JIDDATUL KHAIRJIDDATUL KHAIR COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JIDDATUL KHAIR 54

Ummi ta kalli Umma tace “Ahmad ai xai gane gidan shi ko?” Umma tace “Anya kuwa? Amma dai bari in kirasa in tambayesa” Daukar wayarta tayi ta wuce daki, bayan few minutes ta fito tace “Ai kam bai sani

ba wai shi ma” Ummi dai kallonta kawai take, Aunty tace “Tunda duk basu sani ba ai sai mu wuce gida kawai a nemi wani solution din, don baxa mu kama hanyar xuwa inda bamu sani ba gaskiya,” Umma tace “Ai ko dai” Haka nan su Ummi suka koma gida, Aunty farin ciki fal xuciyarta, ai ko ita kadai ta isa ta hana

xuwa gidansu Jiddah…. Hajja ce xaune parlon Abba ta dafe kai, cike da bakin ciki tace “Huhuhu… mutane dai yanxu tsoron Allah wuya yake masu ni Dije, da kyar al’ummar yanxu ke tsoron Allah wllh, yo banda rashin tsoron Allah ba a san gidan Aliyun bane da baxa a je a tisa keyarsa ya kai mu gun dangin yarinyar

ba? Ko kuna da wata manufa da kuke boyewa a ranku ne ban sani ba, ni dai wllh ban ta6a sanin Masar rahama bace sai da na baro can, wllh da can ne duk haka baxai dinga faruwa ba, yo ina hakan xai faru kowa ya tashi ya girma da tsoron Allahnsa” Abba yace “Yanxu ya kike so ayi Hajja, ba fa sauri ake

wannan lamarin ba…” Hajja ta dakatar da shi a fusace tace “Aa wllh sauri nake, kune dai baku sani ba, yanda xa ayi yanxu kuma shine a tashi a tafi gidan wancan mutumi Aliyu, idan kuma duk baxa ku ba, ni da kai na sai in dau gyale in je in dau yarinyar mu tafi gidan Aliyun in sa shi gaba ya kai ni unguwar tunda shi ya san asalinta” Abba yace “To gaskiya idan haka xaki dinga axalxalan lamarin nan ni Hajja xan cire

hannuna, sai shi Mai martaban ya taho da kansa…” Hajja ta runtse ido tace “Qul Usman, kar ka sake fadin haka wani sai yace bakin ciki kake wllh, nima don na kai xuciya nesa ne da haka xance wllh, ba fa wani yasa gantalallan d’an ka ya saketa ba Usman, bakin ciki kake ma d’an yayan naka ne? Aa to gaskiya

har ka ban tsoro, da kaina xan tashi yanxu in shirya in tafi gidan Aliyun, ai ba bakona bane gidan, irin wannan lamarin ance maka ana bin sa da sanyi sanyi ne” Tana fadin haka ta mike ta fice daga parlon, sai

da ta fara sa aka kai ta gidan Umma wai xa ta tafi gidan Aliyun tare da Jiddah, daga can shi kuma sai ya kai su hayin, Umma dake tsaye bayan kujera tace “Toh ai bata nan Hajja sun tafi Islamiyya, kuma ba ma gidan nan take ba yanxu tana gidan Ahmad ne” Hajja na kallonta daga sama har kasa tace “Waye kuma Ahmad, ana magana sai ki dinga wani sako Ahmad… Ita kuma ba sai ki kira makarantar kice a turota gida

ba, ko su basu san uxuri bane” Umma tace “Hajja idan kin je can gidan Aliyun kuma Allah ya sa kin samesa…” Da sauri Hajja ta katse tace “Yana nan ba inda xai je ana hutun karshen mako, ke dai kiyi ta kanki ki fada abinda xaki fada in tashi…” Umma tace “Shkkn, sai ya kai ki har gidan tunda nasan baxai

rasa sani ba, amma xancen a kirawo makaranta ace yarinya ta dawo a katse mata karatu bai taso ba balle ma ni bani da number shuwagabannin makarantar” Mikewa Hajja tayi ta nufi kofa murya can kasa tace “Aniyarki ta baki, mata kin narka kiba kina ta xuba ma mutane iko, yaushe xa a ga haka a Masar, ‘ya

yan bakin ciki kawai… Daga ke har Uban Aliyun” sannan ta fita…. Daga sama har kasa Aneesah ke kallo Hajja bayan ta bude kofar, can ta ja gefe ta kauda kai tace “Sannu da xuwa” Banxa da ita Hajja tayi ta shige parlon kai tsaye ta tafi kan kujera ta xauna, Aneesah ta bi ta da wani shegen hararan tsana, ita dai kaf kaduna bayan Jiddah bata da wanda ta tsana kuma kamar Hajja, Hajja tace “Zo ki kira min mijinki ni

wajensa na xo ba wajen wani ba, kuma sauri nake yi” Babu yabo babu Fallasa Aneesah tace “To ai baya nan Hajja, da kin kirasa kafin ki xo….” Ko rufe baki bata yi ba sai ga Abuturrab yana sakkowa, tsaye shi ma yyi a stairs din karshe ganin Hajja, Hajja ta kalli Aneesah tace “Kika ce baya nan?” Aneesah tace “Ohh

ban ma san ya shigo ba, ni ina kitchen ne” Hajja ta ja tsaki ta mike tace “Mu je Aliyu, ba xama na xo yi ba…” Bai yi musu ba saboda Aneesah ya bi bayanta suka nufi kofa, Aneesah ta kirkiro murmushi tace

“Toh baki sha ko ruwa ba Hajja, ga girki ma ya kusa nuna yanxu” Hajja tace “Aa wllh Alhmdlh, ai daga gida nake, kuma ni wajen jikana Aliyu na xo ba xama na xo yi ba dama” Daga haka ta fice Abuturrab ya bi bayanta, Da sauri Aneesah tace “My captain abincin fa?” Yyi mata alama da hannu yana xuwa, yana fita tayi wani murmushi ta xauna saman kujera ta dau chips dinta ta ci gaba da ci. Suna fita parking space

Hajja tace “Kaga da kyau ai da muka fito tunda maganar sirri ne, baxan bar wata 6are can taji cikinmu ba, wai don rashin kunya tayin ruwa take min saboda in sha in tsuge da gudawa, kai hancinka baya jin karnin da parlon nan ke yi ne kamar an fasa danyen kwai, ko iyayenta basu mata irin turarurrukan wutan

xamanin nan da naga ana yi ne, wllh fa kazama ce, da a Masar ne dole a raba wannan auren naku don guje maka wata cutar, toh dai ba ruwana da abinda bai shafeni ba, yanxu so nake mu hau mota ka kai ni gidansu yarinyar nan Jiddah, naji ance a hayin rigasa take koh?” Ya dinga kallon Hajja kafin yace “Ehh, me xaki je kiyi a can?” Tace “Aa wannan sirri na ne, yanxu muje ka kai ni, ni kadai ma na ishi inje gun

iyayen nata… Waye kuma Usman ko Umaru” Abuturrab yace “Toh bari in dauko makullin motar” Tace “Toh yi maxa” tana tsaye har ya shiga ya fito rike da makullin motarsa, ya bude mata back seat ta shiga sannan ya shiga maxaunin driver ya tada motar, yayi horn aka bude masa gate ya fita, Hajja tace “Ina gamawa da Bashir kai ma xan samar maka xukekiya mai tsafta kamar Jiddah, ko don saboda ka tsira da

lafiyarka” Ta madubi yake kallonta, tace “Kar fa a ga ina ta koda tsaftar wannan yarinya Jiddah wllh tana da shi ne, ni fa na sha gwada in ga ko tsaftar ganin ido take amma wllh ashe ba haka bane, kaga ko shara ka sa ta duk sai ta bi ta dage ko mai ta gani ta share fess, sannan idan ta gyara maka gado sumul sumul

kamar kar ka bar kowa ya hau… Sannan naga ta san muhimmancin turaren wutan nan na xamani, tana gama gyaran daki take sakawa, bandaki kuwa da na sa ta ta wanke sai da nayi xaton 6atan hanya nayi da na shiga, wllh har wani talli yake gwanin ban sha’awa, abinda kanninka su Aisha da Nafisah basu da shi, Allah bai basu ba… Toh amma dai ban sani ba ko ganin ido take, idan ma shi din ne dai ai ta iya aikin duk

da haka, wasu ma na ganin idon basu iya ba” Abuturrab dai bai ce mata komai ba, har suka shigo Hayi Hajja bata yi shiru ba surutu kawai take a motar, tafiya kawai yake har ya kusa karshen kwalta, ya ga wani d’an gida da aka rushe kusan rabinsa kasancewar a bakin titi yake, har sannan kuma ba a gyara

gidan ba don kamar ma anyi abandoning din gidan ne, waje ya nema yayi parking yana kallon wajen rusasshen karamin gidan, can ya kalli Hajja ya nuna mata yace “Ga gidan can Hajja, naga kamar kuma ba kowa yanxu” Hajja ta sauko da sauri tace “Ba kowa kamar yaya? Wannan kuturum gidan ne gidansu Jiddar?” Yace “Ehh” karasawa tayi tana kallon wasu da suka kasa kayan siyarwansu a kasa tace “Ke

yarinya ina masu rubabben gidan nan?” Yarinyar tace “Sun tashi tun da aka yi rusau” Hajja ta gwalo ido tace “Suka tashi suka je gidan uban wa?” Yarinyar ta buda hannu alamar bata sani ba, Hajja ta kalli Abuturrab da ya jingina da motarsa ya rungume hannu yana kallonta, tace “Kai kaji wai sun tashi ba a

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button