just have to take it softly” tana kallonsa tace “Ina sauraronka” Ya d’an kalli kofa, Ummi na ganin haka ta mike tace “Mu je daki to” Mikewa yayi ya bi

bayanta xuwa dakin. Driving Abuturrab yake a hankali har ya isa gida, bayan yayi parking ya sauka motar, baka ta6a fadin wani kalan expression ne a fuskarsa a lkcn, yana shiga parlor Aneesah ta leko daga kitchen tace “Welcome back my Captain” Yace “Thank you” tace “Na gama hada maka kayan, kaje ka duba ko sun yi” yace “Sai nayi sallah” Bandaki dake parlon ya shiga ya dauro alwala ya tafi masallaci don

lokaci yayi, Aneesah ta karasa ta dau wayarta dake ringing bayan ya fita, ganin Aunty ke kiranta ta daga ta kai kunne, daga daya bangaren Aunty tace “Kar ki kuskura yayi tafiyar nan baki amshi abin nan ba Aneesah” Aneesah na ci gaba da taunar cingam din bakinta tace “Sai kace ina hauka Aunty, na fa gaya maki yanxu lafiya muke xaune babu komai wllh, duk abinda nace yana yi, girki kuwa kan ya dawo

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button