Lu’u Lu’u 5

*5*

 

Ayam data rumgume hannaye a k’irji cike da izza, salo da kuma gadara tana kallon k’wayar idonshi ita ma cikin harshen Gallois da bata tab’a sanin ta iya ba tace “Af Allan, ond byddwch yn mynd ar ol ar fy ol (zan fita, amma ka koreni a mutumce).”

Baisan sanda mamaki ya sake bayyana a fuskarshi ba, gyara tsayuwa yayi da kyau dan ya Fahim I shekarar da zaiyi kisan kan shi ce ta kama, nuna ta ya sake yi a dake yace” Ke, ke mahaukaciyar ina ce?”

Ba tare data rusuna idonta ba ta sake muskutawa ita m’a sannan tace” Sanin mahaukaciyar ina ce ni ba zai anfaneka da komai ba, kawai ka janye kalmar nan ta b’arauniya daka fad’a min.”

Hannayenshi bibbiyu ya rabka a k’ugunshi ya dafe jajayen idonshi a kan ta, ba alamar wasa a tare dashi yace” Ke ‘yar garin nan ce?”

K’urawa fuskarsa ido tayi ba tace komai ba, ganin bata da niyyar magana sa茂 ranshi ya sake b’aci, a harzuk’e ya cabki hannunta da nufin fitar da ita, da k’arfi ta fincike hannunta tana mai kallon inda ya rik’e, wani abu ta ji kamar wutar lantarki tana janta.

Kallonta ya shiga yi shi ma da tunanin ko dai abinda ya ji ita ma ta ji? Tsaki ya buga kawai ya juya ya sake shigewa ban d’akin zuciyarshi kamar zata fashe.

Ayam ma na ganin haka ta ja k’afarta data mata nauyi ta fita ita ma, a bakin k’ofar ta samu su Deeyam suna jiranta, da zumud’i Sabrine tace “Ya dai? Me ya faru 脿 ciki?”

Shiru tayi sa茂 sauka a matakalar data shiga yi, Deeyam ce tace “Ya muka ji kinyi ihu? Ko dai d’an hannu ne shi ma?”

Babu wacce ta amsa ma har suka koma ta inda suka fito suka koma d’akinsu suka kwanta, amma Ayam sai tayi zaune akan gado ta zabga tagumi tana sake kallon wuyan hannunta daya rik’e.

*A* wajen Umad ma saida ya ji an rufe d’akin ya fito, wajen hoton ya k’arasa ya durk’usa ya shiga tattare glass d’in, a kwandon shara ya zuba sannan ya d’auki hoton yana kallo, cikin yarenshi yace ” *Majka* (uwata), kiyi hak’uri ba laifina bane, waccen mahaukaciyar ce da ban san me ta zo nema ba.”

Ba tare daya saka kaya a jikinshi ba shi ma ya zauna kan gadon yana ta kallon hoton nan, so yake yayita zazzaga masifa ko ya ji sauk’i, amma dake mutum ne ba mai hayaniya ba sa茂 kawai yake ta tsaki shi kad’ai.

Sai dai ya k’agu gari ya waye ya bincika ya ji wacece wai ita d’in? Da wannan tunanin har bacci ya d’aukeshi bayan ya tofe jikinshi da addu’o’in tsari.

*Washe gari*

Zazzaune suke a cikin aji kowa na mazauninshi zaman mutum d’aya, sunyi shiru kuma sun nutsu suna sauraren jawabain ban kwanan da malam Pedro ke musu, yana gamawa yayi murmushi a harshen fransanci yace “To d’alibai, ni zan tafi yanzu, sai mun sake had’uwa da ku, ina muku fatan nasara.”

A tare dukansu suka amsa da “Za mu yi kewarka malam.”

Dariya yayi wanda hakan yasa Ayam juyawa ta kalli Deeyam cikin rad’a tace “Malam Pedro na dariya dama?”

Dariya Deeyam tayi a kan idon malamin, harara ya galla musu yace “Hirata kuke ko?”

Da sauri Ayam ta girgiza kai alamar a’a, shi ma girgiza kan yayi yace “Na sanki fa Ayam, da ni d’in nan ragon namiji ne da kin jima da sani hauka.”

Girgiza kai ya sake yi yace “To d’alibai, ni zan tafi na bawa sabon malamin ku dama ya shigo dan ya gabatar muku da kanshi.”

Hannu ya d’aga musu ya nufi hanyar fita, su ma hannun suka shiga d’aga mi shi, tun bai k’arasa fita ba Ayam ta mik’e ta tsaya a inda ya tsaya shi ma, irin tsayuwarshi tayi da yanda yake cije fuska ta tsuke baki ta fara magana kamar yanda yake alama tana kwaikwayonshi tana fad’in “To ni zan tafi, wani aiki ne ya taso da ake neman agazawarmu, amma ban ji dad’in rabuwa da ku ba musamman da shekara ta kusa k’arewa, amma duk da haka…”

Mik’ewar da duk sukayi d’aliban suna gaishe da malamin daya shigo yasa Ayam k’amewa tare da bud’e baki irin” Na shiga uku.”

Cikin sand’a kamar wacce k’wai ya fashe ma a cikita shiga takawa har ta zauna teburinta, tana jin takon takalmin malamin suna bada sauti d’a茂 bayan d’aya, saida ya tsaya tsakiyarsu sannan ya musu izinin zama.

Shiru ajin ya d’auka bayan sun zauna, shi yana k’are musu kallo su ma suna k’are mishi kallo suna fahimtar wane iri ne shi ? Zaiyi dad’in sha’ani ko kuma d’aurarrar fuska ce dashi kamar malam Pedro.

Ba tare daya juyar da kanshi ba iya idonshi kawai ya zuba mata, fuskar nan tamau da ita ba alamar annuri cikin dakusashiyar murya mai firgitarwa yace “Ya sunanki?”

Kamar sauran d’aliban ita ma d’aga kai tayi ta kalleshi dan son sanin da wa yake, idon da suka had’a yasa gabanta tsinkewa ya fad’i tare da kad’awar kayan cikinta, 脿 take kawai ta tausayawa kanta, marairaicewa tayi tana matse k’afafunta daga sama, wuwulk’ita idonta ta shiga yi cikin daburcewa da sark’ewar murya tace “A.. Yam.”

Wannan karan d’auke idonshi yayi daga kanta ya sake fad’in “Sunanki?”

‘Yar k’walla kawai ta ji ta zo mata a kan kunci, a sanyaye ta sake maimaita “Ayam.”

Takowa ya fara yi zuwa gabanta, da sauri ta sauke idonta tana kallon teburin, saida ya tsaya daf da teburin 脿 mugun kausashe yace “Ayam, baki da sunan uba ne?”

D’aga ido tayi da sauri ta zuba cikin na shi idon, hawaye taji kan kuncinta suna kwaranya, sosai maganar ta mata zafi, amma saita shanye tunda malaminta ne a aji, kanta sadde k’asa tace “Ayam Utais.”

Cikin tsananin bala’in haushinta da yake ji 脿 tsawace ya buga teburin da take zaune 脿 kai da hannu cikin d’aga muryar data sa ajin amsawa baki d’aya yace “Ayam Utais, ba’a koya miki tarbiyyar mik’ewa tsaye yayin magana da malami ba?”

Tunda ya buga tebur d’in yan matan ajin wasu sukayi ihu wasu kuma suka k’ame, kamar dai Ayam da ita ma k’amewar tayi amma fa kuma idonta cikin na shi.

Abu d’aya ya zo masa a daidai lokacin, maganarshi da babban malamin shi a sanda yake son sanin alamomin da zai ganeta, a yanzun da abun nan ya faru sai ya tuna sanda malamin yace _”Had’uwarku ta farko ba zata bada k’ayatarwa ba, saidai 脿 wurinka da zaka aje hankali, kowane motsinta zai baka al’ajabi, a zahiri mace ce kamar kowace mace, tana jin tsoron abinda zai tsorata kowace mace, saidai ba komai ke tsorata ba, akwai b’oyayyar jarumta a tare da ita, abinda ya cancanci ya bata tsoro ba shi ke tsorata ba kai tsaye, wanda kuma kai zai iya kayar maka da gaba, sa茂 kaga ita abin ado ne a gareta, saidai fa duk da haka mace ce mai birgewa, saboda tana da abinda duk wani namiji yake tsananin so ga ‘ya mace.”_

A lokacin tambayar daya masa ita ce _” Menene shi abun?”_

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button